← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 46

Sashe 45

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

_2 weeks ltr_

Su Ikram ne zaune a daki da friends dinsu suna ta pictures, sunyi kyau sosai cikin kayansu iri daya, bude dakin akai Rafi'ah ta shigo da warmer a hannunta, sosai tayi wani mungun kyau sai sheki take, ga cikinta ya fito sosai cikin gown din jikinta, juyawa Khairiyya tayi tana kallanta ta ce "Wooow Antyn mu u look so cute" Rafi'ah ta danyi murmushi tana amsa gaisuwar da friends dinsu ke mata ta ce "Ai kune da kyau Khairi, Amare irinku haka kyawawa" dariya suka danyi Ikram ta ce "Pls Anty Yaya ya fita ne?" Rafi'ah ta ce "Yana daki, is anything wrong" kamar zatai kuka ta ce "Dama zamuje Saloon ne kuma naji dazu yace baxamu sake fita ba sai za'aje kamu" murmushi ta danyi ta ce "Zan mishi magana, sai drivernsa ya kaiku, ga abinci nan kuci" daga haka ta juya ta fita, daya daga cikin friends dinsu ta ce "Woow Antynku ta birgeni Ikram, kyakkyawa ce" Ikram ta danyi murmushi ta ce "To ko zaki dawo ku zauna tare" dariya sukai sosai sannan Khairiyya ta jawo warmer da plate ta fara zuba musu abincin.
Tana bude dakin ta sameshi gaban mirror yaci Ash shadda yana saisaita hular kansa ya juyo suka hada ido, ta danyi murmushi ta karasa gabansa ta ce "Masha Allah Yayana me kyau" rungumeta yayi yana shakan kamshin jikinta ya ce "I love u wife, inasan kullum in dinga jinki a jikina, i don't want to miss u even for a seconds" daga haka ya shiga kissing dinta passionately, bayan seconds ta zame jikinta tana dariya ta ce "Naki yawan" ya ce "Pls" juyawa tayi ta koma bakin kofa ta ce "No pls, Yaya su Ikram zasuje Saloon" ya ce "Let them, amma daga nan su dawo" ta ce "To, bakamin fishi bako?" Ya ce "Uhm" juyawa tayi tana murmushi ta fita a dakin, kasa kasa ya ce "I will caught u".
Karfe 5 na yamma aka shirya amare tsaf cikin kayansu iri daya aka tafi wajen kamu, kowa da kowa ya tafi amma banda Rafi'ah dake hannun Jawad, tana zaune bakin mirror daure da towel tana turo baki ya fito a toilet, ta dauke kanta taci gaba da abinda take, kusanta ya karasa ya rungumeta ta baya ya ce "I'm sorry wife" kin kulashi tayi sai dai hawaye ya taru tap a idanta, ta zame jikinta a hankali zata tashi ya ce "Won't u pardon me Baby, yau fa throughout baki kula dani ba" kafin tayi magana hawayen idanta ya shiga sakkowa, ya rungumeta sosai yana jijjigata ya ce "Kiyi hkr dan Allah, bari na tayaki ki shirya mu tafi" ba musu ta zauna ya fara mata drying kanta yana mata combing dinsa, bayan sun gama ya dauko kayanta dake kan gado ya ce "Should i help?" Ta daga masa kai, daga haka ya tayata ta shirya, gaban mirror ta zauna ta fara make up shi kuma ya fita zua dakinsa, within few minutes ta gama make~up dinta me kyau, ta dora dankwalinta sannan ta feshe jikinta da turare ta dauka veil dinta ta shafa, woow masha Allah tayi wani sanyayyen kyau, side bag dinta ta dauka ta lankaya sannan ta fita a dakin, tsayawa tayi tana kallansa ganin yadda yayi kyau, ya sakar mata murmushi ya ce "Masha Allah, zamu haifa cute babies insha Allah" murmushi ta danyi ta dauko wayarta a jaka tana kallan screen din, ya ce "Who's calling?" A hankali ta ce "Ameera" daga haka ta dauka wayar, Ameera ta ce "Ban ganki ba" ta ce "Ina hanya Amarya" daga haka ta danyi murmushi tayi hanging call din, Jawad ya ce "Ta kusa aure ne?" Ta ce "In the next 1 month zatai aure" ya ce "Allah ya sanya alkhairi" ta ce "Ameen" daga haka ya bata side hug suka fita.
Suna shiga wajen kallo ya dawo kansu saboda yadda sukai kyau, ta dan zame hannunta a cikin nasa ta nufi inda Ameera ke zaune, Imaan ta taso da gudu ta rungumeta ta ce "Look at Papa" ta nuna mata Yusuf dake gefen Khairiyya a high table, ta daga musu hannu tana murmushi sannan ta zauna tasa Imaan a cinyarta, Ameera ta ce "Kuma kika bar Ogan a gefe" juyawa tayi taga yana zaune gefen Aliyu suna hira, ta juyo sannan ta ce "Gashi ga abokinsa nan, ina Ogan naki ke?" Ameera ta ce "Ya tafi Kaduna kuma yayi niyyar zuwa wallahi" Rafi'ah ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya" ta ce "Ameen, wai yaushe zaki haihu musha suna?" Rafi'ah ta ce "bayan auranki da wata 1" Ameera ta ce "Kina nufin sauran wata 2" ta ce "Insha Allah" Sosai da sosai akaci akasha sannan akai hotuna kowa ya watse. Washegari ya kama Saturday karfe 1 aka daura auren Yusuf da Khairiyya da Sameer da Ikram, bayan 'yan daurin aure sun dawo akai hotuna sosai. Da Daddare kuwa bayan Isha aka fara shirye shiryen kai Amare, gida daya aka kaisu kowa da nata part din, gidan yayi mungun haduwa, suna kuka haka aka barsu kowa ya watse, Rafi'ah ta musu nasiha sosai sannan ta basu misalai kala kala ciki kuwa harda abinda ya faru da ita, sanda ta tashi tafiya saida suka sata kuka itama, da kyar ta daure ta karasa mota ta shiga, Jawad dake zaune yana jiranta ya ce "Allah ya basu zaman lafiya, muma muje muci namu amarcin" harara ta dan 6alla masa ta turo baki ta maida kanta gefe, yayi murmushi yana shafa beard dinsa yaja motar suka tafi.

*4 YEARS LATER*
Chapter 45 · 0% Book details