← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 46

Sashe 12

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_~The next day~_
Washegari ya kama jibi suna, Rafi'ah na zaune tare da Ameera a daki suna dan hira Ummi ta shigo, Rafi'ah ta mike tana kallanta ta ce "Munyi magana da Mummy dazu" Ummi ta ce "Kizo dakina yanzu" daga haka ta juya, kallan Ameera tayi kamar zatai kuka ta ce "Wai fa akan sunan Babyn ne, nina ce susa sunan duk wanda suke so, nasan ko nace asa sunan wacce nake so ba lallai asa ba" Ameera dake kallanta ta ce "Kamar ya? Ba dai su suka ce ki fada ba?" zama Rafi'ah tayi a bakin gado tana share hawayen idanta ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso asa Ameera, but nasan they won't listen to me" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta tana kuka, Ameera ta ce "U shouldn't think that Fatima, kika san ko zasu yarda" ta girgiza kai a hankali ta ce "Doctor have no prents alive, even one Ameera, ba shi da uwa ba shi da uba, sai Ammi kadai ce take son shi, ya sha fadamin in dai ya haifi mace zai sa sunan mamanshi idan Baby boy ne sunan mamanshi, i have to fulfill his wish Ameera, nasan ya min abinda bazan manta da shi ba harna koma ga Allah, amma at this time inaso na cika masa burin daya dade yana fata, and i don't think they will accept it" Ameera ta sauke ajiyar zuciya tana kallanta cike da tausayi ta ce "Ki gwada, idan sun ki then u accept whatever they say" mikewa tayi a hankali ta share hawayen idanta sannan ta bude press dinta ta dauko hijab ta saka ta fita a dakin Ameera ta bita da kallo, jikinta duk a sanyaye ta bude dakin ta shiga hade da sallama, Ummi dake duba abu a press dinta ta ce "Kije kawai Rafi'ah zata fita, anjima sai muyi magana idan ta dawo" har zata juya Mummy ta ce "Come here" karasowa tayi kanta a kasa ta ce "Gani" Mummy ta ce "Ya idanki yayi jaa?" A hankali ta ce "Ba komai" sai lokacin Ummi ta kalleta, bata dai ce komai ba taci gaba da abinda take, Mummy ta ce "U said nothing, amma kamar kinyi kuka?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne kawai yake ciwo" Mummy ta ce "Go and make sure u take your drugs" juyawa tayi bata ce komai ba ta fita a dakin ta koma dakinta.
Jawad ne zaune a parlorn gidansa shida Aliyu, kowa da abinda yake tinanin, caaan Jawad ya danyi tsaki ya ce "Tabbas baya kasar nan, to amma wa kake ganin zai san inda yake?" Aliyu yayi shiru yana tinani, sai kuma ya ce "Idan fa akwai wanda zai san inda yake so definitely it most be me ko Mukthar, sai kuma wannan cousin din nasa Sameer" Jawad ya cire glasses din idansa ya ce "Kenan duk baku sani ba?" Aliyu ya ce "Ehh, ko ita maman Sameer din bata sani ba, dan kwana biyu da faruwan abun sun zo asibitinmu ita da mijinta ko zasu samu wani bayanai akansa amma babu" mikewa Jawad yayi yana zira hannayensa cikin pockets din wandansa ya ce "Kace baya shan komai?" Aliyu ya ce "Kyakkyawan sani nayi wa Yusuf, kaga dai shi kikita ne ko? Amma wallahi kwayar magani da kyar yake hadiya balle kuma har yayi shaye shaye, ni kaina abin mamaki ya bani, i don't know what comes over him, yana san matarsa fa wallahi" dan karamin tsaki Jawad yaja ya ce "To idan yana santa me zaisa ya saketa da ciki, almost a year harta haihu bai dawo ya ganta ba" Aliyu ya ce "Shine kuma abin dubawa, amma ina ganin koma menene ya faru da sa hannun mutanen gidansu, tinda duk tasu suka tafi, kuma suka tafi harda matar da suke so ya aura, Yusuf ba zai ta6a cutar da Fatima ba Ahmad, karkace nayi maka shishigi game da abinda kake, kai aikinka ne ni kuma ina fadan abinda nasan Yusuf zai iya ne, Yusuf ba shi da hali marar kyau Barrister sai dai kuma kasan dan Adam ta wani bangaren" a hankali Jawad ya zauna gefen shi ya ce "No, ai wannan ba shishigi bane, nima a nawa fahimtar banga alamun rashin gaskiya a tattare da shi ba, just that ni bana shiri da shi sabida wani dalili nashi" Aliyu ya ce "Yanzu menene abinyi kenan?" Jawad ya maida glasses dinsa ya ce "We should keep on praying, idan aka kasa gano abu sai ayi ta addu'a, but ina tabbatar masa duk ranar daya dawo he will be arrested kuma matar daya saka tayi masa nisa by then, dan tini ta auri wanda zai sota har abada" Aliyu ya ce "Allah ya za6a mana mafi alkhairi, ya kuma bayyana shi" a hankali ya ce "Ameen, thanks for ur time Dr. Aliyu" Aliyu ya mike yana mika masa hannu ya ce "Ur welcome Barrister, in dai naji wani abu i will let u know" Jawad ya ce "Nagode sosai" har bakin motarsa ya rakashi ya bude masa gate bayan ya fita ya rife ya dawo ciki, phone dinsa ya dauka ya kira Rafi'ah, tana fara ringing ta dauka hade da sallama, ya ce "How are u?" Ta ce "Fine" ya ce "What about my Baby" ta danyi murmushi sannan ta ce "She's fine too, sai kuma kuka takemin jiya i didn't slept well at night" ta karashe maganar tana turo baki kamar yana kallanta, ya dan shafa kansa yana limshe ido ya ce "To ki bani ita kawai" ta ce "To kazo ka kar6a idan zaka iya rikewa" ya bude idanuwansa ya ce "Sai dai idan tare duk zaku dawo gidana, kinga sai mu rike babynmu da kyau" a hankali ta danyi murmushi har yana jiyo ta sannan ta ce "Sai dai ita din dai" ya ce "A'a ni da Mummy da daughter nakeso" tayi dariya kawai bata ce komai ba, Jawad ya ce "Ya jikinki din ya warke?" Sai data kalli wajen CS dinta sannan ta ce "Saura kadan" ya ce "Allah ya sauwake" ta ce "Ameen" ya ce "I will call ltr, i'm going home, tin jiya banje na gansu ba" ta ce "Alright saika dawo" daga haka yayi hanging wayar ya dauka hula ya saka sannan ya dauki key din mota ya fito a gidan, garin is too cloudy sai iska da ake busawa me kura, sai daya rife duk windows din gidan kafin ya fitar da mota ya kulle gate din sannan ya dauki hanyar gida. Kafin ya iso gida an fara ruwa sosai da sosai, yana isa yayi horn aka bude gate sannan ya shiga yayi parking ya fito da sauri ya nufi entrance din gidan, ba abinda ya tsana irin yaji shi a jike, ba kowa a parlorn hakan yasa ya wuce dakinsa ya canza kaya sannan ya dawo part din Maminsa, Sadeeq da Ikram na zaune a parlorn suna cin abinci, duk suka masa sannu da zuwa sannan ya shige ciki, dakin ma ba kowa amma yana jiyo alamun mutum a toilet, hakan yasa ya kwanta kan gadon ya rufe kafafuwansa da blanket, after few minutes Mami ta fito a toilet, ta tsaya tana kallan kan gadon don dakin yayi duhu, a hankali ta ce "Sadeeq" ya bude idanuwansa yana kallanta ya ce "It's me" ta hade rai ta juya masa baya sannan ta nufi kofa ta fice a dakin, mikewa yayi da kyar dan sanyi yakeji sosai, ya fito a dakin ya shiga wanda ke opposite dinsa, yana shiga Mami ta mike daga zaunen da take ta ce "Uban me zan baka ne Jawad kake bina haka, cin mutunci da kayimin bai isheka ba kazo ka karamin wani ne?" a hankali ya ce "Dan Allah kiyi hakuri ki daina fishi dani Mami, i have no mother but u, ke fa kika haifeni idan banzo wajenki ba wajenwa kike tinanin zanje naji dadi Mami, pls forgive me Mami" tsayawa tayi tana kallansa ganin yadda ya kamo hannayenta duka biyu, sosai taji jikinsa yayi dumi, ta ce "Are u sick?" Ya ce "Kawai sanyi nakeji Mami" a hankali ta ce "Ka kwanta to" kwanciya yayi akan gadon yayi pillow da cinyarta, ta jawo blanket ta rufa masa, ya limshe ido yana jin wani dadi yana ratsashi, shafa gashin kansa ta shiga yi a hankali ta ce "I hope ba zazza6i za kai ba?" ya ce "No insha Allah" daga haka ta kura masa ido, duk cikin 'ya'yanta ba wanda take jin shi har ranta kamar Jawad, tasha wahala kafin ta haifeshi, after then sai da yayi shekara 11 kafin ta haifi Sadeeq, wani lokaci saita masa abu itama taji duk bata kyauta ba, sai dai kuma idan Rafi'ah yake so ta nan bangaren sai inda karfinta ya kare, kamo hannunta yayi ya ce "Mami" ta dawo daga tinanin data lula ta ce "Ahmad" ya ce "Kiyi hakauri" ta ce "It's ok" daga haka ta gyara masa blanket din tana kallansa. Abdul ne ya shigo dakin Rafi'ah rike da baby girl, tana zaune akan sallaya ta idar da sallan la'asar, ya ce "Anty Mummy na kiranki a dakin Ummi" ta ce "Ohk, be careful karka jefarta" ya danyi dariya ya ce "Aina fiki ma iya rikewa" ita dai bata ce masa komai ba ta mike ta nufi dakin Ummi, ita da Mummy ne kawai a dakin, ta nemi waje ta zauna tana kallan Ummi ta ce "Gani" Mummy ta ce "Akan maganar sunan Babynki ne, kikace asa sunan duk wanda aka ga dama ko" ta daga kanta a hankali ta ce "Eh, duk wanda kuka ga ya dace" Mummy ta ce "Kar mu tauye miki hakki ne daman, idan akwai wacce kikeso asa sunanta saiki fada" shiru tayi at first taki cewa komai, Mummy ta ce "Ina jinki" sauke kanta tayi kasa ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso a sa" da mungun mamaki Ummi ta dago tana kallanta, sai kuma ta6e baki ta mike ta fita a dakin, Mumny dake kallanta cikin 6acin rai ta ce "Uban waye shi daza asa sunan uwarsa, shiya raini cikin? Ko shiya sha wahala dake" hawayen idanta ta share ta ce "Amma ai shi ne mahaifint..." Kafin ta rufe bakinta Mummy ta kifa mata mari, Rafi'ah ta fashe da kuka ta mike tana jaa da baya ta ce "Kiyi hkr pls Mummy"
Chapter 12 · 0% Book details