← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 46

Sashe 23

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ce "Mungode masa Engineer" Daddy ya ce "To dan Allah ki daina kuka haka nan, bari na kira mahaifin Fatima na sanar masa" Ammi ta ce "A'a dai tukunna, yanzu idan yayi wanka sai muje gidan gaba daya" Ya ce "To Allah ya kaimu" daga haka Daddy ya fita a parlorn, ana kiran Magrib Sameer ma ya fito a dakin, Ammi ta mike ta shiga dakin da Yusuf yake, fitowansa a wanka kenan, ta kura masa ido ganin yadda ya rame sosai, nan da nan kuma idanta ya kawo ruwa, Yusuf ya sauke kansa kasa ya ce "Naji sauki Ammi, u worry not" Ammi ta ce "Idan kayi sallah u meet me in my room" daga haka ta juya ta fita, kaya ya saka yayi sallah sannan yayi addu'a, karfin hali kawai yake amma shi kadai yasan abinda yakeji, mikewa yayi gently ya nufi dakin Ammi, da sallama ya karasa ciki ya zauna, ta ce "Kayi sallan?" Ya ce "Ehh" ta zauna gefensa ta ce "Ina ka shiga all this while Yusuf?" A hankali ya ce "Egypt" ta ce "You and who?" Ya ce "Umma, Khadija da kuma Jiddah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Where are they?" Ya ce "Jiddan na gidansu, but Umma da Khadija ban sani ba" nan ya bata labarin dawowarsu zuwa kwanciya a asibiti da yayi har tahowansu Kano, duk yadda Ammi taso ta danne kukanta kasawa tayi, ta dinga share hawaye, Yusuf ya sauke kansa shima yana goge hawayen idansa ya ce "Wallahi Ammi bansan meke faruwa dani ba, tin daga ranar dana tafi ban sake tina taba sai jiya, i cried alot Ammi, musamman idan na tuna yadda na tafi na barta" Ammi ta dago kanta tana kallansa ta ce "Kasan ka barta da ciki ne?" With shock ya dago kansa yana kallan Ammi ya ce "Ciki kuma? Nasan dai bata lafiya then, but bansan meyeke daminta ba" Ammi ta share hawayen idanta cikin sanyin murya ta ce "Ka barta da ciki Yusuf, she suffered alot har kamar ba zatai rai ba, haka tai ta rainan cikin har Allah ya kawo ranar haifansa, nan ma ta kasa sai CS aka mata aka cire mata yarinya" kuka ne ya kwace mata ta kasa karasawa, Yusuf dai still yayi yana kallanta, ji yake kamar ba dashi take ba, Ammi ta dago tana kallansa ta ce "Ur Baby is now 3 years old, ina tinanin idan akwai wacce zata yafe maka kaji dadi bai wuce Rafi'ah ba" mikewa yayi ya rasa abinda zaice, sai kuma ya zauna bakin gado yana furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un,, ya dinga share hawayen dake zubo masa cikin kuka ya ce "I don't know she's pregnant Ammi, this was the biggest sin i have ever made, meyasa nayi haka" ganin kamar ba hayyacinsa yake ba yasa Ammi ta kamo hannunsa ta ce "Stay calm Yusuf, u know ur condition, karka samun attack pls" rungume Ammi yayi yana kuka ya ce "This is all my fault Ammi, nasan da wuya ta yafemin" Ammi ta share hawayen idanta ta ce "It's not your fault Yusuf, Allah zai tona asirin duk wanda yakesan yaga bayanka" saketa yayi ya mike yana share hawayen idansa, Sameer ne ya shigo dakin shida Daddy, Yusuf ya ce "Bani key din motarka" Ammi ta mike tana kallansa ta ce "Ina zakaje kuma?" Ya ce "I'm going to see my wife Ammi" ta ce "Amma kasan ba matarka bace a yanzu ko?" Ya ce "Na sani" daga haka ya fita a dakin suka bi bayansa. Rafi'ah ce tsaye a kitchen tana wanke hannunta, bayan ta gama ta goge hannun da towel ta fito tana kallan Mummy dake zaune a parlor ta ce "Nifa na kira wayar Ammi several times bata dauka ba, kawai mu fara sauke Khairiyya sai mu kaiki" Mummy ta ce "An fasa jiran Jawad din ne, naga yace yana hanya" Rafi'ah ta dan 6ata rai ta ce "Yanzu fa bayan magrib ne, kuma Ammi zatai fada Mummy, sai dai kuma idan zaki bari a fara sauketa" Ummi dake canzawa Imaan kaya ta ce "To ba sai a fara sauketa ba what's in it?" Rafi'ah ta ce "Allah sai Mummy tace sai mun sauketa sannan mu wuce" Mummy ta dalla mata harara ta ce "To badan Jawad ya matsa na jira ba da tin tini nayi tafiya ta, dama 'yar uwata nazo gani ba kowa ba, indan take da 'yarki ne ai bazan zo ba" Khairiyya ta danyi murmushi tana taya Ummi sawa Imaan takalmi, ita dai Rafi'ah tin data turo baki ta samu waje ta zauna, bata mike ba sai da taji horn, ta tashi ta saka hijab Mummy ta ce "To Zainab Allah bamu alheri, gobe dai a kaimin Imaan ta wuni" Ummi ta mike zata rakasu ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ta kalli Khairiyya dake saka shoes dinta ta ce "Kin dauki ledan karki manta" ta ce "Ehh gashi nan, nagode Ummi sosai" Ummi ta ce "Ki gaishe da Amminki" ta ce "To zataji" suna fita compound motar Daddy ta shigo gidan, Mummy ta ce "Bako kukayi ne, ashe ba Jawad din bane" tana rife bakinta motar Jawad ma ta shigo, Imaan ta wara ido ta tafi da gudu tana kiran "Daddy" dai dai nan Yusuf ya fito a motarsu ya kurawa cute girl din ido, Ammi ma duk suka fito a motar, Rafi'ah ta dafe kirjinta zata durkusa Ummi ta rikota, cikin 6acin rai Mummy ta nufi Yusuf ta shako shi tana fadin "Ubanme kazo yi gidan nan Malam, kazo ka karasa kasheta ne?" Shi dai Yusuf banda kallan Imaan ba abinda yake, harta dale jikin Jawad sannan ya sauke idansa a kansu, yana juyowa kuwa Mummy ta sauke masa mari a kumatunsa hawaye na sakkowa a idanta ta ce...
Chapter 23 · 0% Book details