← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 46

Sashe 40

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*2 weeks ltr*
Yau ya kasance friday ranar daurin auren Rafi'ah da Jawad, kowa ka gani yana cikin farinciki, gida ya cika sosai fiye da auranta na farko, Tana zaune a daki ita da Ameera Anty Salma ta shigo, ta zauna bakin gado tana kallan Rafi'ah dake zaune tayi shiru, Anty Salma ta bata side hug ta ce "Kiyita addu'a Fatima, ba wanda ya isa ya miki abinda Allah bai kaddara zai sameki ba" rungume Anty Salma tayi cikin kuka ta ce "Anty wallahi tsoro nakeji, gani nake kamar abinda ya faru 4years back zai sake faruwa" Anty Salma ta shiga rarrashinta ta ce "Ba haka bane daughter, insha Allah gidan zamanki ne na har abada" ta daga mata kai a hankali ta ce "I hope so Anty" Anty Salma ta shiga share mata idanta ta ce "Yanzu muka dawo daga gidanki mun karasa gyara komai, the house was so masha Allah, ki godewa Allah" dan murmushi tayi ta ce "Nagode masa Anty" tashi Anty Salma tayi ta ciro mata wani kaya ta ce "Yanzu mai make up din zata karaso, sai ki canza kaya kafin 'yan daurin aure su dawo" sauke kanta tayi kasa ta amsa da toh. Karfe 1 bayan an idar da sallan juma'a dumbum mutane suka shaida daurin auren FATIMA MUHAMMAD da AHMAD MUHAMMAD AHMAD, tinda Rafi"ah taji 'yan daurin aure sun dawo hankalinta ya kara tashi, batasan lokacin data fashe da kuka ba ta kankame Ameera cikin rawar murya ta ce "Ameera ina tsoro wallahi" Ameera ta ce "Bakiji abinda Anty tace ba kiyita addu'a babu abinda zai faru insha Allah" kuka sosai take tana addu'a cikin ranta, dan gaba daya ta girgiza da abinda ya faru da ita a baya. Da yamma liss aka shirya Amarya shiri na alfarma akai ta hotuna duk da fuskarta babu walwala sosai amma tayi mungun kyau, Khairiyya na gidan itama duk inda tayi Imaan na binta a baya, Mummy dai wannan karan tana bangaren ango, dan tinda aka fara biki bata leko gidan ba, suna caan suna nasu hidiman suma, karfe 7 aka kara shiryata cikin wani tsadadden lace da yayi mungun mata kyau, sai kamshi take ta ko ina, duk da gyaran jikin na sati biyu kawai akai amma sai sheki take, sosai da sosai Abba da Ummi suka mata fada, tana kuka haka aka dagata zuwa mota, shima Abdul duk yadda yaso kar yayi kuka saida hawaye ya xubo masa, hannunta ya kamo ya ce "Allah ya sanya alkhairi Anty" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta shiga motar, motoci masu yawa ne suka rakata gidan Abi, ana parking a kofar gidan zuciyarta ya hau bugawa, aka fito da ita zuwa cikin gidan, fada sosai da naseeha Mami da Mummy suka mata, daga haka ta daga veil din da aka rife mata fuskarta dashi aka musu hotuna, Ikraam nata kallanta tana murmushi, ita dai taki yarda ta hada ido da kowa, bayan an gama komai daga nan aka wuce da ita gidanta, har dakinta Mummy ta kaita ba irin fadan data manta bata mata ba, tun tana daurewa harta fashe da kuka, bayan 'yan kawo amarya sun watse ya rage saura Ameera da Mummy sai Ikram da Anty Salma su suka kara gyara gidan yayi tass, bayan sun gama Mummy tace su tafi, ita tayi driving dinsu suka bar gidan. Rafi'ah na zaune taci kuka harta godewa Allah taji Karar shigowar message, jawo wayar tayi ta duba text message din, message ne na fatan zaman lafiya da kuma addu'o'i a rayuwar auranta a karshe ya mata fatan alkhairi, murmushi tayi ganin sunan Yusuf a karshe, tayi reply da "Thank u so much Yaya Yusuf i appreciate, and i wish u same" ajiye phone din tayi ta kifa kanta akan gwiwowinta, b jimawa taji an bude kofar dakin, ta dago kanta da sauri suka hada ido, sauke kanta tayi kasa, Jawad ya danyi murmushi ya zauna gefenta ya ce "I'm i not welcome wife?" Ta noke kafada hawaye na sakko mata, rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta ya ce "You stop crying Sweetheart" dago kanta tayi a hankali sai dai bata bari sun hada ido ba, ya ce "Kinajin yunwa ko?" Ta daga masa kai, ya ce "To muje parlor muci abinci sai muyi sallah" har lokacin jikinta rawa yake kuma ziciyarta na bugawa, dukawa yayi yana kallan jajayen idanuwanta ya ce "Ko in goya ki" ta rufe fuskarta ta ce "Ni bance maka ba ai" ya mike yana kallanta ya ce "To ki bari na daukeki" bai jira cewarta ba ya dauketa ya sata a shoulder dinsa suka fita parlor, akan kujera ya sauketa tayi saurin kifa kanta akan cushion ta ce "Ni banaso fa" ya ce "Ki bari sai anjima kice bakyaso" ta dago kanta tana kallansa ya kashe mata ido daya ya ce "Yes", plate ya dauko ya juye gasheshen kazar ya zuba fresh milk me sanyi cikin glass cup guda biyu ya ce "I want to feed u today" daga haka ya gutsuro naman ya fara bata a baki tana kar6a, ganin tana kunya yasa ya jawota jikinsa ya ce "Bari to na miki irin na babies" zame jikinta take sonyi amma ta kasa saboda rikon daya mata, haka dai ta hakura ta kwanta ajikinsa ya dinga bata, sosai taci kazar ta sha fresh milk dinta, ganin ta koshi ya daga plate din yana kallanta ya ce "To dagani na kai kitchen" a hankali ta sauka ajikinsa ta ce "Kai baka ciba" ya ce "Na koshi" daga haka ya wuce kitchen, yana dawowa ya sameta zaune inda ya barta, ya kai hannu zai dagata ta danyi kara ta ce "Nida kaina ne" ya ce "Ai banaso kisha wahala, let me just carry you" kin yarda tayi ta kara nokewa, ya ce "Then let me hold ur hand" hannunta ta mika masa ta ce "Sai dai na kama naka" ya ce "To gashi" ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka wuce daki. Brush sukai sannan sukai alwala suka fito, ya jasu sukai raka'ah biyu sannan ya dinga musu addu'ar zaman kafiya har karshen rayuwarsu, tashi yayi ya ce "Bari naje kasa na kulle kofa" daga haka ya fita a dakin, mikewa tayi ta cire hijabin jikinta ta bude press dinta, night gown kala kala ta gani, ta dauko wata doguwa sannan ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta dauko rigar zata sa kenan Jawad ya bude dakin, tayi saurin durkusawa ta ce "Wayyo Yaya ka fita na shirya mana" ya danyi murmushi ya karaso cikin dakin ya ce "Let me help u" daga haka ya dagota daga tsugunen da take, hannunsa yasa ya kashe switch din dakin, ta ce "Yaya kace tayani za..." Shiru tayi jin bakinsa akan nata, tayi saurin rintse idanuwanta zuciyarta na bugawa.

*Firstly, my apology goes straight to TEAM YUSUF, u people shoul understand me here pls, a rayuwa ba komaine kakeso kuma kake samu ba, wani abin kana sanshi amma baka san ba shine alkhairi a tattare da kai ba, shiyasa akeso a kullum mutum idan yayi addu'a yayi fatan wannan abin shine alkhairi a rayuwarsa idan ba alkhairi bane Allah ya canza masa da mafi alkhairi, wannan shine fatanmu a koda yaushe Allah kuma yasa mu dace 🤲🏻 so inaso ku gane Allah ya kaddara zaman Rafi'ah da Yusuf ya kare ta dalilin wadannan mutunen, Allah kuma ya kaddara za'a haifi Imaan, furthermore littafina na gina shine akan Jawad da kuma Rafi'ah 🥰, thank u for reading 🤗*

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_24_
Chapter 40 · 0% Book details