← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 46

Sashe 35

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

_7 hours ltr_
Dawowansu kenan a asibiti bayan an sallamosu, Ammi na hada masa tea yana kwance akan 3 seater duk idanuwansa sun juya launi zuwa jaa sosai, ya limshe idanuwansa yana kallan Ammi ya ce "I want to bath first" Ammi ta ce "Ka sha tea din mana sai kasha magani, kuma alluran ma ai bai gama bin jikinka ba, da dai ka bari zuwa karfe 9pm sai kayi wankan" kai kawai ya gyada mata ya tashi ya zauna, ta mika masa tea din ya kar6a ya rike a hannu, Ammi ta zauna gefensa ta ce "Ka sha mana" a dole ya kai tea din bakinsa dan bashida appetite, da kyar ya sha kadan ya ajiye mug din kan center table ya koma ya kwanta, Ammi ta kamo hannunsa tana masa nasiha hade da kwantar masa da hankali.
Washegari karfe 10am Rafi'ah ta fito a dakin Ummi bayan tayi wanka, ita kam jikinta da sauki sosai, sai ciwan ai kadan kadan, jikinta duk a sanyaye ta karasa parlorn da Abba ke zaune Ummi na gefensa, ta dayan side din kuma Mummy ce zaune taci kuka harta godewa Allah, a hankali Rafi'ah ta kalli Abba dake zaune yayi shiru, idanuwansa sun kada sosai, bata ta6a ganin Abbanta cikin tashin hankaki iri haka ba, murya caan kasa ta ce "Ina kwana Abba" ya dan kalleta cike da damuwa ya ce "How are u daughter?" Ta ce "Fine" Rafi'ah ta gaishe dasu Ummi ta zauna a wajen, kukan Imaan da sukaji a daki yasa Ummi ta mike ta shiga dakin, wanka ta mata tayi brush sannan ta shiryata suka fito, Ummi ta kalli Rafi'ah dake gefen Abba ta ce "Kije kiyi breakfast mana" mikewa tayi a hankali Ummi ta mika mata Imaan suka wuce. karfe 11 Abba ya ce "Suje su duba jikin Yusuf dan an maidashi asibiti ana kara masa jini" duk jikinsu yayi sanyi musamman Rafi'ah da idan ta tuna rashin kunyar data masa jiya sai kuka yazo mata, key din mota Abba ya dauka duk suka bi bayansa dama ko wacce da hijabinta, har suka isa clinic din baifi sau 3 sukai magana ba shima Imaan ne duk tayi causing,
Bayan Abba yayi parking suka fito suka shiga ciki, Daddy ne da wasu 'yan uwan mahaifin Yusuf da suka iso da safe su 3, bayan sun gaisa Daddy yace su shiga ciki, a kwance suka sameshi yana bacci ana kara masa jini, gaba daya ya gama ramewa sai haske daya kara sosai, Ummi dai juyawa tayi ta fita, Mummy ta masa addu'ah itama ta juya, Imaan nata kallansa a tsorace sai dai ba tai magana ba, bayan few minutes Abba ya fita dakin ya rage daga shi sai Rafi'ah sai kuma Imaan, Hawayen idanta ta share ganin ko numfashi da kyau baya yi, taja kujera ta zauna a gefen gadon, bude ido yayi jin karan kujeran, suna hada ido ya maida kansa gefe hawaye na gangaro masa, daurewa tayi ta ce "How are u" da kyar ya daga mata kai, Imaan ta kalli Rafi'a dake kuka a hankali ta ce "Momma is Papa sick?" Juyawa Yusuf yayi ya kamo hannunta ya ce "But i recovered dear, i missed u yesterday" dan murmushi tayi ta ce "I missed u too" mikewa Rafi'ah tayi ta fita a dakin har lokacin kuka yaki tsaya mata. Har dare Yusuf yana asibitin, Ummi ta koma gida tayi dinner ta kawo musu, Mummy dai na tare da Ammi, sai Sameer da Rafi'ah, su Abba kam tintini sun koma da Ummi, tindaya farka da safe ya koma bacci bai sake tashi ba, jininma daya kare suka kara saka masa wani, karfe 9 Ammi da Mummy suka tafi salla, Sameer ma tinda ya fita sallan Isha bai dawo ba, Rafi'ah na zaune ta buga uban tagumi ta kuma yi nisa a duniyar tinanin data tafi, jin tarin da yayi yasa ta mike ta karasa kusa dashi, ta ce "Sannu" ya ce "Uhm" zama tayi a akan kujerar dake gefen gadon, silently ta ce "How are u feeling now?" Ya ce "Alhamdulilah" ta share dan guntun hawayenta ta ce "I'm sorry with what happened yesterday, i shouted at u which is not fair dan Allah ka yafemin" Yusuf ya mike da kyar ya zauna ya jingina da bango yana kallanta ya ce "Ba komai ya wuce, and u forgive me too, i cause too much pain in ur life" a hankali ta girgiza kai ta ce "They did but not u" shiru yayi yana kallan hannunsa daya kumbura saboda neman vains, a hankali ya ce "Imaan fa?" ta ce "Sun tafi gida da Ummina" ya ce "Ohk" juyowa yayi suka hada ido tayi saurin sauke nata idon, ya ce "Bani ruwa" ta mike a sanyaye ta nufi Fridge din dakin ta dauko bottle water sannan ta wanke cup din ta xuba masa, zama tayi a bakin gadon har ta kai cup din bakinsa sai kuma ta mika masa a dayan hannun, ya kar6a ya sha kadan sannan ya mika mata ta ajiye a gefe, komawa tayi gefe ta zauna kanta a kasa, Yusuf ya dan kalleta ya ce "Did u forgive me?" Da sauri ta kalleshi sai kuma ta daga masa kai tana share hawayen idanta ta ce "Yes i did, Allah ya yafe mana gaba daya" ya ce "Ameen" bude kofar dakin akai wani Dr ya shigo, suka gaisa da Yusuf ya masa ya jiki, ganin hannunsa ya kumbura ya ce "Bari a canza maka hannun ya huta" daga haka ya kashe ya maida masa dayan hannun sannan ya kunna yana masa sannu, daga haka ya fita a dakin, sun kai minti 5 a zaune kowa da abinda yake sakawa cikin ransa, ya dan kalleta ya ce "Pls help me with some water" ta mike ta dauko ruwan dazu ta mika masa, yana kar6a hannunsa yayi kasa cup din zai fadi tayi saurin rikewa, sai lokacin ta tuna hannunsa da ciwo, kamar baza tai ba kuma ta kai cup din bakinsa tana bashi ruwan, hakan yasa ta kauda kanta gefe bata bari sun hada ido ba, bude kofar dakin akai Jawad ya shigo rike da babban leda a hannunsa me dauke da fruits kala kala, yayi saurin dauke kansa ganinsu a haka, itama da sauri ta zare cup din a bakinsa ta ajiye a gefe kanta a kasa, Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce...

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_20_
Chapter 35 · 0% Book details