← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 46

Sashe 25

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude idanuwansa yayi a hankali ya fara bin dakin da kallo, Ammi dake zaune gefensa tayi saurin matsowa ta ce "How are u?" Silently ya ce "I'm fine Ammi, where is my daughter?" Ammi ta ce "Don't stress yourself again pls, everyone is fine, Rafi'an ma a jiyan aka sallameta tana gida" Yusuf ya dan kalleta ya ce "U said?" Ta ce "Rafi'ah" shiru yayi yana tina incident din jiya daya faru, Ammi ta ce "Pray first sai mu wuce gida" mikewa yayi a hankali yana kallan agogon dakin dake nuna karfe 7 saura, da taimakon Ammi ya shiga toilet yayi alwala sannan ya fito yayi sallah, idan ka ganshi zakace bashida damuwa saboda ya saki ransa yau ba kadan ba, sai dai kuma in kaga ramar da yayi. Kafin ya idar da sallah Daddy da Abi da kuma Abba da saukarsa a garin kenan suka shigo dakin, bayan sun gaisa da Ammi, Yusuf ya juyo a hankali yana kallansu, sai kuma ya sauke idansa kasa ya ce "Ina kwananku?" A tare duk suka amsa, Abba ya ce "Ya karfin jiki?" Ya ce "Alhamdulilah" Daddy ya kalli Ammi ya ce "Tinda an sallameku Sameer zaizo ya maidaku gida, sannan karfe 10 akwai meeting a guest house dina da akai organizing just because of this case, and i hope kowa zaiyi attending dan samun kwanciyar hankali" Ammi ta ce "Allah ya kaimu" Abi ya ce "Allah ya kara maka lafiya" daga haka suka fita a dakin, sauke kansa kasa yayi yana kallan Ammi ya ce "Good morning" Ammi ta ce "Morning too, ya karfin jiki?" Ya danyi murmushin karfin hali ya ce "Da sauki" ta ce "Allah ya kara sauki" shiru yayi yana san ya tambayi Imaan amma sai yaji nauyin hakan, jinginar da kansa yayi jikin gadon yana addu'a kasa kasa, sai daya ji an bude kofar dakin sannan ya dago yana kallan direction din kofar, wani dan uwan mahaifinsa ne tare da Sameer suka shigo dakin, Yusuf ya danyi murmushi yana kallan Kawun nasa ya ce "Ina kwana Kawu Umar" Kawu ya ce "Alhamdulilah, ya karfin jiki" ya ce "Da sauki Kawu" daga haka suka gaisa da Ammi, Sameer ya durkusa yana kallansa ya ce "How are u feeling now" Yusuf ya ce "Better" Sameer ya ce "Masha Allah, dazu Faruk ya kira zan hada ku ku gaisa kuma kana bacci" Yusuf ya ce "Ohk anjima sai muyi waya" mikewa Ammi tayi ta fara tattara duk kayansu ta bawa Sameer ya kai mota, sannan suka fito zuwa gida bayan sun kara siyan wani magani guda daya. Rafi'ah ce kwance akan gadon dakin Ummi tana faman goge hawaye, tinda aka sallameta a asibiti jiya da daddare bata rintsa ba har yanzu, Mummy dake zaune gefenta ta ce "Allah dai ya isa wallahi, yaushe raban da ciwanki ya tashi haka sai bayan dawowar wannan yaran" tana rife bakinta Abba ya shigo Ummi na biye dashi, ya zauna bakin gado yana kallan Rafi'ah ya ce "So u didn't stop crying, u forgot all i told u ko?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "No Abba, just that i can't control my tears" Abba ya ce "Try and control it then" daga haka ya kalli Ummi ya ce "Zamu je meeting din da sukayi organizing karfe 10" Mummy ta ce "Meeting din me kuma? bayan gamu da marar lafiya a gida" Abba ya ce "Wannan ba dalili bane Halima, u have to attend" Mummy ta hade rai ta ce "Aini banga wani meeting da za'ai ba, bayan ya saketa ai magana ta kare meye kuma za'a ce sai mun kara haduwa duk tamu" Abba ya dafa Imaan dake kwance tana bacci ya ce "For the sake of her, ya kamata ace an saurari bayani daga bakinsa, tinda koma menene shine mahaifinta, bayan an gama meeting din komai sai ya biyo baya, but we can seperata him with his daughter" Mummy dai bata ce komai ba a wannan karan, Ummi ta ce "Allah ya kaimu, sai dai bamusan wajen ba" Abba ya ce "Munyi waya da Jawad, zaizo ya kaiku sun bada address" Ummi ta ce "Allah ya kaimu". Khairiyya na zaune a parlor tayi tagumi su Ammi suka shigo, tayi saurin dauke kanta daga kallan Yusuf hawaye ya fara zuba a idanta, ba abinda take tinawa sai ranar daya saki Rafi'ah, ta mike da sauri ta wuce dakinta tana kuka sosai, dakin Sameer Ammi ta rakashi ta hada masa ruwan wanka ta ce "Bari na hada maka breakfast kafin ka gama" ya ce "To nagode Ammi" daga haka ta fita, dakin Khairiyya ta shiga ta sameta kwance tana kuka kasa kasa, Ammi ta zauna bakin gado ta ce "Kukan ne bazaki daina ba har yanzu?" Tayi shiru kawai tana goge hawayen idanta, Ammi ta ce "Kije ki gaishe da Yayanku sannan ki wuce kitchen ki fara feremin dankali, i want to bath first, banajin dadin jikina" mikewa tayi a hankali tana hade rai ta fita a dakin, direct kitchen ta nufa ta farayin abinda akace, duk bayan miti daya sai ta tsaya ta share hawayen idanta kafin taci gaba. Kafin karfe goma sun gama shiryawa, Ummi ta gama shirya Imaan ta ce "Go and call ur Momma for me" Imaan ta tafi da gudu zuwa dakin Rafi'ah, a bakin gado ta sameta zaune ta gama shiryawa tasa hijabi, Imaan ta rungumeta ta ce "Ummi is calling u" Rafi'ah ta rungumeta itama ta ce "I'm coming" daga haka ta mike ta kama hannun Imaan suka fita a dakin, da sallama suka shiga dakin Ummi, bayan sun zauna Ummi ta ce "Ki kwantar da hankalinki kinji ko, babu abinda zai faru insha Allah, saki ne ya riga daya sake ki, babu sauran alakarki da shi" Rafi'ah ta ce "To" Ummi ta ce "Ina Anty Halima?" Ta ce "Ta sauka tin dazu, suna tare da Yaya ne" Ummi ta ce "Ohk" juyawa tayi ta fita a dakin Imaan tabi bayanta, tinda suke sakkowa a stairs Jawad yake kallanta, ita kuma taki bari su hada ido, ta dan tsaya bayan kujera ta ce "Good morning" daga haka ta nufi hanyar fita ya bita da kallo, Mummy ta ce "Ai wallahi yayi attempting kar6an yarinyar nan kotu zamu kaishi" Jawad ya mike yana gyaran hulan kansa ya ce "Is better" daga haka ya fice a parlorn, parking lot ya duba baiga Rafi'ah ba, ya zagaya backyard ya ganta a zaune ta kifa kanta da gwiwowinta, ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Dear" kin dago kanta tayi, ya ce "Tashi ki gani" taki dagowa, hannunsa yasa ya daga kanta dake kan cinyarta ya ce "Are u still crying?" Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, ya shafa bayanta cikin rarrashi ya ce "Calm down pls, ur heart beats too fast, taba kiji" daga haka ya dagata a jikinshi ya dora hannunta saitin heart dinta ya ce "Kinji" ta daga masa kai, ya ce "Then keep quite, insha Allah alkhairi kawai zakiji, ki daina jin tsoro" ta turo baki ta ce "Ni banasan ganinsa kuma" ya ce "To bazan bari ya kalle kiba, aike ce duk kika jawo mana, kikace ke karatu zakiyi ba aure ba, kinga da munyi auran mu a acikin babban rigana zan saka ki ba yadda zai kallan min ke" ta danyi murmushi tana kallan shigar da yayi ta ce "Ya maka kyau sosai" ya ce "Ko? Kema kinyi kyau, just that idan nan ya kumbura kinyi kuka sosai" ta ce "Kuma inajin bacci ma" ya ce "Don't worry idan mun dawo sai kiyi baccin" ta ce "To" mikewa yayi jin muryar Mummy a parking lot ya ce "Karfa kibi bayana, ki koma ta kitchen" daga haka ya bar wajen, ta danyi murmushi ta tashi ta koma ta kofar baya ta shiga cikin gidan sannan ta kara fitowa ta parlor, duk suna tsaye a parking lot, yayi reverse sannan suka shiga motar yaja suka wuce. Suna isa katoton guess house din Daddy Jawad yayi horn aka bude masa gate, babban gidane sosai amma ba kowa a ciki, Jawad yayi parking yana kallan motoci hudu dake pake a wajen, da alama dai su kadai ake jira kenan, bayan duk sun fito Imaan ta daga masa hannu alaman ya dauketa, ya dagata sama sannan ya sauketa kan shoulders dinsa suka shiga ciki, duk ilahirin mutanen na zaune a wakeken parlorn, suka shigo da sallama sannan suka zazzauna, caan gefe Rafi'ah ta samu ta zauna kanta a kasa bata bari koda wasa ta hada ido da mutanen parlorn ba, Yusuf ya sauke idansa daga kallan Imaan ya wani sauke ajiyar zuciya, godiya ga Allah yake cikin ransa daya bashi this cute girl, kowa ya ganta yasan shine mahaifinta, Daddy yayi sallama sannan ya bawa Yusuf damar magana akan ya fadi dalilinsa na sakin matarsa sannan meyasa ya tafi ya barta almost 4 years ba'a san inda yake ba, shiru duk mutanen parlorn sukayi suna kallan Yusuf da kansa ke kasa, Rafi'ah ce kawai bata yarda ta kara kallansa ba, Cikin cool voice dinsa yayi musu bayanin komai, tin daga ranar daya farajin tsanar Rafi'ah har ta kai ga ya saketa sannan ya kara da cewa tinda ya tafi Egypt bai kara tina taba sai ranar, duk mutanen parlorn jikinsu yayi sanyi sosai, Kawu Umar ya ce "Ninasan wannan aikin Fatima ne, wallahi zata iya yin komai dan dai ta rushe farincikin yaran nan, yanzu ina take ita da 'yartata" Yusuf ya ce "I don't know Kawu, tinda aka sallameni a asibiti ban sake ganinsu ba" Kawu ya ce "Baka da number dinsu ne?" Ya ce "Ina dashi, sai dai banbi ta kan wayar ba, ga dai ta nan a pocket dina" Kawu ya ce "Kira mana ita" Yusuf ya ciro wayar ya danna yana kallan screen din, 25 missed calls ya gani, ya duba yaga kiran Umma ne, cire wayar yayi a silent sannan yayi dialing phone dinta, Kawu Umaru dake kallansa ya ce "Kar kace mata kana gida" shi dai shiru yayi yana kallan phone din dake ringing, bayan Umma ta daga yasa a hands free, ta ce "Yusuf" ya ce "Na'am" ta ce "Kana ina?" Yayi shiru sannan ya ce "Ina hanyar zuwa kano" Umma ta fashe da kuka ta ce "Yusuf gamu
Chapter 25 · 0% Book details