← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 43

Sashe 3

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masarauta
Wazirine zaune kusa da sarki su biyu, a hankali sarki ya Fara magana waziri ina San zanje dakin ajiya kuma kasan IN zanje bana shigata irin na sarki saboda haka kace wa dogarai Yau nace bana bukatar ganinsu hutawa zanyi ina tunanin ka fahimta dan banasan kowa yaga naje gun ,an gama ranka ya dade ya fada tare da ficewa, yana fita sarki ya canza shiga Ya fice ta kofar baya sannan ya rufe fuska da kafarshi Ya taka yana tafiya, ya danyi nisa Ya nufi wani gun da kwata kwata mutane basa yin gun Ma, wani bawane yazo wucewa yaga wani nayi gidan ajiya alhalin yasan an hana hakan yasa yabi bayan sarki yana dabe dan yaga inda zaije, dai dai da sarkin zai bude kofa yana inuwa alamar ana binshi ,murmushi yayi aidama yasan duk sanda zaizo wannan gun dolene yayi kisa hakan yasa yai fuska kamar baiga kowa ba ya shiga, shima bawan kuwa bai fasa biba, labewa Sarkin yayi abayan kofan saida bawan ya shiga ciki sannan ya rufe kofan yasa kwado ya rufe, bawan Ya juya baya yana dube dube sarkin yai gaba hakan yasa bawan bin bayanshi Sun danyi tafiya kafin bawa ya Fara fadin wai waye wannan? Da gudu sarki Ya kwasa hakan yasa bawan kwasar gudu shima,.
A razane bawan Ya taka burki ganin wani mutun da yayi a cikin cell, ya dago yana kallanshi a razane Ya furta SARKI ABDULSALAM?

BY HAJARA MAMI NATTY GIRL
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 6*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Da sauri ya karasa gunshi yana fadin sarki abdulsalam dama baka mutuba me kake anan? A hankali sarkin Ya fara magana ME yasa ka biyoshi bakasan bana San ana kashe mutanena saboda niba bakasan shi mugu bane, kallanshi mutumin yayi waye mugu yau zan fitar da kai anan zan fadawa sarki Abdullahi na ganka nasan zaiyi murna da hakan, hawaye sarki abdulsalam ya Fara yana jijjaga kai,.

Jin ANA tafi yasa bawan juyawa mikewa bawan yayi ganin sarkin su yasa ya karasa gunshi yana fadin sarki abdulsalam bai mutuba Ashe yana nan....... Saikuma yai shiru tanu abun da tsohun sarkin nashi yace mai mugune me yasa ka biyo shi Da sauri ya kalli sarkin nasu yana jijjaga kai, Amman ba wannan bane mugun badai sarkin muba, matsawa kusa dashi sarkin yayi nina kawo shi nan ai nana sashi anan ina jiran wani lokacine da zan kashe shi, Da sauri bawan ya kalleshi saboda me? Saboda kunfi sanshi kun sanshi akan ni alhalin nima inasan mulkin kuma nine babba saboda da ME bazan yanke wannan hkuncinba? Da sauri bawan ya kalleshi aikuwa kaiba sarki mai adalci bane kuma yau zan tuna ma asiri wlh, gadan gadan Ya nufi sarki, yana zuwa saijin saukan wuka yayi a cikinshi, kallan Cikin yayi ya kalli sarkin kafin yai kasa yana shahada nan take ya mutu,.

Kuka sosai sarki abdulsalam yake zama sarki Abdullahi yayi kusa dashi karka wani damu ni bani nace Ya biyoniba shishigine irin nashi kuma kasan duk zuwa ina samun irin su, cikin kuka sarki abdulsalam ya Fara magana wai ME kake jirane ka kasheni kawai mana, no no bazan kashe kaba ai nasan Yarka zata zo agabanta zan kashe ka ai karka wani damu, kallanshi sarkin yayi aikuwa babban kuskure zaka tabka dan ittace ajalinka itta zata tuna ma asiri inba kasaniba ,wata dariya yasa aikuwa zanso ganin wannan ranar tab kace akwai shagali, Hmmmm kawai sarkin yace bai kara cemai komaiba, haka yaitaiwa kanin nashi surutai yana bashi labarin yadda zai kashe shi, daga baya Ya mai sallama sannan Ya fita da gawar wannan bawan,.

Tunda suka shigo gombe take ta kalle kalle garin yai mata kyau tana feeling wani happy ta rasa dalili, haka suka sauka a tasha da kyar suka Sami wajen kwana dan gobe zaai sabin diba a masarauta gobe zataje dan shiga,.

Tans bacci ta Fara mafarki

Dan faraaa matar take kallan sultana barka da zuwa garinku masarautar mu Amman sultana sai kina hadawa da addua fa, kallan ta sultana tai na gode Amman Dan Allah ke wace, murmushj matar tai babanki xai fada miki, kallanta ta sake yi kawu ne zai fada mun? Aa bashiba mahaifi Wanda ya haufe ki, zaro ido tai yana rayene? Kwarai kuwa, to yana ina? Yana masarautar mu, ina zuwa zan ganshi taya zan gane shi? Aa ba zaki ganeshi ba shi zai ganeki, sannan IN kikaje karki bari ina ganin fuskarki sosai dan yan garrin manya yan iskane suna bata matane, zaro ido tai bama zan Bari aga fuskata ba, dariya matar tai bance kina kin bude fuska bafa, murmushi sultana tai,.

Washe gari Ta gama shirinta har wajen masarautar kawu Ya kaita sannan ya Mata sallama mtanene a jere kuwa yana jiran kira

by Hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 7*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```

Kallan masarautar tai daga wajentama abun kallone balle cikinta,.

Baccinshi yake mai dadi karar da aka sakine ya tasheshi da adduar bacci ya tashi, tare da mikewa Ya bude window, tsaki yaja yau za debi sabin bayi kenan ni na rasa me yasa ake samun bayi alhalin kullun kisa ake a masarautar mtswww yaja saki, gabanshine Ya fadi da sauri Ya dafe girjinshi tare da karanto addua, sannan ya Sami saukin dukan girjin nashi ya shiga wanka,.

Budewa musu gate din akwai ana sanarwa mata subi layi mazama haka haka kuwa sukai sannan wani yazo Ya fara musu jawahi zamu Zaga da ku KO ina Dan daukarku a kowanne sashe da ake da bukata ,basuce komaiba sudai sunyi tsaye kamar sojoji, gaba Wanda ya gama musu magana yayi suka bishi a baya,.

Wata matacw ke zaune a parlour Ta caka uban dan kwali Ta daura daya kan daya ga bayi a kusa da itta suna mata hidima, Da sallama wata baiwa Ta shigo ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, sannan ta kalli matar gimbiya sabin bayine inkina da bukata, kallan jakadiyar tayi ina bukatar masu tsafta da kyarki gudu biyar, angama ranki shi dade Ta fada tare da mikewa,.

Tana zuwa Ta zabi gudu biyar din kamar yadda ta fada sannan Sukai gaba, haka akai Ta zagawa dasu ana diba Amman har wannan lokacin ba a dauki sultana ba duk tabi Ta damu kardai aki daukanta ace ta hakura,.

Part din Maman sultan suka nufa itta Ma baiwa Ta isar mata da sako sultan dake kusa da itta ya kalleta momy me zakiyi da bayi kuma banda wadannan da kike dasu? Murmushi tai ta kalli jakadiyar autana yace basai Na dauka ba amma ki dakko min daya mai hankali saboda wata rana, mikewa tayi Ta fice dan cika aiki kallanta sultan yayi wato dole saikin dauka KO momy? Shafa kanshi tayi kawai zan daukane saboda wata rana jijjaga kai kawai yayi baice komaiba,.

Baiwar Na fita ta Fara kallan Yan matan gun idonta ya sauka kan sultana da idonta ya cika da kwalla amma fuskarta a rufe, kallan bawan kusa da itta tayi a dakko waccan ta fada tare da nuna sultana, ajiyar zuciya Ta sauke najin dadin An zabeta da sauri Ta mike Har hakan yasa baiwar murmusawa,kallan sauran bawan yayi To ku zamu wuce daku dakin girki zamu raba muku sauran aikin, Da haka sukai gaba,.

Kusa da jakadiya sultana ta karasa har kasa tana fadin ina wuni? Murmushi matar tayi lafiya qlau ya sunanki? Sultana, zaro ido tai sultana dakyau shigo muje, tai gaba sannan ittama tabi Bayan jakadiyar,.

Da sallama suka shiga parlour nan take sultana taji gabanta ya fadi idonta ya sauka kan momy dake kallanta kafin Ta kalli sultan da hankalinshi ke kan Waya, ganin jakadiya tayi kasa hakan ittama yasa tai kasa Ta fadin abin da jakadiyar Ta ke fada, kallanta momy tai ya sunan ki? Sultana ta fada kamar mai shirin kuka, dago kai sultan yayi jin mai irin sunan shi idonta kawai ya gani dan Ta rufe fuska idon ya tara hawaye, tabe baki yayi kawai yaci gaba da abun da yake, kallanta momy tai tana murmushi mai sunan danace ma ashe Ta fada Tana kallan sultan,uhmmm kawai yace.

To sultana ina miki barka da zuwa wannan masarautar da fatan zaki rike amana indai kika kasance Mai hakan zanji dadi Amman fa indai kika ki rike amana anan zamu bata gaskiya, kasa sultana tai da kai tare da fadin insha Allahu zan kiyaye, murmushin jin dadi momy tai sannan tsafta ki kasance Mai tsafta hakan zaisa IN kara sanki sannan ki ksance mai addini, duk zan kiyaye insha Allahu, kallan jakadiya momy tai kije ki kaita part din bayi na wannan bangaren nawa gobe ki taho da itta zan baata aikin da Ya face Ta dinga mun, angama ranki ya dde jakadiyar ta fada, sultan ne ya katse su tare da fadin ke baki bude fuska NE?kallanshi sultana tai Dan itta kadaice mai rufe da fuska agun nan take mafarki ya dawo mata inda waccan take ce mata kartana barin ana ganin fuskarta yan iska nada yawa a wannan masarautar hakan yasa Ta dubul bulce tana fara kinkina, tsaki yaja tare da fadin you can go, Da sauri ta mike jakadiya kuwa bata mikeba tunda bata San me yace ba, shikewa mamaki yake Ta gane mai yace batai kama da wadda tai karatu ba, tabe baki yayi sannan suka wuce da jakadiya

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 8*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com
Chapter 3 · 0% Book details