Sashe 5
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
_08103810398_
*I appreciate all ur calls and messages, nagode sosai da sosai i'm more than healthy now 🤗*
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._
_By FATIMA ✍🏻_
_3_
Da yamma Rafi'ah na zaune a parlor tayi pillow da cinyar Ummi aka danna bell, Ummi ta dan kalleta ta ce "Open the door Rafi'ah" mikewa tayi a hankali tasa Himar dinta sannan ta bude kofar, murmushi ta danyi ganin Ammi a tsaye, Khairiyya ta rungumeta calmly ta ce "I missed u Anty" a hankali Rafi'ah ta ce "I missed u namesake" daga haka ta matsa gefe Ammi ta shigo. With smile Ummi ta cire glasses din idanta ta ce "Sannu da zuwa Hajiya" Ammi ta zauna akan sofa tana kallan Rafi'ah dake tsaye ta ce "Sannu, jiki ya fara sauki ko" Ummi ta ce "Sosai wallahi sai godiyar Allah" sake hannun Rafi'ah Khairiyya tayi ta ce "Ina yini Ummi" ta ce "Lafiya kalau Khairi, how are u?" Khairiyya ta ce "Fine Ummi", zama duk sukayi a kan carpet, Ammi ta kalli Ummi ta ce "Amma ta rage aman ko?" Ummi ta ce "Ehh, yau dai tinda ta tashi ba tai ba jikinma da sauki sosai" Ammi ta ce "Allah ya kara mata lafiya, ya kuma bata hakurin jurewa" Ummi ta ce "Ameen". Cikin few Minutes Saudatu ta jerawa Ammi abinci da abinsha, duk cikinsu ba wanda ya ci, Khairiyya ce kawai ta sha Mango juice, bayan sun dan jima Ammi ta kara musu sannu suka wuce, sosai itama taji dadin ganin jikin Rafi'ah.
A haka rayuwar Rafi'ah ta dinga tafiya wata rana ta tashi garau wata rana taita amai harda zazza6i, duk bayan kwana biyu Jawad ya kanzo ya dubata, ba laifi yanzu tayi sabo dashi ba kadan ba, tin tana kin gaya masa abinda takesan ci harta fara fada masa, wata rana ma a waya zata kirashi, idan kuwa ta kira ko me yake sai ya bari ya kawo mata abinda ta bukata, kullum kara kwantar mata da hankali yake yana nuna mata misalai kala kala wanda suka faru kuma a yanzu komai ya zama tarihi. A yanzu a gidansa yake kwana, abinci kawai yake zuwa yaci idan yaga dama shima, dan mostly idan yaje gaishesu baya wani cin abinci, Mami kuwa komawarsa gidansa ba karamin dadi ya mata ba, hankalinta kwance ya fiye mata yazo ya gaisheta ya tafi, kayan Babies yake saya sosai yana tarasu cikin wani akwati, sai da yaga ya cika sannan ya daina sayan kayan, gaba daya unisex ya saya saboda baisan me zata haifa ba. Bangaren Sameer ma baiyi kasa a gwiwa ba, yakan zo ya duba Rafi'ah time to time, shima duk abinda yasan tana so saiya kawo mata, ita dai kawai kulashi take amma harga Allah batasan zuwan sa gidan, bata so ta sake sakin jiki da dangin Yusuf, yawanci Jawad yana haduwa da Sameer a gidan, idan ya tambayi Rafi'ah sai tace wani dan uwan Yusuf ne, ba wani shiri suke da Sameer ba, ko gaisuwa randa bata kansu basa yi. Rafi'ah kuwa tin sanda cikinta ya girma take zama da hijab, idan ta cire hijabi to tana tare da Ummi ne ko Mummy ko kuma Saudat, amma ko Abba ne yazo yini zatai tana yawo da hijab a jikinta, musamman da cikin ya shiga wata 8, kullum fadansu da Ummi ta tashi tayi aiki, dan tinda ta daina laulayi Ummi ta raba musu aikin gida ita da Saudat, wani lokacin harda kuka take karasawa sabida gajiya, ga ciwan baya da yake daminta sosai, amma hakan baisa Ummi ta daga mata kafa ba, gaba daya ta kara ramewa tayi fari akan da.
kwanciya tayi akan gado tana sauke ajiyar zuciya, toilet dinta ta gama wankewa shine ta mike ta dan huta, tana jin an bude kofar dakinta ta juya tana kallan me shigowa, Ummi ce ta shigo da shirinta na zuwa aiki, ta zauna gefen Rafi'ah dake kwance ta ce "Kin sharemin parlorn?" Girgiza kai tayi kamar zatai kuka ta ce "Banyi ba, wallahi na gaji Ummi" Ummi ta mike tana kallanta ya ce "U don't have to, ki tashi kije ki gyara parlorn nan, sannan kuyi abinci idan kinga dama kuma ki gudu ki barta tayi ita kadai, idan kin huta kuma ki wanke inner~wears dinki da kika jera min su a toilet dan bazan wanke ba" hawayen idanta ta share bata ce komai ba, Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Sai na dawo" tana fita Rafi'ah ta jawo phone dinta ta kira Mummy, bayan ta daga tayi sallama, da kyar ta amsa tana danne kukan dake cinta, Mummy da hankalinta ya fara tashi ta ce "Lafiya Fatima? Meya faru ne?" Cikin muryar kuka ta ce "Kinga Ummi bata daina sani aiki ba, kuma bayana ciwo yake bazan iya ba wallahi" daga haka ta fashe da kuka, Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To kiyi shiru ki daina kuka, kiyi abinda zaki iya sauran ki bar mata shi, zanzo yau da yamma, ban san meyasa Zainab ke haka ba wallahi, aiki ai kina yi amma wallahi baza kiyi abinda yafi karfin kuba, dama caan ba lafiya ba balle kuma ga larura, zanzo da yamma idan ta dawo" to kawai tace tayi hanging call din, da kyar ta mike ta zauna, ta kurawa kananun kafafuwanta ido ganin yadda suka kumbura, ta zira su kasa gently ta sauko akan gadon sannan ta dauki hijab dinta ta saka, koda ta sakko kasa kwanciya tayi akan kujera, sai sauke numfashi take daki daki, tana nan zaune Saudatu ta fito a kitchen tana murmushi ta ce "Anty Rafi'ah lafiya dai?" Ta ce "Ehh, hutawa nake" daga haka ta turo baki ta gyara kwanciya akan kujera ta limshe ido, bacci ne me shegen nauyi ya dauke ta, sai karfe 12 ta tashi, tana kallon agogo tayi sauri ta dauko tsintsiya sannan ta dawo ta fara share parlorn, tana gamawa kuwa batai mopping ba Ummi ta shigo tayi parking, Rafi'ah ta kalli Saudatu dake dariya kasa kasa ta ce "Dan Allah kice mata banda lafiya har amai nayi, zanje na kwanta" daga haka ta wuce sama da sauri.
```1 month ltr```