Sashe 32
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ce "Amma meyasa all this while da abubuwan suka faru baki zo kin sanar da kanwar mahaifiyarsa ba" Jiddah tayi kasa da kanta ta ce "Saboda nima ina sanshi, matukar nayi niyyar tona asirinsu zasu rabani dashi" Jawad dake kallanta ya girgiza kai ya kara ce wa "To yanzu wane dalili ne yasa ki kai magana?" A hankali ta ce "Saboda naga suna hannun hukuma kuma sannan tayi fatan Yusuf ya mutu saboda bata da asara, saboda taga ni nake dauke dauke da cikinsa, hakan yasa har mukai fada ta mareni nima na rama" with shock duk mutanen wajen suka tsaya kallan Jiddah, Abba ya girgiza kai ya maida kansa gefe yana addu'a kasa kasa, gaba daya tausayin Rafi'ah yakeji, lokaci daya suka canza mata rayuwa tin tanada karanci shekaru har zuwa yanzu, ita dai Rafi'ah ta kifa kanta akan kujerar wajen tana kuka sosai. Wani abokin aikin Jawad ne ya mike yayi rubutu a wata farar takardar sannan ya mikawa na kusa dashi ya ce "Zaki iya tafiya" Jiddah ta fito a wajen ta koma ta zauna, Yusuf dai na zaune kansa a kasa shima, tsabar bakin ciki kasa kuka sosai yayi, Jawad ya kalli Umma dake tsaye gefen Anty Khadija ya ce "Hajiya Fatima kin daiji abinda matar Yusuf tace, ko a maganganunta akwai abinda baki yarda kun aikata ba?" Umma tayi wulli wulli da ido ta rasa abin cewa, sai kuma ta ce "To idan tone tone ne ba sai ayi ba, aiba mu kadai mukai wannan aikin ba akwai wasu wanda suka bamu gudumawa kusan ma nasu yafi yawa" ganin abinda Alkali yayi yasa Jawad ya sauke kansa kasa irin yadda sukeyi alamar girmamawa sannan ya karasa wajen Alkali ya kar6i takardar hannunsa, duk sauran lawyers din wajen mikewa sukai suma, Jawad ya ce "Kotu ta daga shari'ah nan zuwa jibi wato 9 ga watan 9" police din dake gefe suka kara tasa keyar su Umma da hannunsu na daure da handcuffs suka wuce dasu. Mikewa Yusuf yayi ya saba Imaan a kafadarsa suka fita, Rafi'ah ta dago kanta ta kalli direction din da yake zaune taga bayanin, mikewa tayi da sauri ganin su Mummy na magana da Ammi, Abba yana gaisawa Daddy, fitowa tayi daga court din ta tsaya a compound tana kallan motocin dake parke a wajen amma bata gansu ba, hakan yasa ta nufi gate da sauri ta fita, tana fitowa a gate taga Napeep dinsu ya tashi, tayi saurin taran wani Napeep din ta shiga ta ce "Dan Allah wannan Napeep din zaka bi" daga haka ta gaya masa number Napeep din. A kofar gidansa aka sauke shi, ya bashi kudinsa sannan ya ajiye Imaan a kasa ya zaro key din gidan ya bude padlock din, daga haka ya tura gate din ya dauki Imaan suka shiga, da sauri Rafi'ah ta sakko a Napeep dinta ta bashi 500 ta juya da sauri ta shiga gidan, Yusuf ya juyo jin an bude gate din, da mamaki yake kallanta sai dai bace komai ba, hawaye na sauka a idanta ta ce "Nazo na tafi da Imaan, baka da wani dalili da zaka rabani da yarinyana" Yusuf ya mata wani kallo ya ce "I'm her Father, so u let me idan na yanke shawara zan baki ita from now till tomorrow" cikin tsawa ta ce "Stop saying u are her father Doctor, u don't know anything about her, idan ma akwai wanda ya dace ta kirashi mahaifi to Yaya ne" a hankali ya gyarawa Imaan zama a hannunsa ya ce "Tinda shiya miki cikinta sai kice masa yazo ya kar6a miki ita, and get out in my house now" daga haka ya juya ya bude kofar parlor ya shiga ya rufo kofar yasa sakata, yana zama wasu hawaye masu zafi suka sakko masa, bubbuga kofar da Rafi'ah keyi ne yasa ya mike ya share hawayen idansa ya bude kofar yana kallanta da jajayen idanuwansa cikin 6acin rai ya ce "What do u want then? get out and stop knocking my door before i show u the bad side of me" ya karashe maganar ransa a 6ace yana nuna mata hanyar gate.