← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 46

Sashe 36

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce "Ya gama shan ruwan ne?" Ba tare data kalleshi ba ta daga masa kai, Ya ajiye ledan hannunsa yana kallan Yusuf ya ce "How are feeling now?" Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Jawad yaja kujera ya zauna ya ce "Allah ya sauwake" ya ce "Ameen" zaro wayarsa a pocket yayi yana dannawa, kusan minti 10 suna zaune kafin ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Ina Imaan?" ta ce "Tana gida" bude kofar dakin akayi Ammi da Mummy suka shigo, Jawad dake kallansu yayi murmushi suka sake gaisawa da Ammi ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki sannu da kokari, Allah ya maka albarka" Sameer ne ya shigo dakin rike da ledan Apple, Mummy ta ce "Jawad muje ko?" Ya ce "Ohk to" kallan Yusuf yayi ya ce "Allah ya sauwake" Yusuf ya amsa da "Ameen" daga haka ya fita, Mummy ta ce "Hajiya sai gobe Allah ya yaye masa" Ammi ta ce "Ameen, Allah ya kaimu" mikewa Rafi'ah tayi tana kallan Ammi ta ce "Allah ya sauwake Ammi" ta ce "Ameen, mungode" ta gefen ido ta kalli Yusuf ta ce "Sai da safe" bata jira ya amsa ba ta fice a dakin Mummy tabi bayanta, a parking space suka sami Jawad yana zaune a mota, Rafi'ah ta shiga front seat Mummy kuma ta shiga baya, kallan Mummy yayi ta mirror ya ce "Yau kam gida zan kaiki ko?" Mummy ta ce "Aa sai gobe zan koma, danma jikin Rafi'ah da sauki" ya danyi murmushi yaja motar suka tafi ya ce "Mami tace ai yau zatazo duba Fatima nace bata gida" Mummy ta ce "Gobe idan ka kawota sai mu koma, shi dai Sadeeq bazai shiga mutane ayi komai dashi ba, kullum yana wajen abokai suna yawan banza" Jawad ya ce "Day before yesterday ma Mummy sai dana masa magana, bayasan shiga mutane saam" Mummy ta ta6e baki ta ce "To watakila zai daina, kai naka ada ai saida mukaita rokon Allah, gara shima yana shiga abokai" Jawad ya shafa kansa yana murmushi, ita dai Rafi'ah tana zaune tayi shiru, bayan 10 minutes suka karasa gida, Jawad yayi parking a waje Mummy ta fito ta ce "To saida safe" daga haka ta shiga ciki, kamo hannun Rafi'ah yayi cikin sanyin murya ya ce "Dear kinyi shiru" ta danyi murmushi ta ce "Ba komai" sai kuma ta sauke kanta kasa, ya gyara mata hijab din jikinta ya ce "Ohk, kici abinci sosai, sai ki kwanta" a hankali ta ce "Pls kayi hkr abinda nayi dazu, naga hannunsa da ciwo ne kuma..." Duk da baiji dadin abinda ya gani ba amma ya danyi murmushi ya daura Finger dinsa akan lips dinta ya ce "U don't have to explain, ba komai" murmushi ta sakar masa ta bude kofar zata fita ya ce "Good night" ta daga masa hannu ta rife kofar sannan ta shiga ciki. Washegari karfe 12 Yusuf na zaune akan gadon asibiti yana lunch Khairiyya ta fito a toilet, ta zauna gefenshi ta ce "Ya jikin Yaya?" ya ce "Lafiya lou" ta ce "Baka jin komai?" Ya ce "Naji sauki" dan murmushi tayi tana kallansa ta ce "Yaya Nabeel ya kusan dawowa, tare zamu koma inji Daddy, in fara makaranta shi kuma yana Masters dinsa" Yusuf dake jujjuya abincin hannunsa da spoon ya ce "Ina din?" Ta ce "America mana" girgiza kai yayi ya ce "No, ba dai keba, dan bazaki jeba" ta ce "But Daddy yace idan inaso inje fa Yaya" ya ce "Ki bari ki nema admission anan, i think it will be good for u, it's not safe mace karama irinki ta tafi wata kasa karatu" dan 6ata rai tayi ta ce "To ai angama bada admission Yaya" ya ce "Then u wait till next year" bata daice komai ba ta mike ta fara diban abinci tana hade rai. Kwanciya Imaan tayi saman carpet taki kar6an Apple din da Rafi'ah ke mika mata, Rafi'ah ta zare mata ido ta ce "Will u collect it like this or no?" kamar zatai kuka ta noke kafada ta ce "That's not how Papa used to gave me" cikin fishi Rafi'ah ta bar wajen ta shige dakinta, Imaan ta fashe da kuka tana shamba kafa hade da kiran Papa, Abbane ya fito a daki ya dauketa yana jijjigata ya ce "Me aka miki haka little Fatee?" cikin kuka ta ce "I want to eat Apple" Abba ya dauki daya daga cikin Apples din kan plate ya bata taki kar6a, ya ce "Ba kyaso ne kuma?" Ta dan turo baki ta ce "Daddynah yana yankamin ai, not that Daddy with Blue car, the fair one" sai kuma ta kara 6ata fuska ta ce "And he was sick" dakin Rafi'ah Abba ya bude ya sameta kwance tana waya, tayi saurin mikewa ganinsa, ya ce "Jeki yanka mata ki bata, ya za'ai ki barta kuma tana kuka mamana?" Hannun Imaan ta kama kamar zata fashe da kuka ta ce "To Abba sai tace ita sai abinda takeso, tin dazu nake mata hidima kamar wata baiwa" Ummi da shigowanta dakin kenan ta dalla mata harara ta ce "To karkiyi idan kinga dama, nan kika kafa mana kuka sanda ubanta ya dauketa, yanzu common ki yayyanka mata Apple zakice kina mata hidima, ai ke ba'a miki ba da kina karama girma kawai kikai" daga haka ta kama hannun Imaan dake share idanta, Abba ya ce "To menene abin fada anan kuma Madam?" Ummi ta ce "Saita zauna ai idan taga dama ta shekara tana kwance" daga haka ta fita da Imaan, Abba ya kalli Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Are u happy with what u did?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Ki daure kina mata abinda takeso kinji mamana, ke kinsan irin rigimar da kikai ne?" Ta danyi murmushi ta boye fuskarta da head tie dinta, Abba yayi saki murmushi ya nufi kofar fita ya ce "Allah ya miki albarka".
Karfe 1:30 Mami tazo ta duba Rafi'ah, ta kawo mata fruits iri da kala, sun jima suna hira da Ummi kafin Sadeeq yazo ya dauketa, karfe 3 Ummi ta gama shirya basket din asibiti, Rafi'ah ta fito sanye da hijab tana kallan Ummi ta ce "Ke baza kije ba?" Ummi ta ce "Naga da safe naje, kuma munyi waya da Ammin tace may ba a sallamosu yau da daddare" Rafi'ah ta ce "Ohk" Ummi ta ce "Zaki tafi da Imaan ko?" ta wani hade rai tana kallan Ummi ta ce "Gaskiya ni zata takuramin Ummi, naga itama dazu da ita kikaje, yanzu mafa da kyar na samu na bata wayana kafin tayi shiru" Ummi ta ta6e baki taci gaba da kwashe abinci a warmer, Rafi'ah ta dauki basket din ta ce "Saina dawo" Ummi ta ce "A dawo lpy" daga haka ta fita zuwa parking lot Mustapha yaja suka bar gidan.
Within few minutes suka iso asibitin, Mustapha yayi parking sannan ta fito ta shiga ciki, da sallama ta tura kofar dakin ta shiga, Sameer ya dago kai yana kallanta sannan ya amsa, Yusuf na kwance akan gadon yana kallan ceiling, by now babu komai a hannunsa jininma ya kare, ya mike a hankali ya zauna yana kallanta, sauke idanta tayi ta ajiye basket din a gefe ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau" ta ce "Ya jikin?" Ya ce "Da sauki" kallan Sameer tayi dake danna wayarsa ta gaishe shi ya amsa mata da fara'ah ta ce "Ammi fa?" Ya ce "Basu jima ba suka koma gida ba ita da Khairi" ta ce "Ayyah" shiru tayi ta zauna caan gefe, wayar Yusuf dake gefenta ne ya fara ringing, ta kalli screen din sannan ta dauke kai, harya katse shima Yusuf baibi ta kan wayar ba, aka sake kira for d second time Rafi'ah ta ta6e baki ta kara kauda kai, Yusuf ya bude idanuwansa dake limshe yana kallan wayar ya ce "Pls help me with the phone" ta dauki wayar ta mika masa sannan ta koma kan kujeran ta zauna, a hankali yayi picking call din ya ce "Jiddah" ta fashe masa kuka ta ce "Wai meyasa baka kula dani ne Doctor, ko bakasan abinda ke cikina ne? u just left us aside kamar bamu da hakki akan ka" Yusuf ya ce "Banajin dadi we will talk ltr or tomorrow" daga haka ya katse wayar ya kashe phone din baki daya, mikewa Sameer yayi yana kallansa ya ce "Bari naje waje na huta Doctor" Yusuf ya ce "Ba komai, a huta lpy" daga haka Sameer ya fita, kusan minti 2 basuce komai ba, kowa yana zaune inda yake, Yusuf ya sauko a kan bed yana gyara zaman rigarsa ya nufi toilet a hankali, gaba daya jikinsa yayi weak, yana isa bakin kofar yayi saurin riko handle din jin zai fadi, Rafi'ah ta ce "Subhanallah" hannu ya daga mata alamar ba komai sannan ya shiga toilet din ya rufo kofar, bayan few minutes ya fito a toilet din, still dai he's not normal wani jiri yaji ya debeshi, Rafi'ah tayi saurin rikoshi ya fada jikinta, sai da sukai kamar zasu fadi sannan yayi karfin hali ya riko kujera suka fadi a nan wajen, bude kofar Jawad yayi ya shigo da sallama, Rafi'ah rayi saurin janye jikinta daga nasa ta matsa gefe, karasowa Jawad yayi yana kallan Yusuf ya ce "Are u ok?" Yusuf ya daga masa kai ya ce "U pls help me to my bed" Jawad ya kamashi ya mike sannan suka karasa kan gadon ya zauna, Rafi'ah na zaune kan kujeran kanta a kasa, kirjinta banda bugawa babu abinda yake, Jawad ya zauna a kan karamar kujera dake gefen bed din ya ce "Amma ya jikin?" Yusuf ya ce "Da sauki" Jawad ya ce "Masha Allah, yau an gama kama duk wani wanda yake da hannu a tafiyarka, sannan takaddun filayenka da gidajenka na wajen Umma yana office dina, dukda bincike ya nuna akwai abubuwa da dama da suka siyar, gobe insha Allah zan kawo maka takardun, abinda sukai amfani dashi ko suka siyar ka barsu da Allah, that's your own destiny in life, Allah kuma ya kara tsaremu daga sharrin masu hali irinsu, and i wish u quick recovery" sauke ajiyar zuciya Yusuf yayi ya kamo hannun Jawad dake gefensa ya ce "I don't know the words i will used to thank u Barrister, u have been there for me right from the beginning till end, jazakallahi khairan, u made so much to me which i can never pays u back, ka zamo gatan yarinyana a lokacin da take neman soyayyar mahaifi, ka bata gata wanda ko a wajena inaga da wuya ta samu kamarsa, u are a real man Ahmad, abinda ya faru a baya ka yafemin" Murmushi Jawad yayi me kyau yana kallansa ya ce "Allah ya yafe mana baki daya" Yusuf ya ce "Ameen" mikewa Jawad yayi ya basa hannu ya ce "Allah ya sauwake sai goben" daga haka ya nufi hanyar fita, yana fita Rafi'ah tabi bayansa da sauri, a parking lot ta sameshi tsaye yana kokarin bude mota, ta ce "Yaya zamu tafi tare" sau daya ya kalleta ya dauke kai, nan da nan idanuwanta suka cika da kwalla, ta ce "Kayi hkr, wallahi faduwa zaiyi shine na rikesa, i didn't do it intentional" ko ya daga kai ya kalleta, ta fashe da kuka ta dora kanta a bayansa ta ce "Wallahi i love u Yaya, i love u more than anyone else, pls don't leave me here" ta kankameshi tana kuka sosai and she didn't mind the way people are looking at them.
Chapter 36 · 0% Book details