Sashe 9
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan few minutes Rafi'ah ta dawo da tray a hannunta me dauke da snacks sai exotic da glass cup a gefe, calmly ta ajiye a gabansa ta ce "Here it is Yaya" Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Thanks" mikewa tayi yayi saurin riko hannunta ta zauna gefensa ya ce "Ina zaki je?" ta ce "Abinci zan kawo maka" ya ce "No, wannan ma ya isa" ta juyo tana kallansa ta ce "Kace fa baka ci komai ba" Ya ce "Ai zanci wannan" ta dan matsa baya a hankali ta ce "Alright" kara matsowa yayi gefenta ya kamo hannunta, ya kalli Babyn dake bacci hankali kwance sannan ya kara kallanta ya ce "Are u with me Fatima?" Ta daga masa kai a hankali, silently ya ce "I just want to tell u that, right from the day i met u, i love the way u smile the way u laugh, and u know what?" Girgiza masa kai tayi kanta a kasa tana kallan hannunta dake cikin nasa, limshe ido yayi ya tattaro courage dinsa ya ce "I notice that it was lo..." Shiru yayi jin an bude kofar parlorn, tayi saurin jaa baya tana kallan Mummy dake kallansu, ta ce "Meye haka Jawad?" Kansa ya dan shafa ya ce "Ehh, dama abu ne ya fada mata a ido shine na hure mata" Mummy ta zauna akan kujera ba tare data kalli Rafi'ah ba ta ce "Yayi kyau, when did u came back?" Ya ce "Ban jima ba, banma je gida ba, but daga nan can zan wuce" ta ce "Ohk" ya danyi kasa da murya ya ce "Congratulations once again for the cute Baby" ta ce "Thank u, baza kaci abinci bane?" Ya ce "No, wannan dinma ya isa" sai lokacin Mummy ta kalli Rafi'ah dake zaune gefe tana jujjuya ring din hannunta ta ce "Kar6eta ki bashi waje yaci abinci" mikewa tayi a hankali ta kar6i Babyn sannan ta nufi hanyar fita a parlorn, Mummy ta mike tabi bayanta ta ce "Idan ka gama zamu wuce tare" ya ce "Ohk to" daga haka taja masa kofar. Cikin minti kadan ya gama cin abinda zai ci ya mike yasa phone dinsa a pocket sannan ya wuce sink ya wanke hannu ya dawo ya dauka key din motarsa, a parlor ya tarar da duk ilahirin gidan amma banda Rafi'ah, ya dan durkusa ya ce "Zan tafi Ummi Allah ya raya da imani" Ummi dake murmushi ta ce "Ameen" Gwaggo ta ce "To ni tinda nazo banga Hadiza tazo barka ba dama kuma..." Da sauri Ummi ta ce "Tazo mana Gwaggo, tin muna asibiti ai tazo" Jawad ya mike ya nufi kofar fita, Ummi ta ce "Allah ya kiyaye" Mummy da Anty Salma suka mike sannan sukai musu sallama suka tafi. Har suka isa gida Mummy da Anty Salma hirarsu suke, shi dai yana ta driving but zuciyarsa ya tafi wani tinani daban, what if Mami taga ya sauke su fa? ta kuma tabbatar tare suke? dan karamin tsaki yaja yaci gaba da tuki, Mummy ta dan kallesa ta ce "Lafiya da tsaki haka?" Ya ce "Ba komai" ta6e baki tayi taci gaba da bawa Anty Salma labarin yadda Rafi'ah ta sha wahala a rainon cikinta. Dai dai kofar gida Jawad yayi parking, Mummy ta ce "Ya zaka dire mu anan young man?" Ya dan shafa tilin gashin dake kansa ya ce "Eh, zan fita an jima kadan that's why" Mummy tayi masa wani kallo ta ce "Ko kana tsoron uwarka ba" daga haka ta fito a motar Anty Salma ma ta fito suka wuce ciki, sai bayan shigarsu da minti 10 sannan ya gyara motar ya danna horn, bayan an bude gate ya shigar da motar yayi parking sannan ya fito ya nufi entrance din gidan, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo, ta mike a hankali ganinsa ta ce "Yaya sannu da dawowa" ya ce "Thank u, Mami fa?" Ta ce "Tana kitchen" daga haka ya wuce kitchen walking gently, a bakin gas ya sameta tsaye tana gauraya pepper chicken din da take, ya rungumeta ta baya yana murmushi ya ce "Mami" ta danyi murmushi ta ce "Ahmad, saukar yaushe?" Ya ce "Yanzun nan, aiki kike?" Ta ce "Kai nake yiwa pepper chicken, naga basan cin abincin gidanmu kake ba, kaga koka tafi dashi sai kai warming dinsa, ai kana da microwave ko?" Ya ce "Yes i have, thank u mother" ta ce "To kayi wanka kafin na karasa" ya ce "Alright to" daga haka ya fita a kitchen din ya nufi dakinsa na da, ba kowa a dakin amma a gyare tsaf tsaf, ya cire rigar jikinsa ya dauki towel ya shiga toilet. Kananun kaya ya saka sannan ya fito a dakin, yayi kyau sosai da sosai sai kamshi yake, ya leka kitchen yaga bata nan, hakan yasa ya wuce part dinsu yana balle botton din hannunsa, a parlor ya sameta tana zaune ta zuba masa papper a plate sauran kuma tasa a warmer, ya zauna gefenta ya ce "Is this all for me Mami?" ta ce "Sure" a hankali ya jawo center table din gabansa ya fara cin naman, kusan minti 10 ba wanda yayi magana a cikin, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ahmad" dagowa yayi yana kallanta ba tare daya amsa ba, ta ce "Yaushe zakai aure ne Jawad? 37yrs kana zaune min a gida haba dan Allah, yanzu ko Sadeeq da yake shekara 25 ai zai iya aure, ya gama degree dinsa yana masters, amma kai ka gama komai kana aiki, kana da gida sai dai kawai kaje gidan kayi bacci ka tashi ba mace, gidanma yana maka dadi ne a haka?" Sauke kansa yayi daga kallanta ya ce "Very soon insha Allah, ki daina damuwa" ta ce "To a ina yarinyar take, menene dalilin da bazai sa akai tambaya gidansu ba, why not now?" a hankali ya dauki tissue yana goge hannunsa ya ce "Saboda ta haihu ne, so i have to wait sai ta gama shayarwa" zaro ido Mami tayi tana kallansa, lokaci daya taji zuciyarta na bugawa, cikin sauri ta ce "Wa kake nufi ne, a ina take?" Ya ce "Wata yarinya ce, mijinta Allah ya masa rasuwa, dama kuma tin kafin ya aureta muna tare, so iyayenta suka aura mata shi" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya kyauta, amma meya kaika auran bazawara Jawad? Ga 'yammata kaca kaca a fadin duniyar nan ka rasa wacce zaka aura sai bazawara" ya ce "Ita nakeso Mami, idan kika ganta baza kiyi tinanin ta haifi diya ba, dan itama bata fi diyar ba, bata cika shekara 19 bama a duniya" Mami ta masa wani kallo ta ce "A ina take, and what's her name?" Ya gyara wristwatch din hannunsa ya ce "Sunanta Zarah, tana zaune a unguwar rimi, amma iyayenta ba anan garin suke ba" Mami ta sake sauke biyayyar ajiyar zuciya ta ce "Tinda haka ka zabarwa kanka Allah ya kyauta, ni dai bazan maka fatan sharri ba, fatana ka samu wacce zata kula da kai" a hankali ya ce "Insha Allah" Mami ta ce "Kaji Rafi'ah ta haihu ko?" Ya juyo surprisingly yana kallanta ya ce "When?" Ta ce "Kwana hudu kenan, ai tayi~tayi ta haihu da kanta ta kasa, kasanfa ba wayo ne, da wata babbace tsaf zata iya haihuwa, to yarinya dai sai data galabaita ko hannunta bata iya dagawa sannan aka mata CS aka ciro mata diya mace, tana nan duk ta kara karewa kamar ba a cikinta aka ciro wannan 'yar ba, kuma diyar sak kama da ubanta, nidai nace wannan mutumi ya bar mata babban tabo a rayuwa, ai nasan duk inda zata shiga da 'yar nan sai dai ace kanwarta ce, ba wanda zaice ita ta haifeta ta, shi dai ya cucesu ya maida musu 'ya bazawara" shidai shiru kawai yayi yana saurarenta, caan ya danyi tsaki ya mike, ta ce "Ina zuwa?" ya ce "Gidana" ta ce "Sai gadarar cewa gidana gida ba mata, Allah ya kiyaye, kuma wallahi ka rage wannan uban gashin" ya dan shafa kansa ya ce "Gobe insha Allah" daga haka ya dauki food flask din ya fita ta bishi da kallo. Few minutes ya kai shi gidansa dake old GRA, ya fito ya bude gate sannan ya shigar da motar yayi parking ya koma ya rufe gate din, key yasa ya bude kofar shiga gidan, ya zare key din sannan ya maida ta ciki ya tura kofar, kujeru ne masu kyau a parlorn sai TV sai kuma air-conditioner dake kunne, ya wuce upstairs ya shiga dakin dake farko ya rufe kofar, dakin tas tas ya sha farin bedsheed, ya kwanta saman gadon ya jawo wayarsa ya kira Aliyu, bayan ya dauka ya ce "Ka dawo ne Aumad?" Jawad ya limshe idansa ya ce "Ehh, na dawo dazu, kazo mana sai mu karasa magana" Aliyu ya ce "Sai na tashi a aiki kenan, kana gida ko?" Ya ce "Ina gidana, zan baka address" Aliyu ya ce "Alright then, saina gama zan ta6a ka" daga haka yayi hanging wayar, number Rafi'ah yayi dailing, sai daya kusan tsinkewa tayi picking, ya ce "Dear" a hankali ta ce "Yes, i hope u reach home safe?" Ya ce "Fine, how is my Baby" ta ce "She's sleeping" ya ce "Ki shafamin ita" ta ce "Ohk, dazu kana min magana kuma baka karasa ba" ya ce "Zan karasa but inaso sai ina kallanki kina kallona" ta danyi murmushi ta ce "Alright to, ya gajiya" ya ce "Ba wani gajiya, how are u feeling now?" Ta ce "Da sauki sosai" ya ce "Allah ya kara maki lafiya, i will call u ltr, don't off ur phone pls" ta ce "To, sai anjima" ya mike ya ce "Thanks Baby" daga haka ya katse wayar, kallan wayar ta dinga yi tana tinani, ko to bataji daidai bane, ko kuma ce mata yayi ta gaishe da Baby?, ta dan ta6e baki ta mike ta shiga toilet kar ruwan wankanta yayi sanyi. Da yamma Mami tasa Sadeeq ya kaita gidansu Rafi'ah kamar yadda Abi ya bada umarni, bata wani jima ba saboda surutun Gwaggo, bayan taga Baby da Rafi'ah ta mike ta musu sallama, Gwaggo ta kalli Ummi ta ce "Ya dai fi babu