← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 46

Sashe 14

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

😄 *Jawad zai bi Mummy ko dai ya fasa ya bi umarnin uwa?* 🤭

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_8_

Komawa Jawad yayi ya zauna akan sofa yana kallan Mami data kafeshi da ido, ya sauke kansa kasa ya ce "Is Abi out?" Harara ta dalla masa ta ce "Why won't u call him" daga haka ta wuce part dinta, mikewa yayi a hankali ya shiga daki ya zauna bakin gado, sosai kayan jikinsa suka masa kyau, ya mike yasa glasses dinsa sannan ya fito a dakin ya nufi part Mami, a parlor ya sameta suna zaune tana wa Ikram tsifa, ya zauna akan kujerar dake opposite dinsu, Ikram ta ce "Yaya dan Allah ka kaini gidan Baffa idan fita za kai" ya dan hade rai ya ce "Who is your driver?" Ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami ta ce "Ina zakaje yanzu kaida ba jin dadi kake ba?" A hankali yana girgiza key din motarsa ya ce "My house" ta ce "To do what?" Ya ce "Yau zan koma tinda naji sauki" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen" mikewa yayi zai fita Ikram ta ce "Yaya na taso mu tafi dan Allah" ya ce "No, i'm not going that way, ki bari Sadeeq yazo ya kaiki" daga haka ya fice a parlorn ya rufo musu kofa. cikin quick light steps ya karasa part din Mummy ya murda handle din ya shige, ba kowa a parlorn ya zauna akan kujera yayi sallama in a low voice, Mummy ta fito rike da wayarta a hannu ta zauna tana kallansa ta ce "So u came?" Ya dan shafa gashin kansa ya ce "Yes, kiyi hakuri abinda ya faru dazu" Mummy ta ce "No, ba komai ai uwa ce, ni kuma kaga ban haifa ba" ya dan zaro ido ya ce "Noo, ba haka bane, ni duk na daukeku a matsayin iyayena" ta ce "Ohk, dama akan kayan da ka kai jiya ne, mungode Allah ya saka da alkhairi" silently ya ce "Ameen" Mummy ta ce "Amma do u have any feeling for her?" A hankali ya dago ya kalleta sai kuma yayi shiru, Mummy ta ce "Yes u have, but y kake ganin hakan zai faru Jawad? Ni dai bazan muku fatan tsiya ba, amma kafi kowa sanin halin mahaifiyarka, kuma ba lallai ne ta yarda ba, beside bama san zuwan Rafi'ah gidan nan take ba balle ace ta zama matar dan ta" shiru Jawad yayi yana jin Mummy, bayan ta gama ya ce "Ba abinda zai faru insha Allah" Mummy ta ce "Ohk Allah yasa, Allah kuma ya za6a muku duk abinda yafi alkhairi" ya ce "Ameen" ta ce "And then ni baza'a ji wannan maganar a bakina ba, idan ta amince kun fahimci junan to, amma duba da abinda ya faru da ita a baya bazan sake takurata tayi aure nan kusa ba" Jawad ya ce "No it isn't ur fault Mummy, ai kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa" ta ce "Hakane, but there is a reason" daga haka ta mike ta ce "Ya jikin naka?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Allah ya baka lafiya" daga haka ta shige daki, mikewa yayi ya karasa kofar parlor ya bude a hankali yana lekawa, ganin ba kowa ya fito ya fice a gidan da sauri.
A ranar duk mutanen da suka halacci suna suka wuce, Ammi tazo da wasu 'yan uwanta mata biyu suka kawo akwatina guda biyu na kayan baby dana Rafi'ah, sosai Khairiyya ta makale Imaan a jikinta wai da ita zata tafi, bayan da suka tashi tafiya Ammi ta danyi mata nasiha daya sa gaba daya jikinta yayi sanyi, karshe dai sai da tayi kuka. Kwana uku da suna Ameera ma ta koma school, Ummi ta koma aiki, gidan ya rage daga ita sai Saudatu.
Chapter 14 · 0% Book details