← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 43

Sashe 27

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Key Ta dauka Ta dauki mayafi babba Ta fice abun,kofan Ta bude Ta fito gaidata wani bawa yayi dake waje yayi Ta amsa sannan tai gaba abunta,dube dube take bata San kowa ya ganta, haka har ta karasa, dai dai kofan Ta tsaya Ta dakko key din Ta bude sannan ta cire key din Ta shiga Ta rufe kofan Ta ciki Ta kulle, kallan gun take babba ne sosai Amman waime yasa zuciyarta take raya mata akwai abu anan ne? Tsaki taja ki tsaya bata lokaci dai har su dawo, gaba tayi Tana dube dube saida Ta kalli hanyar Da tabi ranar bataga komaiba hakan yasa ta yanke hukuncin bin daya hanyar, tafiya take abunta, tun daga nesa Ta hango mutane biyu zaune, tsayawa tai ta tsorata sosai me ye wannan mutane dama akwai mutanen Da suke rayuwa anan, karasawa take a hankali, a hankali kawu ya dago Yana kAllan ta,zaro ido yai tare da fadin sultana, Da sauri Ta karasa gunshi kawu Ta fada idonta Da hawaye kawu sawa yayi aka kamoka KO? Kawu nina jawo maka ko Dan Allah kayi hakuri zanje in fada mashi nice inyaso sai kashemu tayi, riko Ta yayi bance kije ba sultana, sultana bakiga canba ya fada yana nuna mata gun sarki, kallan gun sultana tai ido sarki ya Zuba mata, tabbas wannan ittace yarshi gashi yaga Tana kama Da Fatima, karasawa gunshi tai Tana kallashi kafin Ta kalli kawu ,kawu ban ganeshiba, mahaifinkine sultana, kallan sarkin tai hawaye na zuba a idonta, riko hannunshi tai Tana kallan yadda hannun ya koma Irin Wanda yasha wuya, Kallan shi tai kaine abbana, me kake anan sarkine ya ajjiyeka anan? Ta fada tare da rumgumeshi Tana kuka sosai bubbaga bayan Ta yake alamar tayi shiru,amma kuka take sosai dama mamanta Ta fada mata a cikin mafarki cew zata hadu Da abbanta gashi yanzu T ganshi, dagowa tayi Tana sharemai hawayen fuskar shi, abbah Da kawu yanzu zan daukeku kubar wannan gun tafiya za muyi kawai ni bazan iya barkinku anan ba, rike hannunta abbah yayi aa yata baa abu kai tsaye haka ki Bari ba yanzuba in kika fita damu ina zaki kaimu? Shikenan abba Amman dole inkai sarkinnan kara jibi yadda ya mayarmun Da mahaifi, dole zan sanarwa Da sultan nasan zai taimaka mun dashi za muyi aikinnan, kallan kawu tai kawu yanzu yaushe yace zai dawo? Anjima yace kuma sati daya yaban in fada Mai inda kika inba hakaba zai kashe ni ,sati daya nima kuma a sati daya zan fitar daku a wannan gun I promise Amman dole sai na tambaya hadin kan sultan dole saida na dpo din dake handling din wannan case din kara zan shigar Da sarki akan wannan abun wlh bazan yafe mai ba imani tsakanina dashi,.

Mikewa tayi Tana kallan gun ta ina zata Fara ne?wayarta Ta dakko Ta cire sim din sannan ta kunna wayar can sama Ta samu Ta juna wayar yadda zatai mata record da kyau, kallan kawu ta kawu Da kaji alamar zai shigo Dan Allah ki danna nan Ta fada Tana muna Mai ban sa mata key ba record kawai zaka mun saina Tara shaidata sannan zan tunkareshi, komawa gun abbanta tai, abbah na kusa fitar daku anan insha allahu, karku nuna Mai wani yashigo nan, Bari inje yanzu in kawo muku abinci sannan ta mike yanzu zanje in dawo, Da haka Ta kama hanya saida Ta rufe kofan sannan ta koma bangaren momy din, Tana shiga taga momy a parlour, aa dama baki kitchen din? Eh momy abu Na duba abaya yanzu dai zan shiga Ta fada tare da fadawa kitchen din,.

Tana Cikin dafa abincinne daji ana dawowa abun ya bata mamaki Da aka dawo Da wuri ba zata Sami damar kai musu abincinba kenan

Jin sallamar aunty mairo yasa ta fito, kallan ta aunty mairo tai Ya jikin har naga kin shiga kitchen INa masu aikin?jiki Da sauki kuma nafisan inyi aikin Da kainane aunty Ya naga kun dawo Da wuri? Eh kinsan mu iyaye ba zamu dadeba shiyasa kumama nabar yata ba lafiya ai dole inyi maza inje in dawo, murmurshi sultana tai aunty kuma har sarkin shima ya dawo? Ahhh to shiba uba bane mai tsaidashi, ajiyar zuciya zuciya sultana ta sauke Tana tunanin abunyi, kallan ta aunty mairo tai lafiya naganko haka kamar bakiji dadiba? Aa aunty ba komai kawai dai na dauka kuma acan zaku zauna har zuwa anjima ne, aa gamu dai mum dawo, ta fada tare dayin sama tabarta anan,.

Ayi manage Da wannan xuwa anjima plz

By hajara Mami natty girl

👑👑👑🕍🕍🕍👑👑👑
🕍🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍
👑👑👑🕍🕍🕍👑👑
🕍🕍👑👑👑🕍🕍
*MARAUTAR MUCE 65*
🕍🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍
👑👑👑🕍🕍🕍👑👑👑
🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍

*INDICATED TO MAMAN SHUKRA AUNTY UMMI*

Azujiyar zuciya sultana ta sauke ya zama dole ta naimi taimakon sultan itta daya dai ba zata iya wannan abun ba, ajjiye abincin tai ta nufi kofa, Gani tai masarautar Ta kara cika abun zai mata wuya Ta fice Ta kai musu abinci, tsaki tai tare da komawa tayi sama,.

Bayan sallah i,sha suka gama party dinsu,. Da sallama aunty mairo Ta shiga dakin sultana,.
Yata ki tashi ki Fara shiri Dan yanzu zaku Kama hanya, marairaicewa sultana tai kuma aunty nan da can ai duk dayane abarni anan plz, harararta aunty mairo tai comon jare Tashi kiban gu ko inyi ciki dake mikewa sultana tai aunty to wanne kayan zansa? Mika mata na hannunta aunty mairo tai wannan zakisa wata atamface purple da baki Da yellow a jiki atamfar tayi kyau sai mayafi purple, karba sultana tai idanta ya kawo kwalla duk sai take jin wani iri,mika mata abu aunty mairo tai a cikin ruba ki zuba wannan a Cikin ruwan wanka sannan wannnan in ki fito kisha, juyar Da kai sultana tai itta duk wannan abun bataga amfaninsu ba tunda auren bawai suna San junane ba, murmushi yake tai ta karba, kallan aunty Mairo tai wlh saura ki zubar ba naga kina wani ya mutsa fuskar kiba, murmushi kawai tai tare da shigewa toilet din,.

Mama dake fama Da Hindu kan tai maza itta ake jira, Mama plz inasan zuwa Zanyiwa matar sultan magana, haba Hindu wanne magana kuma?bayan kun Rabu ina ruwanki Da itta plz mama, yanzu zan dawo, saiki sauri, murmushi tai tarw Da mikewa Ta fice,.
Da sallama Ta shiga bangaren su momy, kallan ta sukai murmushi tai tare da gaidasu Ta gaida mom abun ya bata mamaki abun Da Hindu bata taba yi mataba kenan Ta gaida Da respect, kallan mom tai Mom inasan zanyi magana Da sultana matar sultan, kallan ta momy tai sai kuma Ta tabe baki tana Sama, nurmushi tai tare dayin sama,.

Da sallama Ta shiga dakin yayi dai dai Da fitowar sultana daga toilet, kallan Hindu tai tana tunanin Me kuma ya kawota, karasawa Hindu tai tare da fadin sannu Sai kuma tai shiru me zata cewa sultana kuma? Ta tambayi kanta, zama tai a bakin gadon kafin Ta Fara magana yanzu zan wuce Amman inasan inyi magana NE dake game da wata Mai Irin sunanki,amma kuma jikina ya ki tabbatar mun cewa bake bace waccan sultana kawai inaji ajikina kece, Da sauri sultana ta kalleta baa suna iri dayane? Sultan yaban labarin waccan yanzu me kuma ya kawo maganar wacccan? Tabe baki Hindu tai sako zan baki ki bata koda zata dawo bana nan, bana daukan alkawari ban cika ba gashinan na cika mata alkawarinta alkawarinta na daya daga cikin abun Da Yasa na ki auren sultan sannan kuma naso rama rashin mutuncin Da sultan yai mun sai kuna hakan bai yuyuba Amman ai nasan hakanma bai Mai dadiba any way so nake in ta dawo ki bata wannan number tawace duk sanda take Da bukatar wani abun tai mun magana saboda kawai naji inasan tai maka mata ne ta mikawa sultana, kallan number sultana tai to me xatai Da wannan, uhmmm wannan sultana da kike fada ba zata dawoba nibanga amfanin bada wannan ba, murmushi Hindu tai imma kishi kike ni baida menba Ta ajjiye takardar tare da ficewa, Da kallan sultana ta bita wai kishi abunma dariya ya bata, tsaki tayi tare da zama agan madubi Ta Fara kwalliya abunta,.
Hindu na fita suka Kama hanya dama itta daya ake jira duk jikinta yayi sanyi gani take kamar zata rabu da waniqa cikinsu in ta tafi, Amman hakan Ta daure taso haduwa Da sultan Amman bata ganshiba,.

Da sauri aunty mairo Ta karasa dakin sultana me kike haka nace kiyi kwalliya Da kankine nasan ai baki iya ba, dariya sultana tai kaji aunty wai ban iyaba haba sai kace ba Yan mataba, murmushi aunty mairo tai sannan tasa ai mata kwalliyan, haka aka xauna aka Fara tsara mata kwalliiyan har aka gama sannan ta kalli kanta a madubi Ta Saki murmushi,haba gaki kin fito amaryar ki, uhmmm kawai tace,.
Sultana na gama shirinta suka dauketa zuwa bangaren Ta nan da nan dimma saida suka sha yawu a masarautar kafin aka kaita bangaren sultan din bnagren sultana kuma,. ,.

By hajara Mami natty girl
👑👑👑🕍🕍🕍👑👑👑
🕍🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍
👑👑👑🕍🕍🕍👑👑
🕍🕍👑👑👑🕍🕍
*MARAUTAR MUCE 66*
🕍🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍
👑👑👑🕍🕍🕍👑👑👑
🕍🕍👑👑👑🕍🕍🕍
Chapter 27 · 0% Book details