Sashe 19
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"To kace baka santa zan maka dole ne Yusuf?" Kama kansa yayi ya kara furta innalillahi wa inna~ilaihirraji'un, ya dago yana kallan Umma ya ce "Kenan shekara 4 tana gida? All i can remember is lokacin da muka je gidansu ziyara, i think she was 2 weeks in my house then, amma Umma ni bayan nan na manta ta a rayuwana ne" mikewa yayi kamar zaiyi hauka ya ce "Why Umma, muna zuwa Kaduna once in a year amma kuma baki ta6a tinamin ita ba, ban manta da kowa ba sai ita Umma, why? Meyasa haka ya faru dani ne?" Umma ta mike ta ce "Ni ina zan sani Yusuf, tinda ka saki yarinyar nan kana abu kamar kowa amma baka sake tambayarta ba, to zan maka dole saika dawo da ita ne" kifa kansa yayi akan dinning yana karanto addu'o'i ko zai samu saukin abinda yakeji, har yanzu he's so surprise da abinda ya faru da shi, duk yadda yake saan matarshi amma ya manta ta lokaci daya, shekara 4 bai sake maganarta ba sai yau, da karfi ya ce "Noo, it's impossible, i dont know what comes over me 4 years back" daga haka ya wuce daki da sauri yana kallan Jiddah ya ce "Where is my key?" Sai xare ido ta ke ta ce "Yanzu fa past 9pm kuma a Egypt kake da mota ba anan..." Wani mungun tsaki yaja ya wuceta ya fice a dakin ta biyo bayansa, lokaci daya yaji zuciyarsa ta buga, ya danne kirjinsa da hannunsa na dama yana furta subhanallah, anan wajen ya xu6e sumamme, Jiddah ta kwala ihu tana kiran Umma, da sauri Umma ta fito a daki ta ce "Faduwa yayi?" Cikin kuka Jiddah ta ce "Umma ya samu attack me tsanani, pls do help Umma, mu kaisa asibiti karya mutu, nima wallahi mutuwa zanyi, ganin Umma ta tashi ta shiga daki Jiddah ta mike ta fita a parlorn, dayan apartment din gefensu ta nufa, dayake dama gidan haya ne ta fara musu knocking kamar zata balla kofar. Anty Khadija na daga wayar Umma ta ce "Kin isa ne?" Ta ce "A'a Umma, sai gobe zan karasa ina cikin Kano a hotel" Umma ta ce "To da asuba zaki fita, ya tashi yana tambayar meyasa aka barshi ya saketa, yanzu dai ya samu attack ya sume gashi caan parlor, ki lalla6ashi ya gyara mana aikin nan Khadija, ki bashi ko nawa ya bukata" Anty Khadija ta ce "Toh Umma" daga haka tayi hanging call din. Koda Umma ta fito parlor neighbor dinsu harya sa Yusuf a mota, ta zura hijabi ta kullo kofar ta shiga motar suka tafi, wani nearest private hospital suka kaishi inda cikin gaggawa aka karbeshi. kusan awa daya su Umma na reception a zaune sannan akai kiransu, Jiddah banda kuka ba abinda take, Dr ya musu bayanin komai, cewar su kwantar da hankalinsu, amma anyi admitting dinsu zuwa gobe, daga haka ya wuce office dinsa, Umma ta shiga dakin da yake Jiddah tabi bayanta, yana nan kwance akan gadon idanuwansa a limshe, neighbor dinsu na kansa yana masa sannu, Jiddah ta kamo hannunsa cikin kuka ta ce " Karka maida abinda yake cikina maraya tin baizo duniya ba, dan Allah ka tashi Yaya, idan ka barni nima mutuwa zanyi" Umma ta kama hannunta suka fita a dakin ta ce "Ki daina kuka haka mana Jiddah, ko mutuwa yayi munada asara ne bayan duk dukiyarsa na hannunmu, da zarar Khadija ta dawo zai sake mance ta kuci gaba da rayuwarku" Jiddah dake kallan Umma ta kara share hawayen idanta cikin fishi ta ce "Eh ai saboda bake kika haifeshi ba zakice ya mutu, sannan bake kike dauke da cikinsa ba shiyasa xaki ce ya mutu, to wallahi Yaya ba zai mutu ba idan kuma ya mutu kema bazaki zauna lafiya ba saina tona miki asiri na gayawa duniya kece sanadiyyar mutuwar sa" Umma dake kallanta surprisingly ta ce "Jiddah ni kike dagawa murya haka? Ni zaki kalla kina nunawa da yatsa" cikin 6acin rai ta ce "An nunaki da yatsan nima ki kasheni ki huta, wallahi idan ba tashi yayi ba bazan yafe miki ba, duk kece silar abubuwan da suka faru" wanka mata mari Umma tayi, jiddah ta durkusa tana dafe da kuncinta ta ce "Ni kika mara?" Umma ta kara wanka mata wani marin ta ce "Gobe ki dinga dagamin murya kina nunani da..." Kafin ta rufe bakinta Jiddah ta wanka mata mari ta ce "Wallahi baki isa ki mareni ban rama ba"