← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 46

Sashe 13

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*_I want to see sweets and meaningful comments_* 🤗
_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_7_

A hankali ta durkusa kasa nan bakin kofa tana goge hawayen idanta ta ce "I don't mean to hurt u Mum, u said i should say out what's in my mind, kuma na fada miki ban boye miki komai ba, da nasan hakan zai 6ata miki rai wallahi i won't even say a word" daga haka ta kara fashewa da kuka, Abba ne ya bude dakin jin kukanta, ya kalli Mummy dake zaune har lokacin ranta a 6ace ya ce "What's going on? Why are u crying Mamana?" ita dai Mummy bata ce komai ba, Abba ya kama hannun Rafi'ah suka fita a dakin zuwa dakinsa, a bakin gado ya zaunar da ita yana kallanta ya ce "Keep quite and tell me what's wrong with u" a hankali tasa hijab dinta ta share hawayenta ta ce "Sunce na fadi sunan da za'a sama Babyn shine nace sunan..sunan.." Share mata hawaye Abba ya shiga yi ya ce "Feel free and tell me Mamana" sauke kanta tayi wasu sababbin hawaye na kara gangaro mata ta ce "Sunan Maman Doctor nace, Abba he has no one sai yarinyar nan, ai banyi laifi ba tinda shine dai mahaifinta, no matter how, ko kisa yake i can't change him from who he is, he still remain her father, but she slapped me Abba" cikin rarrashi Abba ya ce "Ya isa kiyi shiru, duk abinda kikeso shi za'ayi, ki kwantar da hankalinki kinji ko?" kai ta daga masa sannan ta mike ta ce "Nagode Abba" cike da damuwa ya ce "Ba komai Mamana" daga haka ta nufi kofar fita, tana bude kofar suka ci karo da Ummi, ta sunkuyar da kanta ta koma gefe, bayan Ummi ta shige ta fita ta jawo kofar.
Tin daga ranar har ranar suna Ummi ko Mummy basu kara mata magana akan sunan ba, ita ma kuma bata ce komai ba, bata san kuma wane hukunci suka yanke ba, ranar suna tin da safe Mummy ta kira mai make~up ta mata, duk da haushinta takeji hakan bai hana ta shiryata ba, tsaf Mummy ta shiryata cikin tsadden lace dinta, tayi mungun kyau sosai da sosai, sai dai har lokacin bata san sunan da aka sawa Babyn ba, mikewa tayi kamar marar lafiya ta haura stairs Gwaggo ta bita da kallo, dakin Abba ta shiga ta rufo kofar, ta zauna gaban mirror tana karewa dakin kallo, tasan an kawo stickers jiya amma kuma bata gansu ba, mikewa tayi ta dinga bubbude drawer ko zata gani amma babu, daga kanta tayi ta hango bakin leda akan wardrobe, ta jawo stool ta hau kai sannan ta dauko ledan, zama tayi a bakin gado ta bude ledan, stickers ne masu yawa a ciki, ta dauko daya tana karantawa, ta saki wani murmushi ganin an rubuta *Fatima Yusuf Muhammad* ta limshe idanuwanta a hankali ta ce "Thank u Abbana, i know it's you, nagode sosai" jin an bude kofar yasa tayi still a wajen tana zare ido, Ummi ta karaso tana kallanta, mikewa tayi ta kulle ladan zata mayar Ummi ta ce "Sai ki tafi dashi kasa ki kaiwa Mummy za suyi amfani dashi, ai hankalinki ya kwanta tinda kin gani" bata ce komai ba ta wuce ta fita a dakin Ummi ta bita da harara, ko data sauka ta bawa Mummy ledan ta wuce parlorn Abba ta zauna, dan ita yanzu bata san shiga mutane kafin a fara mata bori. Da yamma liss gidan Ummi ya cika da baki, aka ci aka sha sannan akai hotuna, sunyi kyau sosai kowa ka gani yana cikin farinciki, Mami ma tazo gidan, Ammi dai bata zoba saboda itama gidanta a cike yake da mutane, Mummy kuwa duk wanda ya tambayeta sunan Babyn sai ta dan hade rai kafin ta fada, kusan magrib duk yawanci mutanen sun watse, sai 'yan uwa, wannan karan dai ba dangin Abba da suka kwana part din Anty Amina, a cewarsu a biki ma basu ji dadi ba, sabida haka basu ma zo da yawa ba. Wajen karfe 9 na dare Rafi'ah na zaune dakinta tana breastfeeding babynta Ummi ta shigo da flask a hannunta, ta dan sauke kanta kasa ganin har Ummi ta iso indan suke, tin data haihu bata yarda tayi breastfeeding a gaban kowa ba, ko dai ta koma daki ita kadai ko kuma tasa veil ko hijab da rufe jikinta, gaba daya she was uncomfortable, Ummi ta ce "Kije parlorn Abba Jawad yazo" ta ce "Ohk" Ummi na tashi ta turo baki ta jawo dan kwalinta dake kan gadon ta sannan ta kwantar da babyn ta dora dan kwalin tasa hijabi sannan ta dauketa suka fita. zaune ta sameshi a parlor ya sha manyan kaya, ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "U are welcome" ya ce "Thank u, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah" bayan ya kar6i babyn ta kalli Cannula dake hannunsa, dan zaro ido tayi ta ce "Are u sick?" Ya ce "I recovered, nayi zazza6i ne" ta dan turo baki ta ce "But baka fadamin ba" ya ce "Is because is not that critical, idan muna waya ai bakya ganewa" ta ce "Yes, karfin hali kake kenan, amma ka rame ma" ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Mind not Rafi'ah, naji sauki sosai" shiru tayi tana wasa da fararen yatsunta, ya ce "Allah ya raya mana Fatima Zarah akan sunnah, mai suna ki kaiwa kanki shine ko kunya babu" ta danyi dariya ta ce "No, sunan Maman Doctor ne, kuma sunana, kaga taci sunan manya" ya ce "Hakane, i also like the name" ta ce "Really" ya ce "Yes" shiru ne ya biyo baya, ta dago kanta tana kallansa taga ita yake kallo, kara sauke kanta tayi, ya danyi murmushinsa me kyau ya ce "Let me ask u" ta ce "I'm all ears" ya ce "Shi Doctor bai fada miki inda zai tafi ba? bai kuma ta6a ce maki akwai kasar da yake son zua ba?" Kin dago kanta tayi jin hawaye ya gama taruwa a idanta, Jawad ya dago kanta yana kallanta, tayi saurin limshe idanuwanta nan kuma hawayen ya samu damar sakkowa, ya share mata hawayen ya ce "I didn't ask u to cry, tambaya fa na miki, or have u forgotten my profession?" Ta girgiza kai ta ce "No, ni bai ta6a fadamin ba" ya ce "But how was his reaction sanda ya baki takardan sakin?" Ta dan turo baki, sai kuma ta ce "He's somehow, hankalinsa kamar baya jikinsa, komai yi yake kamar ana controlling dinsa, but nasan ya tsaneni ne shiyasa, i don't know why bai nunamin true color dinsa ba sai dana aureshi, i regreat knowing him Yaya Jawad, nasan dai it's my destiny kuma raban na haifi wannan abin ne" Jawad ya kamo hannunta yana kallan cute face dinta data wanku da hawaye ya ce "Stop saying all this Fatima, kiyi ta addu'a kawai, idan shine alkhairinki kuma ba shiya cuce kiba, definitely one day zaku..." Shiru yayi yana kallanta, sai kuma ya goge mata hawayen idanta ya ce "Everything will be fine soon, and u stop calling my baby wannan abin" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "To Fatima" ya ce "No, she's bearing ur mother's in-law name, ba zamu kirata da sunan ba" ta bude hannayenta alamun bata sani ba, sai kuma ta ce "Ni bansan me zan ce mata ba" ya ce "Zamu kirata da *Imaan*" ta dan yi murmushi ta ce "Insha Allah" ya ce "Good baby girl, to kiyi min murmushi" ta sake yin murmushi sannan ta boye fuskarta tana dariya, mikewa yayi ya kwantar da babyn akan shoulder dinsa ya ce "I'm going, Allah ya raya mana Imaan" ta ce "Ameen Barrister" daga haka ta mike ta kar6a babyn, har compound ta raka shi sannan ta dawo ciki. Bayan ya karasa parking lot ya bude boot ya ciro babban trolley yana kallan Mustapha ya ce "Ka shigar da shi ciki, but ka budemin gate kafin nan" Mustapha ya ce "Angama oga" daga haka ya bude masa gate, Jawad ya koma mota ya tayar sannan ya fita a gidan. Jan trolley Mustapha yayi har cikin parlor, Gwaggo ne da wasu mata na zaune suna cin abincin dare, ya ajiye akwatin zai fita Gwaggo ta ce "Ke kuma fa?" Ya ce "Cewa yayi na shigo da shi" ta ce "Wa?" Ya ce "Wanda ya fita" Gwaggo ta ce "Ohh dan gidan Hadiza" mikewa tayi zata ja akwatin taji nauyi, Abdul da fitowansa a daki kenan ya tsaya kallanta ya ce "Ina ke ina daukar wannan Gwaggo" ta ce "Maza dauki ka kaiwa Zainab, muje tare dan naji akwatin da nauyi" Abdul yaja trolley suka haura stairs, Ummi da Mummy na zaune a parlor suna magana, ganin Gwaggo yasa sukai shiru, ta ce "Maza shigo dashi" Abdul ya ajiye akwatin a tsakiyar parlor ya ce "Gaskiya da nauyi" daga haka ya fice a parlorn, Ummi ta ce "Wannan fa Gwaggo?" Gwaggo ta zauna ta ce "Ina na sani, dan gidan Hadiza ne ya kawo yace a shigo da shi" Mummy ta ce "Wace Hadiza?" Gwaggo ta zauna gaban akwatin tana zugewa ta ce "Hadiza abokiyar zamanki mana, mu a danginmu akwai me irin sunan ne?" Nan da nan Mummy ta hade rai, Ummi dai kallan kayan cikin akwatin kawai take, pamper ne manya~manya sai kaya masu tsada iri iri da overall, wipes, tissue, baby soap, baby lotion, baby perfume, towels, earrings, rings, socks, vip, pants, duk wani tarkacen da ake bukata sai daya siya ya zuba, bayan Gwaggo ta gama ciccirosu ta kalli Ummi ta ce "Kinga idan ta gama shayarwa sai kawai ayi aure, dan tin ba yau ba nasan wannan yaran santa yake, wannan figigiyar jaririyar na cika wata tara dama ta yayeta, ai tama mata mutunci, naga ubanta tin cikinta bai fito ba ya gudu ya barta" Mummy ta mike ta wuce dakin Rafi'ah, fitowanta a toilet kenan, Mummy ta ce "Yaushe Jawad yazo gidan nan?" Ta sauke kanta kasa ta ce "Dazu, amma ya tafi" Mummy ta ce "Meye tsakaninki da Jawad Rafi'ah?" Ta dan zaro ido ta ce "Ni kuma" Mummy ta ce "Sai kizo parlor kiga abinda ya kawo miki" daga haka ta juya ta fita a dakin, hijab dinta ta saka sannan ta fito, ta tsaya caan bakin kofa tana kallan tilin kayan dake gaban Gwaggo, Mummy ta wuce dakin Ummi ranta a 6ace, Ummi ta mike tabi bayanta, a bakin gado ta sameta a zaune, Ummi ta ce "Karfa ki yanke hukunci baki tabbatar da abu ba" Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai bazai ma yiwu mu hada zuri'ah da Hadiza ba, yanzu ma ba abinda muka hada amma tabi ta takurawa Rafi'ah" Ummi ta ce "Allah ya kyauta" daga haka ta fita a dakin. Komawa daki Rafi'ah tayi ta dauka wayarta ta kira Jawad amma phone dinsa a kashe. karfe 10 da rabi Mummy ta kwashi 'yan kwananta suka wuce gida, tana parking ta fito suka nufi cikin gida, murda handle din Mummy tayi taji a rufe, Anty Salma ta ce "Ko dai sunyi bacci" a takaice ta ce "Akwai key a jakana" daga haka ta ciro key a hand bag dinta ta bude suka shiga.
Washegari karfe 8 bayan sunyi wanka Mummy ta mike don ta samar musu abinda zasu yi breakfast, a parlorn Abi ta samu Mami tana hadawa Jawad tea, shi dai yana zaune akan kujera ya limshe ido, Mummy ta dan kalleshi sannan ta wuce kitchen, within few minutes ta dafa musu indomie ta juye cikin babban tray sannan ta kai wa su Anty Salma dakinta, dawowa parlor tayi tana kallan Jawad ta ce "Ahmad" ya bude idanuwansa a hankali yana kallan Mummy, ta ce "Ka shigo parlorna zamuyi magana" Mami ta ajiye serving spoon din hannunta ta ce "Ya za'ai kina gani bashi da lafiya kice masa ya tashi har wani ya shiga parlor ki" daga mata hannu Mummy tayi ta ce "Look, banfa yi dake ba, dashi nake idan kuma ba zai shiga ba, yayi wa kansa" mikewa Jawad yayi gently yana shafa gashin kansa, Mami ta ce "Koma ka zauna tinda nina haifeka ba wata ta haifamin kai ba" , zama zaiyi akan kujera Mummy ta ce "Ohk sbd bani na haifeka ba saika zauna kenan" ya dan kalleta sai kuma ya kalli Mami dake tsaye wajen dinning ta wani hade rai, Mummy ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Well, idan kaga dama ka zauna saboda ni ban isa na baka umarni ba, amma fa ka sani akwai abinda zaka zo kana nema a wajena, kana tinanin zan baka a haka?" Shiru yayi yana kallanta sai kuma ya sauke kansa kasa, Mummy ta juya ta shige part dinta, bin bayanta zaiyi Mami ta ce "Come back and sit down Jawad" ya juyo yana kallanta yama rasa abinda zai ce.
Chapter 13 · 0% Book details