← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 46

Sashe 38

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_22_

'Bata fuska Khairiyya tayi ta koma dakinta ranta a 6ace, Yusuf ya danyi murmushi yana shafa kansa, ganin Daddy ya shiga daki ya nufi dakinta yana dariya, a hankali ya bude kofar dakin ya hangota caan karshen gado tana kuka, ya maida kofar ya rufe ya karasa inda take yana murmushi ya ce "Ya akai Khairiyyan Yaya?" Fashewa tayi da kukan bakin ciki ta ce "Ni karka sakemin magana Yaya, mena maka daza ka hanani fita wajensa" side hug ya bata cikin rarrashi ya ce "It's not safe dear, naga baki sanshi ba, kullum waya kuke bakisan ya halinsa yake ba, watakila ma guduwa yazo yayi dake" ta dan zare ido tana kallansa ta ce "Guduwa kuma Yaya?" Ya ce "Uhmm, an gaya maki kidnappers suna da kama ne" jikinta ne yayi sanyi sosai, ta share guntun hawayenta ta ce "Kuma hakane, Allah ya kara karewa" ya ce "Ameen, kimayi deleting contact dinsa" ta daga masa kai da sauri, ya ce "kisa a black list ma" ta ce "Ohk" shiru tayi tana kallan Yusuf dake kallant ta ce "But Yaya what if he's innocent?" Ya ce "Just do what i said now" ta dan ta6e baki tasa number a black list sannan tayi deleting baki daya, duk yana kallanta harta gama, ta dago kanta tana kallansa ta ce "Yaya meyasa bazaka dawo da Anty Fatima ba?" Ya danyi murmushi yana girgiza kai ya ce "Kefa kika cemin ta kusan aure?" Ta ce "Yes, but nasan Ya Jawad zai hakura ya baka indai kaso hakan" kanta ya dora akan shoulder dinsa ya ce "Sankai kikeso nayi, ai Allah yace musowa 'yan uwanmu abinda muke sowa kanmu, kuma suna san junansu is hardly nace ta dawo ta yarda, and u know what?" Ta girgiza masa kai ya ce "Koda tace zata dawo bazan iya ba saboda Ahmad, he sacrificed alot Khairiyya wallahi da inada wani abin dazan saka mishi bayan Rafi'ah da zanyi, but haryanzu ina tinanin zan bashi Imaan idan har yanaso" Khairiyya ta danyi murmushi ta dago tana kallansa, sai kuma ta dan 6ata fuska ta ce "Yanzu shikkenan Yaya kun rabu?" Ya ce "No akwai zumunci Khairiyya, ga kuma Imaan sannan nima na cireta a raina by now, Allah ya hada auranmu tun farko saboda akwai raban Imaan tazo duniya, sannan auranmu shine silar kaddararmu" Khairiyya ta goge guntun hawayenta tana kallansa ta ce "Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya hade goshinsu yana kallan idanta ya ce "Ameen" jin an bude kofar yasa yayi saurin janye fuskarsa akan nata, Ammi ta kallesu sau daya ta kauda kai ta ce "Ka sameni a dakina" ya ce "Ohk to" mikewa yayi yana kallan Khairiyya ya ce "Till i come back" ta daga masa kai sannan ya fita a dakin. Da sallama Yusuf ya shiga dakin Ammi, ya nemi gefe ya zauna ya ce "Gani" Ammi ta ce "Toda farko dai mungode Allah daya kwatar maka 'yancinka ya kuma kubutar daku a hannun wannan mutanen" a hankali ya ce "Allah ya kara tsarewa" ta ce "Ameen, sai kuma maganar Rafi'ah, ka dawo kuma gashi tana shirin yin aure" a hankali ya dago yana kallanta sai kuma yayi murmushi ya ce "Allah ya sanya alkhairi Ammi, koda ba aure zata yi ba idan Allah ya kaddara zamanmu ya kare dole haka zamu hakura" Ammi ta ce "Toh fatanmu Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya amsa da "Ameen"
Fitowa tayi walking slowly tana murmushi harta karasa kusa dashi, ya cire glasses din idansa ya ce "Amaryar Ahmad" ta sunkuyar da kai ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya kalau, kin shirya muje?" Ta daga masa kai ya ce "To bismillah" daga haka ya bude mata front seat ta shiga ta zauna, shima ya zagaya mazauninsa yayiwa motar key suka bar layin. Hannunta ya kamo yana kallan idanta ya ce "How is Imaan?" Ta ce "Tana nan lafiya" ya ce "Haka akeso" zame hannunta tayi a cikin nasa ta ce "Ummi tace za'a kaita wajen Babanta" ya ce "When?" Ta ce "Inaga yau" Jawad ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" shiru tayi tana kallan sajen fuskarsa daya kwanta sosai, ganin zai juyo yasa tayi saurin juyawa tana kallan window, murmushi yayi mai kyau ya ce "I caught you, me kike kalla a fuskana" ta danyi murmushi ba tare data juyo ba ta ce "Nothing" ya ce "There's" ta ce "To idan baka yarda ba shikkenan" ya ce "To zuwa zanyi na aske tinda bakyaso" tayi saurin juyowa tana kallansa ta ce "Nooo pls" ya juyo ya dan kalleta sai kuma ya maida hankalinsa ga titi, in a very low voice ta ce "Yana maka kyau sosai" ya juyo yana kallanta tayi saurin rife fuskarta da hijabi, ya ce "Wallahi wannan kunyan naki rana daya zan cire miki shi" bata dai dago ta kalleshi ba sai dariya take a hankali. Da sallama Ummi ta shigo parlorn Abba ta sameshi zaune yana rike da Imaan, kallanta kawai yake amma tinaninsa da hankalinsa na wani wajen da ban, jin bai amsa sallaman ba yasa Ummi ta kalleshi, ta sauke ajiyar zuciya ta zauna gefensa ta ce "Abbu Rafi'ah" ya juyo yana kallanta ya ce "Harkin gama ne?" Ta ce "Na dai kusa" ya ce "Ohk, Fatiman ina tafi ne? bamasan yawan fitan nan fa" Ummi ta ce "Taje gidan Anty Halima, kuma ta dade bata je bane shiyasa" Abba ya ce "Allah ya dawo da ita lafiya" ta ce "Ameen, dan Allah Abbu Rafi'ah kayi hkr da abinda ya faru karka sawa kanka wani ciwo" a hankali ya kwantar da Imaan akan kirjinsa ya ce "Ina kokarin yin hakan Zainab, amma kinsan abin da ciwo wani lokaci gani nake kamar mafarki ne" Ummi ta ce "Hakuri dai zakayi, tinda abinda ya faru ya riga ya faru, kuma dai koma menene 'yan uwanka ne, bazaka ta6a canzasu ba" Abba ya limshe ido ya ce "Hakane 'yan uwanane amma a yanzu da abin ya faru na cire hannuna akan lamarin su, ita Umma uwace a gareni sbd haka zanci gaba da kyautata mata kamar da, amma 'ya'yanta bani da sauran alaka dasu, abinda suka min suje suda Allah" duk jikin Ummi sai yayi sanyi, a hankali ta ce "Allah ya kyauta" ya ce "Ameen" daga haka ta mike ta daga Imaan dake bacci a jikinsa suka shiga daki. Jawad na parking Rafi'ah ta fito da sauri ta nufi entrance din gidan, bayan ya rife mota ya bi bayanta. A parlor duk ta samu ilahirin gidan, tayi saurin sunkuyar da kanta ganin sun hada ido da Mami, ta samu caan gefe ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" cike da fara'a Mami ta ce "Lafiya kalau Fatima, ya karatu ana ta hutu ko?" Ta ce "Ehh" dai dai nan Jawad ya shigo rike da key din motarsa ya zauna kusa da Rafi'ah that wasn't comfortable, a hankali ta ce "Ina yini Mummy" Mummy ta ce "Lafiya kalau, yasu Umminki?" Ta ce "Suna nan lafiya" Ikram dake zaune ta ce "Ina yini Anty" a hankali Rafi'ah ta dan kalleta ta amsa, Sadeeq ya ce "Antynmu ina yini" kunya taji ta rife fuskarta da hijabi, Ikram ta mike tana dariya ta shiga kitchen, ba jimawa ta jerawa Rafi'ah different kind of fruits a gabanta, a hankali ta ce "Thank u" Ikram ta ce "Never mind Anty, tin jiya Yaya yake cewa zakizo wai sai Mummy ta miki dambu" ita dai kanta a kasa tana ta murmushi, ganin Mami ta tashi yasa ta mike da sauri ta shiga part din Mummy, Jawad ya danyi murmushi yana kallan Mummy ya ce "Sai ta zauna ita kadai ko? Dan mu yanzu anan muke yini" Mummy ta ce "Atoh idan ta gaji ta fito" Ikram ta dauki tray din tabi bayanta ta ce "Ni dai bazanbar Antynah ita kadai ba" daga haka ta shige part din Mami tana dariya.
Chapter 38 · 0% Book details