← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 46

Sashe 42

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

insha Allah zanzo miki kafin ki koma" ta danyi murmushi ta ce "Ina nan kwana 3 zanyi" ta ce "To sai kin ganni, ki gaishe da mutanen gida, bari na karba phone number ki" Saudatu ta ce "Ameen" daga haka ta saka mata number, Ummi ta ce "To bari na saukeki" ta ce "To ba komai" upstairs Rafi'ah ta nufa ta dauko kayan Imaan set biyu tasa a karamin jaka sannan tayiwa Ummi sallama suka fita, tinda suka fito Jawad yake kallanta yana murmushi, bayan sun shiga motar ya ce "Sai kyau kikeyi wife" ta dan turo baki ta ce "Ummina zata fita yanzu dan girman Allah next week ka kawoni" ya ce "Angama Madam" daga haka yaja motar suka tafi. Suna zuwa kofar gate dinsu yayi horn ya shiga yayi parking, Imaan ta fito da gudu ta nufi cikin gida, ita dai Allah ya gani yanzu bata wani sakewa idan tana tare da Mami, Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "U look sick, ko har yanzu zazzabin ne" ta girgiza kai a hankali ta ce "Ni banajin komai kuma" daga haka yaja hannunta suka nufi entrance din gidan, da sauri ta janye hannunta ganin ba saketa zaiyi ba, ya juyo yana kallanta sai kuma yayi dariya ya bude kofar, Dukkansu suna zaune a parlor Mummy na yiwa Ikram kitso, Mami kuma ta dora Imaan a cinyarta tana fada mata tare da Daddy suka zo, da sallama suka shiga parlorn, Rafi'ah tayi saurin sauke kanta kasa ta zauna akan carpet, zama yayi a tsakiyar Mami da Mummy ya gaishesu, Ikram ta gaishesa sannan Rafi'ah ma ta gaishe su, Ikram ta ce "Anty ina wuni" sauke kanta tayi kasa ta ce "Fine" Mummy ta ce "Har yanzu zazza6in ne? Shekranjiya da mukai waya tace tana zazza6i" ya ce "Ehh amma taji sauki, dama yini daya ne tayi, data sha magani shikkenan" Mummy ta ce "To Allah ya sauwake, ya kuke ina babu komai" ya ce "Alhamdulilah ba komai" Tashi Ikram tayi ta jera mata abinci a gabanta ta ce "Anty ga abinci" ta girgiza kai ta ce "Na koshi Ikram, yanzu ai 10am ne, sai anjima" Ikram ta ce "To bari na tattara" da hannu Jawad ya mata alamar ta barshi ya ce "Zataci, bata ci komai ba" Mummy ta ce "To maiyasa Fatima, ko murnar zuwa gida ne?" Ta girgiza kai a hankali, Mummy ta ce "To dauki abinci kici" daukar warmer Ikram tayi ta shiga parlornsu ta ce "Zaki fi jin dadi anan, feel free pls" Mummy ta ce "To ki tashi ki bita" a hankali ta mike tabi bayan Ikram, Mami dai na zaune sai murmushi take tana shafa bayan Imaan dake kwance a jikinta. Zama Rafi'ah tayi akan carpet tana kallan Ikram ta ce "Pls i need a cup of tea" Ikram tayi dariya ta ce "Laa dama yunwa kikeji shine kikai shiru" murmushi tayi ta ce "Ba wani yunwa" Ikram ta fita tana dariya, bude babban warmern tayi taga chips ne da soayyan kwai, ta bude dayan taga farfesun kayan ciki, kauda kanta tayi gefe da sauri ta rife warmer ta fara jaa baya tana kokarin tashi, kafin ta karasa tashi ta fara kwararo amai a wajen, dai dai lokacin Mami ta shigo Jawad na biye da ita, yayi kanta da sauri yana dagata ya ce "What's wrong with u?" Magana zatai amma ta kasa saboda wani aman daya taho mata, Ikram da shigowanta kenan ta tsaya kallansu, Mami ta sauke Imaan ta karasa kusa dasu ta ce "Kace taji sauki?" ya ce "Ehh but bansan kuma meke damunta ba" Mami ta ce "To dadin meyake daminta?" ya dago yana kallanta sai kuma ya sauke kansa ya ce "It's malaria probably with typhoid" kama hannun Rafi'ah Mami tayi tana masa wani kallo suka shiga daki, toilet ta kaita ta wanke mata baki sannan ta kwantar da ita akan gado, tana bude kofa ta ganshi tsaye yayi folding hannyensa, ta ce "Kasan tanada ciki ka fito da ita a haka?" Ya dan shafa kansa ya ce "Mami ita ta takura saita fito, and i noticed she was pregnant day before yesterday" wuce shi tayi ta jawo kofar dakin ta ce "Da kace Malaria ne?" Ya ce "Uhm da farko haka Doctor yace min".
Chapter 42 · 0% Book details