Sashe 26
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
nan a cell wallahi, mijin da Khadija ta aura shiyasa aka kama mu, bayan ya saketa yace sai an biyashi duk kudin daya kashe mata, to nidai ga ATM's dinka dukka a hannuna ba damar ciran kudi, yanzu abinda nakeso da kai ka wuto station din ka kar6i ATM card ka ciro kudi a biyasu muma duk mu huta" Yusuf ya ce "To gani nan zuwa, a wani station ne?" Ta ce "Na nan unguwar Rimi, kusa da first bank" ya ce "To in zuwa" daga haka yayi hanging call din, Abba ya sauke ajiyar zuciya ce "Then sai muje station din ko?" Yusuf ya ce "Ohk to" Abba ya mike yana kallan Ummi ya ce "Ku wuce gida, mu zamu je staion din, koma me ake ciki i will call u" Ummi ta ce "Alright safe" Juyawa Abba yayi yana kallan Jawad dake gyarawa Imaan gashin kanta ya ce "U follow us too barrister" Jawad ya ce "Ohk" duk mazan mikewa sukai suka fita, Yusuf ya sauke kansa kasa ya fita Mummy ta bishi da kallo, itama duk jikinta yayi sanyi, Jawad ya nufi kofar fita Imaan tabi bayansa da gudu kamar zatai kuka ta ce "Zan bika Daddy" daukanta yayi suka fita a parlorn, Ammi ta kalli Khairiyya ta ce "Kije Sameer ya baki key din motar karya manta ya tafi dashi" Khairiyya ta mike ta fita bayan ta amsa da to, ba jimawa ta dawo da keys guda biyu, ta mikawa Ummi daya ta ce "Yaya Jawad ne yace in kawo, wai ya tafi da Imaan tana kuka saita bishi" Ummi ta ce "Ohk" Ammi ta kalli Mummy dake zaune tayi shiru ta ce "Kuyi hakuri dan Allah Hajiya Halima, nasan abubuwan da suke faruwa akwai ciwo, amma ba wanda ya wuce kaddararsa, Allah ya kaddara hakan zai faru, kuma indai aka sameshi da laifi nayi alkawarin zan bada goyon baya a hukuntashi dai dai da abinda kotu ta yanke masa" Mummy ta ce "Allah ya mana me kyau, amma kuwa idan matar caan ne tayi sanadiyar wargaza mana zuri'a wallahi Allah ne kadai zai rabani da ita, me muka mata? Me muka tare mata a rayuwa Aisha? Meyasa zata sa yarannan cikin wani rayuwa?" Ummi ta ce "Allah ya rufa asiri" Ammi ta ce "Ameen" sannan ta mike ta ce "Zamu wuce mu kam" Ummi ta mike itama ta ce "To sai anjima" daga haka su Ammi suka fita, Mummy ta dago Rafi'ah dake kuka tin tini ta ce "Kiyi shiru Rafi'ah, insha Allah duk wanda yakesan yaga bayanki ba xai ci nasara ba" ta kama hannunta suka fita a parlorn Ummi tabi bayansu. Tafiyar minti 6 sukai ya kaisu station din saboda dama a unguwar ne, Jawad na rike da Imaan suka shiga ciki, shima har lokacin basu hada ido da Yusuf ba, direct office din DPO suka shiga, kawu Umaru ya masa bayanin komai, DPO ya musu bayanin dramar da akai lokacin da aka kamo Anty Khadija, shi dai Yusuf na gefe duk jikinsa yayi sanyi, lokaci lokaci yakan kalli Imaan dake hannun Jawad tana wasa da hular kansa, DPO ya ce "To yanzu dai yace court za'a tura su dan sai anyi musu shari'ah" Kawu ya ce "To muma akwai case din da muka kawo a kansu, ina ga zamu rubuta statement sai a hada rana daya" DPO ya ce "Ba matsala insha Allah" juyawa Yusuf yayi ya fita a office din yana kallan dan sandan dake tsaye bakin kofa ya ce "Dan Allah akwai wasu mata da aka kawo jiya, inasan ganinsu" dan sandan ya ce "Ko kaine wanda suka kira" ya ce "Ehh nine" dan sandan ya nuna masa inda suke sannan ya dawo bakin aikinsa, a hankali Yusuf ya karasa wajen ya leka, suna nan zaune aka kasa dauro duk yaci ubansu sai susa suke, Umma ta taso da sauri ta ce "Dan Albarka, ga ATM din guda 4 bansan dai da wanne za akai amfani ba" Yusuf bai kalleta ba ya ce "Ohk, zaku fita nan yau insha Allah Umma" daga haka ya kar6i ATM cards din ya yasa a pockets dinsa ya juya, Umma na murmushi ta kalli Khadija dake zaune ta ce "Aina gaya miki zaizo, amma me zaisa zan kira Umaru, banda wa'azi ba abinda zaizo ya mana a wajen nan, karshe ma yasa a kaimu kotun". bayan an gama rubuce~rubuce Jawad yayi signing ya kuma tura case din zuwa court dinsu, ba 6ata lokaci akai printing takarar yasa a pocket dinsa, Abba ya ce "Yanzu akwai wani abu kenan?" Ya ce "A'a, idan naje office zan karasa komai sai asa date din da za'a fara zaman" Abba ya ce "To Allah ya kaimu" Daddy ya kalli Yusuf dake zaune kan bench kansa a kasa ya ce "Are u alright" Yusuf ya ce "Sure Daddy" kiran da DPO yayi wa Jawad ne yasa ya mike ya fita, sai lokacin Yusuf ya bishi da kallo, Imaan dake jikin Abba ta 6ata fuska kamar zatai kuka, Yusuf ya mike yana kallanta ya ce "Come" ta mika masa hannu ya dauketa suka fita a office din Daddy ya bisu da ido, fita sukayi a station din ya tsaya a ATM machine yayi withdrawing 30k sannan yasa a pocket dinsa ya tari cab, bayan sun shiga ya ce "Old GRA" mai cab din ya ja suka tafi, a hankali Yusuf ya kalli Imaan da tai collapsing ajikinsa ta rungumeshi, ya rungumeta shima yayi kissing kanta ya ce "I luv u daughter"