Sashe 44
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Zaune suke akan gado ta mimmike kafanta yana mata massage, jin yana bata labari yaji tayi shiru yasa ya dago kansa yana kallanta, kar6e handout din hannunta yayi ya ce "Wai yanzu kam baki da lokacina ko Fatima?" Dan zaro ido tayi ta mike tana kallansa ta ce "Allah sarki Yayana, wallahi ba haka bane kaga final exams zanyi ga babynka kullum yayita damuna" ta karashe maganar tana turo baki, rungumeta yayi sosai yana shafa cikin ya ce "Soon zaku rabu Baby, 2 months ya rage mana" ta danyi murmushi ta ce "I hope so, ranar dana haihu zanyita bacci ko sweetheart?" Ya bata light kiss ya ce "Exactly Babynah" dan zabura tayi ta ce "Wait!! Honey did anyone came today?" Ya ce "Wa kenan?" Ta ce "Sadeeq tailor, yace zai kawomin dinkuna na" ya girgiza kai yana murmushi ya ce "Bai kawo ba, nidai ya kirani yace in baki hakuri" wayarta ta jawo akan bed side drawer yayi saurin kwacewa ya rungumeta ya ce "Me zakiyi?" A fusace ta ce "I want to call him, bayan shi yayi alkawari zai kawomin har gida, wallahi idan bai gama..." Bakinshi da taji a cikin nata ne yasa tayi shiru, ya fara bata hot and romantic French kiss, kusan 3 minutes suna a haka kafin ya zare bakinshi a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce "Ya kawo yana dakina" ta danyi murmushi ta rungumeshi ta ce "Da gaske Yayana" ya daga mata kai, ta sake sakin wani kyakkyawan murmushi ta ce "Dama ya za ai ina yayar Amare kanwar ango ace ba'a kawomin dinkuna na ba" dariya ya danyi ya ce "Kin dai girmi Khairiyya amma Ikram tafi ki" ta dan turo baki ta ce "Amma ai Yayanta nake aure sabida haka i'm her Aunt" collapsing tayi a jikinsa ta ce "Yaya Ikram dinmu zata sha girki, ance fa Ya Sameer baya awa daya baici abinci ba, he eats alot" shi dai murmushi kawai yayi hannunsa na kan cikinta ya ce "Da zaki zama kamarsa dana fi kowa jin dadi" ta zaro ido ta ce "Ni din" ya ce "Eh mana, nafiso kiyita cin abinci ki kara kiba" a hankali ta ce " To zan dinga ci" daga haka ta mike da kyar ta sauka akan gadon ta ce "Bari na dauko dinkin" ta fita ya bita da kallo, duk sai yaji tausayinta sosai ganin yadda cikin ya mata nauyi, ya sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah ya rabata dashi lafiya.
Washegari ya kama Saturday ba school, da sassafe Rafi'ah ta tashi ta musu breakfast sannan ta koma dakinta tayi wanka, sosai tayi wani sanyayyen kyau ga cikinta dan dass lol, tana cikin daura dankwali aka bude kofar dakin, ta juya da sauri jin kamshin turarensa, suna hada ido ta ce "Wooow, Yayana kayi kyau" ya karaso inda take yana murmushi ya durkusa dai dai cikinta ya bashi kiss ya ce "Good morning Baby" ya dora hannunsa akai, dan 6ata rai tayi ta juya kanta a hankali, ya mike ya rungumeta ya ce "How was your night" kamar batasan yin magana ta ce "It wasn't nice" ya dago yana kallanta da sauri ya ce "What makes it boring sweetheart" turo baki tayi bata ce komai ba, ya danyi murmushi ya ce "Ni dai ban yarda ba, ninasan yesterday night was so nice and sweet, ko in tuna maki" daga haka ya kai bakinshi saitin kunnenta yana magana yana murmushi, dan tura shi tayi ta ce "Ni dai banaso" ya ce "Then how are u?" Ta kara turo baki ta ce "I'm not fine" bakinshi ya kai saitin nata ya bata light kiss ya ce "Laifi na miki ne?" Kamar zatai kuka ta ce "Ba saida ka kula unborn dinka ba sannan ka kulani" ta karashe maganar idanta tap da hawaye, wani serious and tidy hug ya bata yana murmushi ya ce "I'm sorry sweetheart, ina sanki fiye da komai nawa, bama kece silar zuwansa duniya ba? I love u more than u think" ta danyi murmushi itama ta rungumeshi ta ce "I love u so much my Barrister" hannunta ya kama suka fita a dakin sukai breakfast, bayan sun gama ta dauko veil dinta da side bag tana kallansa ta ce "Let's go" ya ce "Nifa banasan a kallan min ke" ta kalli jikinta ta ce "Yaya to ai ba'a ganina" mikewa yayi ya gyara mata veil din ya ce "Cover my property" ya karashe maganar yana kashe mata ido daya, ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka fita, key yasa a kofar sannan suka wuce parking lot, ya bude mata mota ta shiga ya zagaya nasa mazaunin ya kunna motar.
Suna hawa bakin titi ya kamo hannunta ya ce "What gift do u want for ur convocation?" ta juyo tana kallansa ta ce "Saura 5 weeks fa Yaya" ya ce "I know, so nake na sani da wuri" ta danyi murmushi ta ce "Just anything sweety, i will appreciate what ever u give me" ya ce "Kin bani za6i kenan?" Ta daga masa kai, ya ce "Ohk angama". Few minutes ya kaisu gida, yayi parking ta fito tana kallansa ta ce "Sai dai ka bini a baya" ya danyi murmushi ya bi bayanta bayan ya rife motar, a balcony ta tsaya jin hayaniya a parlorn, bayan Jawad ya karaso ta kamo hannunsa ta ce "Kamar sunyi baki" shidai bai saketa ba kuma baice komai ba, ya murda handle din kofar, Khairiyya ce da Ikram sai Sadeeq suna buga uban musu, suna ganinsa duk sukai shiru sai Sadeeq dake dariya yana fadin "Baku da wayo ai, ku yarane" shigowa Jawad yayi yana rike da hannun Rafi'ah, ganin su Khairiyya ne yasa ta saki murmushi, suka taso da sauri suka rungumeta, Jawad dake kallansu ya ce "Ku kyaleta ta xauna" suka saketa kowaccensu na murmushi suka gaishe shi, a takaice ya amsa yana kallan Sadeeq ya ce "Kaima dai ka nemo mata aure zan maka" Sadeeq ya kwashe dariya ya ce "Allah ko Yaya" Jawad ya ce "Uhm" daga haka ya shiga part din Mami, Rafi'ah ta kalli Ikram dake zuba mata zance ta ce "Ku rakani wajen su Mami" hannunta Ikram ta kama suka shiga part dinsu, Mami na zaune ita da Mummy da uban kaya gabansu suna hadawa cikin akwati, duk kuma dinkakku ne, Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta gaishe su, Mami ta ce "Ya jiki kuma" a hankali ta ce "Da sauki" Ikram dake kallan Khairiyya ta ce "Kinga wai su Mummy suma harda anko, jiya sun cika wani akwati yau ma sun cika wani" ita dai Khairiyya murmushi kawai tayi, Mummy ta dalla mata harara ta ce "To kar muyi anko, kijimin iskanci banda bikinki sai kuma na Sadeeq idan yana da niyya, saboda haka gara muyi yadda muka ga dama" dariya sukayi Mummy ta ce "Ai gaskiya ne, idan kuwa Sadeeq yayi aure sai bayan shekaru kafin Abdul shima yayi, lokacin dai karfinmu ya kusan karewa, sai kuma na Imaan idan da kwanan mu" Jawad ya ce "Ni baza a yiwa yarinya na auren wuri ba" Mummy ta kama ha6a ta ce "Ikon Allah, ita wannan figigiyar matarta ka shekaranta 17 tayi auran farko, kaima kuma a shekara 21 ka aureta idan auran wuri ne ai bakayi magana ba" ya dan ta6e baki ya mike yana kallan Imaan dake bacci a kan kujera. Mikewa Rafi'ah tayi suka shiga dakin Ikram, bayan sun zauna Ikram ta ce "Anty ankawo mana dinkinmu bari kigani" Ikram ta jawo wani babban akwati ta ce "Sauran suna dakin Mami, anko zamu dingayi har a gama bikin" ita dai Khairiyya tayi shiru, dan harga Allah kunya take idan ta tuna wai Yusuf zata aura musamman a gaban Rafi'ah,,,, kaya kala kala duk bibbiyu iri daya Ikram taita fito dasu tana nunawa Rafi'ah, sunyi mungun kyau sosai, Rafi'ah ta ce "Masha Allah, Allah ya kaimu nan da 2 weeks din nan musha biki" daga haka ta kalli Khairiyya dake boye fuskarta a jikin gado, kamo hannunta Rafi'ah tayi ta ce "Zo muyi magana Khairi na" Khairiyya ta matsa kusa da ita a hankali ta ce "Gani Anty" Rafi'ah tayi murmushi ta bata side hug ta ce "Ki daina kunyana dan Allah, idan ba haka ba zan kira Yaya Yusuf na gaya masa kuma zance ko magana bakya min" ta dan zaro ido tana murmushi, Rafi'ah ta saukar murya caan kasa ta ce "Ko baki aureshi ba dole watarana zaiyi aure, kuma nima ba gashi nayi aure naba, ki saki jikinki ni ki daina kunyana haka nan, i pray ma in the next 1 year Imaan nada kanwa" tayi saurin runtse idanta tana murmushi, Ikram ta ce "Anty wallahi ke kadai takewa kunya, kinga wayar data dinga yi jiya da daddare" Rafi'ah ta ce "Na sani ai, yaushe suka zo?" Ta ce "Kwanan su uku yau, nima idan zasu tafi zan bisu nayi kwana biyu" Rafi'ah ta ce "Ina din?" Ikram ta ce "Gidan Ammi" Rafi'ah ta ce "Ehh lallai baki da kunya, kuma duk ana kallanki sai a barki kije" Ikram ta danyi baya sannan ta ce "Ehh mana, kema fa Anty da kina kwana a gidan nan, kuma ai abinda kuke keda Yaya yafi wanda nayi" pillow Rafi'ah ta jefa mata ta ce "Banasan sharri kuma, aini akwai yayar mamana a gidan, ke kuma wajen wa zakiji?" a hankali ta ce "Ya Sameer" sakin baki Rafi'ah tayi tana kallanta, ita dai Khairiyya sai babbaka dariya take tana daga kwance, Ikram ta dan harareta ta ce "To Khairiyya ma ta ban shawara, suyi hiransu muma muyi namu" ta6e baki Rafi'ah tayi ta mike da kyar ta ce "Ni bazan iya muku ba, bari naje parlor" Ikram ta ce "Ai kuwa duk inda kikai binki zamuyi" bude kofar dakin akai Imaan ta shigo da gudu ta rungume Rafi'ah, sosai ta kankame yarinyar tana bata kiss ta ce "I missed u daughter" Imaan ta ce "I missed u too Momma", daga haka ta dauko sabon Tablet dinta akan gado tana nunawa Rafi'ah ta ce "Papana ya siyamin sabo, harda laptop" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Masha Allah, kince kin gode ko" ta daga mata kai tana kallan Khairiyya ta ce "Ko Antyna?" Khairiyya ta ce "Ehh kin fada" kama hannun Imaan Rafi'ah tayi ta ce "Ko ruwa baku bani ba kun tsareni da surutu" mikewa sukai suka bi bayanta Khairiyya ta ce "Sorry Anty" daga haka suka fita a dakin.
Abinci kala biyu suka jera mata a parlor taci tasha sannan suka ci gaba da hira, kuma duk hiran akan yadda bikinsu zai kasance ne, karfe 3 da rabi Jawad ya dawo gidan shida Yusuf da Aliyu, suna zaune a parlor suka shigo, Ikram ta mike tana kallan Khairiyya ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Yauwa sannu, ina fatan baku sata surutu da yawa ba" murmushi sukai gaba daya, bayan sun zauna Rafi'ah ta ce "Ina wuni Ya Yusuf" ya ce "Lafiya kalau our future Barrister" ta danyi murmushi kanta a kasa, sai boye cikinta take da hijabi, Jawad ya ce "Ba Ya Yusuf zakice ba ango zakice" ita dai murmushi tayi ta mike tana kallan Aliyu ta ce "Ina yini" ya ce "Alhamdulilah madam, ya gida" ta ce "Lafiya kalau" daga haka ta nufi part din Mummy, Khairiyya dai da kyar ta gaishesu dan kunyan Jawad take, ko yana waje bata fiye magana ba, itama kuma Ikram haka ne, tsoransa take gani take kamar zai iya dukanta idan tayi shirme. Hannun Khairiyya Ikram ta kama suka shiga part din Mummy, suna zaune a parlor ita da Rafi'ah suka shigo, Mummy ta ce "To kun kai musu abin sha?" Ikram ta dan ta6e baki ta ce "Khairiyya ki kai musu" wani kallo Khairiyya ta mata ta ce "Wallahi ke zaki kai" kasa kasa Ikram ta ce" Ai naga ba azo da Yaya Sameer ba" Khairiyya ta dan turo baki ta ce "Mummy kinji abinda tace ko" Mummy ta ce "Cewa nayi fa kuje ku kai musu abin sha, kuyiwa Mami magana nima yanzu zanje mu gaisa" daga haka ta mike, Rafi'ah ta ce "Mami tayi bacci ita da Imaan, bansan yanzu ko sun tashi ba naji an kira sallan la'asar" Mummy ta ce "Imaan ta koya mata baccin rana, da dai batayi" Rafi'ah ta danyi murmushi kawai, hijabi Mummy tasa ta fita a dakin, Rafi'ah ta kalli Ikram ta ce "Karku kai musu komai idan kunga dama mu yanzu zamu tafi" Ikram ta danyi murmushi ta ce "Allah sarki Antyn mu insha Allah a gidanki zamu ringa kwana da biki" mikewa Rafi'ah tayi ta dauki veil dinta ta shiga daki, ba jimawa ta fito sai tayi kyau sabida ta shafa powder da lipstick, Khairiyya ta kamo hannunta ta ce "Safe journey Anty, sai munzo next week" ta ce "To Allah ya kaimu, Ikee bye bye" hannu duk suka daga mata sannan suka fita tare, part din Mami ta shiga ta mata sallama sannan ta fito suka fita parking lot, Yusuf na shirin fita suka fito, Rafi'ah ta daga musu hannu ta ce "Safe Ya Yusuf" ya ce "Alright sis" daga haka ya kashewa Khairiyya ido yaja motar suka fita, da sauri ta dauke kai Ikram nata dariya. Bude hannaye Jawad yayi yana kallan Rafi'ah, ta karaso a hankali ta shige jikinsa, ya rungumeta, kallan su Ikram yayi ya ce "To mungode bye bye" kansu duk a kasa suka juya, Ikram ta dan ta6o Khairiyya kasa kasa ta ce "Yayanmu yanzu baya kunya" Khairiyya ta danyi dariya ta ce "Ya kai Yaya Sameer?" Duka ta kai mata tayi saurin kaucewa ta shige gida.