Sashe 10
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
akan baka zo ba, ita kishiyarki tinda nazo banga ta shigo ba, ga dai baki ga hanci amma tsit kake ji" Ummi dai bata ce komai ba, ta gyarawa Babyn kwanciya sannan ta rufa mata net, Gwaggo ta ce "Shi Muhammad din a wajenta yake ne?" Ta ce "Ehh, tinda akai haihuwan ya koma caan, kinga baki suna ta zuwa, bai katura muba muma bamu takura shi ba" Gwaggo ta ce "To dama ana suna kice ya dawo dakinki, kuma saiya rama miki kwanakin da yayi acaan, aike ba dutse bace" Mikewa Ummi tayi ta ce "Bari na kaiwa Rafi'ah tea Gwaggo" Gwaggo ta ta6e baki ta ce "Zandamemiyar budurwa sai an kai mata shayi saboda ta haihu, naga ba haihuwa tayi da kanta ba, ciro yarinyar akayi, ke dai kawai kice kina mata bauta" tin tini Ummi tayi wucewarta ta barta zaune kusa da Babyn tana ta zance. Bayan su Mami sun bar gidan su Rafi'ah gidan Kawu suka wuce kamar yadda ta bada umarni, a bakin gate tace yayi parking saboda ba dadewa zasuyi ba, daga haka ta fito ta shiga gidan, Ihsan ce kadai a parlor tana cin abinci, ta danyi murmushi ganinsu ta ce "Ina wuni Mami, Ikram bata zo ba?" Mami ta ce "Tana caan tana baccin nata na jaraba, ina Hajiya?" Ihsan ta ce "Tana daki" Mami ta wuce daki ta bar Sadeeq suna magana da Ihsan, a bakin gado ta zauna tana kallan Hajiya Fatima ta ce "Yau dai nace bari nayi kokari na karaso, ku bada zua ba muma haka" Hajiya Fatima ta ce "Aikin kyauta, ya yaran da maigidan?" ta ce "Lafiya kalau, ina Kawu?" ta ce "Kawu tin safe bai dawo ba, sai kuma dare" tana rife bakinta Sadeeq ya shigo ya gaisheta sannan ya koma parlor, ta kalli Mami dake zaune ta ce "Ni kuwa ina Jawad ne?" Mami ta ce "Yana nan kinsan yanzu bada mu yake ba, ya koma gidansa zuwa yake yana gaishemu" Hajiya Fatima ta ce "To lallaikam, ko dai ya fara neman aure ne?" Mami ta ce "Dazun nan ya gama gayamin, wai yarinyar ta haihu shiyasa zai jira saita yaye dan" Hajiya Fatima ta ajiye kayan hannunta da take ninkewa tana kallan Mami ta ce "Rafi'ah zai aura kenan?" Wani katon ashar Mami ta saki ta ce "Tabbdi ai sai dai idan bana numfashi, sunan ita waccen Zarah fa, kuma yace ma unguwar rimi take, sannan kuma ita mijinta ne ya mutu" Hajiya Fatima tayi murmushi tana kallan Mami ta ce "Kije dai ki kara bincike, tin ba yau ba ninasan Jawad san yarinyar nan yake, kuma da kike kirarin sunanta Zarah ba sunanta Fatima ba? Koba ita ta haihu ba, kawai dai rainin hankali yake so ya miki, amma so kam yarinyar nan yake so" nan da nan zufa ya fara karyowa Mami, ta rasa abinda zata ce tana tinani, caan ta mike ta fara neman layinsa a waya, bugu biyu ya dauka ya ce "Mami" ta ce "Duk abinda kake koma menene ka bari ka dawo gida ka sameni" ya ce "Mami i have some important things..." A fusace ta ce "Cewa nayi duk abinda kake ka bari kazo gida, umarni na baka ba shawara na nema ba" daga haka tayi hanging wayar ta dauki hand bag dinta kamar zata tashi sama ta fita a dakin, Hajiya Fatima ta bita da kallo tana murmushi. Kallan Aliyu Jawad yayi ya ce "Kaga mun fara maganar guy din can kuma Mami ta kirani urgently, so bansan me yake faruwa ba, i have to go now" Aliyu ya ce "Ba komai, gobe ai Saturday koda safe zamu iya magana, i will call u idan naji wani bayani" Jawad ya ce "Alright thank u" daga haka duk suka mike suka fita a parlorn.