← Book details Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 43

Sashe 11

Masarautar Mu Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri bawan yaje gurinta, wai kizo, ni Ta fada tana nuna kanta,eh ke mana inji gimbiya Hindu, kallan gun tayi kafin Ta sauke ajiyar heart tabi bayanshi, Tana zuwa Ta duka Ta gaidata, bata amsa illah kallan Wanda yake dauke da bakan tayi ka bata tayi in gani, kallan sultana tai aiban iya meye hadina da itta,kallanta Hindu tai hake kikewa sultan magana kina Mai magana akai baki da respect ne? Sosai ran sultana Ya baci bataa San raini da gani kuma yarinyar ba zata fitaba, mikewa tayi Ta nufi gun, karba,.

Sau uku tana yi Amman bata samu inda ake San ta samuba, tsaki Hindu taje ke wacce irice kamar ba daga kauye kike ba, kallan ta sultana tai ranta yana kara baci, sai kuma tai kasa da kai ranki ya dade AI a kauyen namu ba mawunwata bane kinsan mayunwatane kesan koyan harbi Dan su dinga farautar abun da zasu ci, kinyi hakuri da abun da zan fada ranki ya dade muba mayun wata bane, huci kawai Hindu take wai itta baiwa ke cewa mayunwaciya to haka take nufi mana tunda yanzu dai itta ake koyawa harbi, mikewa tayi Ta nufi kusa da sultana,tai facing nata har tana jin nunfashinta, kallan Hindu kawai take kafin Ta dauki hannunta Ta bata wani kyakykyawan Mari Wanda har saida yasa daurinta kusan cirewa Amman tai saurin taro shi, rike kuncinta sultana tai kafin Ta kalli Hindu idonta yayi jaaa ranta ya baci Amman ba damar daukan fansa,.

Ba tare da tace da Hindu ba ta raba ta gefenta zata wuce hindun Ta Sa mata kafa saiii ji kake timmmmm Ta fadi a kasa ai kuwa yan garin suka fara dariya, murmushin mugunta Hindu tai kafin Ta karbi bakan Ta Fara harbawa cike da kwarewa Dan mina Ta Bala,in ban mamaki dama haka Ta iya harbi,.

Mikewa sultana tai ta tafi inda Ta nufa tana shiga parlour bako sallama ta jin gina Da jikin kofan sai a lokacin wani zaffafen hawaye ya Fara zubo mata, Kasa tai kawai tana kuka itta aka mara yau abun da ba,a taba mataba saidai bata saniba KO tana yarinya hakan ya faru da itta Amman itta back Wanda ya taba marinta,sultan dake zaune a parlour yana danna system dinshi yayi shiri da gani gun aiki zaije, ganin Ta shigo Tana kuka yasa ya tsaya yana kallanta, gyaran murya yayi da sauri Ta daga kai Ta kalleshi sai kuma tai saurin mikewa kwata kwata bata San yana ciki ba, hanyar kitchen tayi, kafin Ta karasa ya kirata, juyowa tayi ganin itta yake kallah yasa ta juya Ta karasa gunshi tai kasa tare da fadin ina kwana? Me ya sameki kike kuka? Ba komai, har zaiyi magana sai kuma ya fasa kar Ta dauka ya damu da itta sosai ne, OK Allah yaa kare kiyi sauri ki mun breakfast patien na jirana, to ranka ya dade,.

Hindu ce Ta shigo tare da fadin karata kika kawo ai wannan ma kadan miki badai a kasana kike ba wannan masarautar muce ba yadda kika iya dani kuma Wanda kika fadawa shima ba abun da zaimun tunda dai masarautar muce shima bai kaini power ba ta fada tana kallan Sultan Tare fadin KO Yaya?get out Ya fada ranshi a bace, what yaya ME kuma nayi, Cikin tsawa yace how dere you zaki shigo min ba sallama sannan kizo kina gaya mun magana can you please get out? Turo baki tayi sorry bari inje inyi sallamar bata jira Mai zaice ba ta fice tare da fadin salamu alaikun, mikewa sultana tai tai kitchen jiki ba kwari zata koyawa wannan yarinyar hankali abun Data fada kenan,.
Amsa sallamar yayi Ta shigo Ta zauna kusa dashi mikewa yayi ya zauna a wata kujeran, kallan shi wai Dan Allah yaya Maye Haka nan gaba fa aure zamuyi, wani kallo yai mata ni zaki aura? Yai wani murmushi ni kuma bazan aurekiba, dan marairaicewa tayi saboda dame yaya? Saboda bana sanki nasan inna aurekima ba zan iya miki adalciba saboda haka kiyi hakuri kawai, ni naji karka soni aini ina Sanka tsaki yayi baice komaiba yaci gaba Da abun Da yake itta kuwa sai zuba take mai itta a dole zata shawo kanshi ne

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 27*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Bayan Ta gama Ta jere a dining sannan tace Ta gama, tun kanya tashi Hindu har ta karasa gun, ta zauna tsaki yayi tare da zuwa ya zauna, daukan flask sultana tai zata Fara zubamai Hindu tai saurin rikewa tare da harara sultana Na baki permission ki zubawa mijina abinci ne? Kallan sultan Hindu tai itta shima yake kallo dauke yayi ganin hakan yasa Ta sakewa Hindu flask din, Tana tsaye har Hindu ta gama zubamai sannan ta dawo Ta zauna kallan sultana tai saiki zuba mun aiko, murmushi tai tare da Fara zuba mata Hindu sai hararar Ta take, kallan sultana tai kewai ya sunanki?sultana Ta fada a kaice, kuttt wlh baki isa ba dole ki canza suna aba yanzu hakama asiri kikai Mai wlh abun yana ban mamaki kuma zan karya asirin shine harda Sa irin sunan shi, murmushin takaici sultana tai hakama shima sultan din murmushi kawai yayi Hindu masifa, garin Ta mika mata glass cup din Ya subuce ya fadi akasa ya fashe, a hargitse Hindu ta Mike Da niyar kai mata mari sultana tai saurin ja baya sultan kuma yai saurin rike hannun Hindu, garin matsawa sultana ta taka kwalba hakan yasa Ta Saki kara tare da runtse ido Da sauri sultan Ya karasa gunta Ya rikota ya kalli kafar jini Na fita.

Kallan shi Hindu tai yaya baiwace fa ka riketa ta, harararta yayi Ya kalli kafar sultana dake jini, sannu ya fada ma a hankali, batace komaiba sai hawayen Da take, rike hannunta yayi ya kaita parlour Ya zauna Da itta ki jirani ya fada tare da yin sama, kallansu kawai Hindu take kafin Ta fice Da gudu, murmushi kawai sultana tai,.

Da first aid box ya fito, Ya zauna a kasa Tare da riko kafar tata, daurewa kawai take itta tasan ME take ji inya tabata,runtse ido tai, har ya gama aikin Ya dako yana kallanta, murmushi yayi Ta wani runtse, raguwa ya fada a hankali ya kurawa idonta kallo yana San ganin face dinnan Amman baisan taya zaiyi hakan ba, jin ya daina mata yasa Ta bude ido idonta ya sauka kan nashi murmushi yai mata tare da fadin sannu, dauke kai tayi tare da fadin Na gode ,mikewa yayi ki shigar mun dashi daki nina tafi yana kaiwan nan ya dauki nashi ya nashi ya fita, Da kallo Ta bishi shi duk yau sai taga ya canza mata kamar ba shiba, murmushi kawai tai Tare da mikewa tana dingishi,haka yau tayi aikin nata,.

Hindu kuwa part din Maman taje tasa mata kuka, mama yaya sultan baya sona Allah kinga yadda yamun rashin kutunci yau akan wata baiwa, kallan Mama tai wacce baiwace itta Yar wacece har da za, ai miki rashin mutunci akanta, daura kanta tai a cinya mama, mama ki bari zan dauki mataki, yauwa gara ki dauka in ba zaki iyaba kimun magana ni zan daukar miki farin cikinki shine nawa ai, murmushi Hindu tai kawai,.
Dady ki yace ki shirya ya hada miki party dawowa,gobe zaai saboda haka saiki shirya, yace duk wata baiwa zata iya saka kayan da ba uniform ba Dan kawai tazo tayaki murnan dawowa, dariya tayi tare da rumgume mamanta shiyasq nake kara sanku wlh kuna faranta mun rai ,zan shirya Da wannan party zan fadawa yaya sultan ya shirya

By hajara Mami natty girl
👑🕍👑👑🕍👑👑🕍 🕍👑🕍👑👑🕍👑👑
🕍👑👑🕍👑👑🕍🕍🕍👑🕍👑👑🕍🕍👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍🕍
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. * *MASARAUTAR MUCE 28*
🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍
👑👑👑👑👑🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑
🕍🕍🕍🕍🕍👑👑👑👑🕍🕍🕍
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Yau a gajiye duk suka koma dakinsu, kallan Zuwaira sultana tai kinga har yanzu Zulai bata zoba,tabe baki Zuwaira tai yo ni AI naci abinci a namu bangaren ke wai baki cine? Aa ni bana ci gani nai baa ce in dinga ciba to me zai kaini, gaskiyane cewar Zuwaira da sallama Zulai Ta shigo, zama tayi Tare da fadin washhhh, sannu suka ce Mata,kallan su tai kunsan kuwa gobe ance kowa yaci kwalliya Za,ai abu a wannan masarautar, kallan ta sukai me kuma Za,ai? Wai bikin dawowar hindu mana, kallan ta Zuwaira tai banda wanda muka hada mata a bangaren mamanta kai wannan suna asarar kudi, uhmmmm kawai sultana tace,Ta zuba musu abincin suka zauna suna ci,.

Washe gari Cikin farin ciki Hindu ta tashi yau za,ai mata perty zata gasa kuwa,.
Chapter 11 · 0% Book details