← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 46

Sashe 33

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*DEDICATED TO MY GROUP MEMBERS ❣️*

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_18_

Kuka sosai ta fashe da shi tana kallansa, ya juya ya shiga zai rufo kofar tayi saurin tarewa ta ce "Pls don't do this to me Doctor, meyasa zaka rabani da farincikina, nina riga na yafe maka ka bani Baby na mu tafi for God sake" ta bude kofar ta shiga cikin parlorn ta dauki Imaan zata fita ya tare kofar, share hawayen idanta tayi ta ce "Let me go out pls" Yusuf yadan kalleta kafin ya ce "Idan kinaso ki fita ki ajiyemin daughter na" ta masa wani mungun kallo cikin tsawa ta ce "Stop calling her your daughter, she is not, wallahi kaiba mahaifinta bane, gara na bawa wani caan da bansan da shi ba, baka da wani maraba da mutumin da yayi raping mace baisan ta samu cik..." Wanka mata mari Yusuf yayi tayi saurin dafe wajen ta durkusa a kasa, ganin haka yasa Imaan ma ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta, limshe idanuwansa yayi hawayen dake makale a idansa suka zubo, gaba daya ya rasa me yake masa dadi, maganar da Jiddah ta fada zaiji dashi ko kuma rashin hankalin da Rafi'ah ke masa, mikewa tayi ta gyarawa Imaan zama a jikinta ta ce "Wallahi saina tafi da ita, i'm going with her no matter how, ka matsamin na fita" ta karashe maganar tana kuka sosai, juyawa yayi yasa sakata a kofar sannan ya fisge Imaan a hannunta ya ajiyeta gefe yana kallanta ya ce "Idan kinasan tafiya kije ke dai" tayi kan Imaan zata dauketa ya fisgota ta fado jikinshi, daga ta yayi ta fasa ihu ya shiga da ita part din Jiddah ya ajiyeta akan kujera, yana jin Imaan na kuka haka ya rufe kofar yana kallan Rafi'ah dake kuka ya zauna gefenta ya ce "Sai ki fadamin abubuwan da kika mata yanzu yanzu na biyaki ki fita min a gida" ta dalla masa harara tana ci gaba da kuka, mikewa yayi yasa hannayensa a pocket dinsa ba tare daya kalleta ya fara magana cikin cool voice dinsa kamar haka "I thought you heard all what Jidda said, kinga ba laifina bane, su suka sa na tsaneki naji banasan rayuwa dake, nayi tinanin idan kikaji abinda ya faru kece mutum ta farko da zaki tausayin, kinsan yadda nake sanki more than anyone else, i can't betrayed u for no reason Fatima, nace maki ki bari gobe zan kai miki ita but u followed me and start shouting at me kamar wanda na miki sata, ko sata na miki ba zaki hakura da tsawan kimin magana a nutse ba, shekara nawa na baki a duniya Fatima? do i deserve such things, wane irin soyayyane ban miki ba kafin a shiga tsakaninmu? Or do u think i'm just pretending ba sanki nake ba?" Shiru yayi yana kallan yadda take kuka, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "And u are trying to said bani da maraba da wanda yayi raping mace baisan ta samu ciki ba, how do u call this a rape? nasan akwai wahala laulayin ciki da kuma haihuwa, but this doesn't mean ki zauna kina fadamin maganganu marasa dadi akan yarinyar dana haifa, at first ur Mum slapped me, she insulted me and she called me munafiki macicu azzalumi ta kara da cewa na cucesu Allah ya isa sannan na fita muku a gida kafin ta min illa, this words touch my heart more than u know" limshe jajayen idanuwansa yayi ya ce "Anywhere ki yafe min duk abinda na miki, it wasn't intentional na kuma gode maki with this cute Baby, Idan a zaman da mukai akwai abinda na miki bakiji dadi ba u pls forgive me, zan baki Imaan amma ba yanzu ba kamar yadda na fada miki a farko" bude idanuwansa yayi ya bude kofar parlorn ya fito, Imaan na kwance saman kujera harta fara bacci ya dagata ya goge mata hawayen idanta sannan ya sa6a ta a kafada suka shiga ciki, Rafi'ah na zaune a parlorn har lokacin tana goge hawayen idanta, ya wuce da Imaan daki ya kwantar da ita akan gadon sannan ya zauna bakin gado har yanzu mamakin Umma yake ba kadan ba, yasan bata kaunarsa amma baiyi tinanin zasu wargaza masa rayuwa irin haka ba, ajiyar zuciya ya sauke ya share hawayen daya gangaro a idansa. Kusan minti 10 Rafi'ah na zaune a parlorn, ta mike jikinta duk a sanyaye ta fito a parlorn ta bude kofar main parlor tasa shoes dinta ta fita a gidan, har ta isa bakin titi hawaye yaki tsaya mata, ta tare Napeep ta fada masa inda zai kaita, tana shiga kuma ta fashe da kuka sosai. Within 14 minutes suka iso gida, Mustapha dake zaune a kofar gida yayi saurin mikewa ganinta ya ce "Hajiya nata cikiyarki Rafi'ah" a hankali ta ce "Ka bashi kudinsa" daga haka ta shige ciki, tana bude kofar parlor suka hada ido da Ummi, tayi saurin sunkuyar da kanta Ummi ta ce "Daga ina kike, kinsa inata tambayar makwabta bakya nan, Mummy ma ta tafi caan gidanta bakya nan phone dinki kuma is off" a hankali ta ce "Naje gidansu Ameera ne, phone din kuma na motar Yaya" Ummi ta dinga kallanta kafin ta ce "Ohk, wuce ki rifemin kofa" tura kofar tayi ta wuce upstairs tana share idanta, tana shiga dakinta kuwa ta zube a tsakiyar gadon ta fashe da kuka.
Ajiyar ziciya Mummy ta sauke bayan tayi hanging call din, ta kalli Jawad dake zaune gefenta ta ce "Ta koma gida yanzu, wai gidan su kawarta taje" Mami dake zaune gefe itama ta ce "To masha Allah" Mummy ta kara kallan Jawad dake zaune ta ce "Gaskiya mutanen nan sun cucemu wallahi, sun wargaza mana farincikinmu lokaci daya, ni yanzu wallahi kunyar hada ido da Yusuf nake irin abinda na masa ranar, kuma kaga yau ma har zuwa yayi ya gaishe mu, nidai dama zuciyata ne kawai a kusa na zazzageshi wallahi da nasan haka ne babu ruwana, dama ai baiyi kama da macuta ba, ga kunya da ladabi, Allah yasa dai ya yafemin" Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Irin cases din nan Mummy basu da iyaka, suna faruwa sosai, wani sai sihirin ya karye zakiga ya dawo, wani ma har abada ya tafi kenan shari'a kuma sai anje gaban Allah, to akwai matar da da kanta tayiwa diyarta asiri saboda wasu bukatu nata na duniya, so irin abubuwan na faruwa" Mami dai na zaune tayi shiru, ita kanta lamarin mamaki yake bata, Mummy tayi tagumi ta ce "Allah ya kara karemu, shiyasa ba'aso mutum ya shagala baya addu'a, at least ko abin ya sameka zaizo da sauki" Mami ta ce "Hakane kam Allah yasa mu dace" Jawad ya ce "Ameen" mikewa yayi ya nufi dakinsa ya ce "Sadeeq bai dawo ba?" Mami ta ce "Ya dawo, Kawu ne ya kirashi" ya ce "Ohk" daga haka ya shige ciki.
Mikewa Yusuf yayi yana kallan agogon dake manne jikin bango sannan ya kalli Khairiyya dake cin fried rice cikin take away ya ce "Do fast dear" zama yayi akan kujera ya jirata ta gama sannan ya wanke mata baki suka fita a parlorn ya rife bayan sun fita gate ma ya datse da gwado, daukanta yayi suka karasa bakin titi suka hau Napeep zuwa gidan Ammi, After 10 minutes suka iso gidan, ya biya mai Napeep din sannan suka shiga ciki, Sameer ne kadai zaune a balcony yana waya, ya dan kauda wayar a kunnensa ya ce "Ka dawo" Yusuf ya ce "Ehh" daga haka suka shiga cikin gidan, Ammi ta dago kanta jin an bude kofar, Yusuf ya danyi kasa da kansa ya zauna ya ce "Sannu da gida Ammi" ta ce "Yauwa, ina kukaje haka?" Ya ce "Gidana" ta ce "Ohk, yaushe zaka maida musu Imaan ne?" Kallan Imaan yayi dake kwance ajikinsa ya ce "Idan an gama komai" ta ce "To dazu dai nacewa Umminta suyi hakuri zata dawo" kai kawai ya gyada mata, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Sannan abinda nakeso da kai shine karka saka komai a ranka, insha Allah duk wanda yake da hannu a lalacewar rayuwarka sai sun girbi abinda suka shuka, kaci gaba da addu'a insha Allah soon komai zai zama tarihi" a hankali ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya ajiye Imaan kusa da Ammi ya ce "Inasan hutawa ne" Ammi ta ce "Kana shan magani kuwa?" Ya ce "Ehh" Ammi ta ce "To Allah ya kara lafiya" daga haka ta shafa kan Imaan ta ce "Kinsha tea ne" ta daga mata kai ta ce "Since morning".
Da daddare Jawad yayi parking kofar gidan Ummi, ya fito a motar ya nufi inda suka saba zama ya zauna akan daya daga cikin kujerun wajen, bayan sun gama gaisawa da Mustapha ya ce "Dan yi mata magana" Mustapha ya ce "To" sannan ya juya, bayan 10 minutes ya hangota ta tana tahowa da hijabinta har kasa, ya maida phone dinsa cikin aljihu yana kallanta harta karaso ta zauna a gefensa, ya ce "Ya kike?" A hankali ta ce "Alhamdulilah" ya ce "Dazu kuma sai kika tafi" ta danyi shiru tana wasa da fingers dinta ta ce "Ehh naje gidansu Ameera ne" ya ce "To meyasa baki bari kun dawo dasu Ummi ba" ta dan turo baki tana kallansa ta ce "Na gaji da zama ne kuma naga sunata magana" Jawad ya girgiza kai yana kallanta ya ce "This is not strictly true, kin daibi Yusuf ne ko?" Ta dago tana kallansa ta ce "Who told u ni ban bisa ba" ya danyi murmushi ya ce "Nayi karya kenan" ta ce "Ni bance maka ba" ya ce "To meyasa zaki bishi, bayan kinsan zai baki diyarki" ta dan hararshi bata ce komai ba, ya mika mata wayarta da side bag dinta sannan ya mike ya ce "Zan koma" ta ce "Bakaci abinci ba" ya ce "Na koshi, good night" daga haka ya bar wajen.

*I'm much better today thanks for the care 🥰*

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
Chapter 33 · 0% Book details