← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 46

Sashe 11

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_6_

Parking Jawad yayi dai dai gate din gidansu sannan ya fito a motar ya rufe ya shiga ciki, Ikram ne a balcony tana wanke hijab dinta na islamiyya, ta dago tana kallansa ta ce "Sannu da dawowa" a hankali ya ce "Sannu" daga haka ya murda handle din ya shiga ciki, Abi ne kadai a parlor yana kallan TV, Jawad ya danyi kasa da kansa ya karasa gefensa ya zauna akan carpet ya ce "Sannu da hutawa Abi" Abi ya ce "Thank u son, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya mike ya ce "Let me see Mami" da kai Abi ya amsa masa sannan ya wuce part dinsu, tana nan tsaye a parlor sai kaiwa take tana komowa, jin an bude kofar tayi saurin juyowa tana kallansa ta ce "Who was that girl u were talking about? I want to hear more about her" zama yayi akan kujera yana kallanta ya ce "But i have told u iyayenta baza su bari aje yanzu ba, sai ta gama shayarwa zan baku address din gidansu sai aje tamba..." A fusace ta ce "Ni zaka mayar 'yar iska Ahmad? Are u here to tell me what i'm suppose to do, kaika fini sanin sharudan aurene, ko ce maka nayi auranta zakayi yanzu, so nake na santa na san iyayenta, now give me her number or their home address" dagowa yayi kawai yana kallanta ganin yadda take tada jijiyoyin wuya, ya limshe idanuwansa kansa na mungun sara masa ya ce "I will u give Mami, but pls u calm down, just have a peace of mind even for some minutes" harara ta dalla masa ta ce "Ce maka akai hankalina ba a kwance yake ba, just give me their address before i show u the bad side of me" ta karashe maganar tana kafe shi da ido, jin an bude kofar yayi saurin mikewa yana kallanta ya ce "I will get it to u now" riko rigarsa tayi ta ce "Ba inda zakaje, ka fadamin da baki" karasowa parlorn Abi yayi yana kallan Mami ya ce "Why all this shout Hadiza, muryarki har parlorna ana jinki haka" ba tare data kalleshi ba ta ce "Nace ka bani ko!!!" Shi dai kansa kawai ya sauke kasa, Abi ya cire hannun Mami a jikin rigarsa ya ce "What is exactly happening Ahmad?" A hankali ya ce "Ba komai" Abi ya ce "Ba komai as in how, duk wannan ihun a banza take maka kenan" dan kallan Mami yayi ya koma gefe, Abi ya kalleta ya ce "have a seat" kin zama tayi still tana ta hararan Jawad, Abi ya ce "Magana fa nake miki Hadiza" Mami ta juyo tana kallansa ta ce "Jiransa nake ya bani address din gidan yarinyar da yake nema" da mamaki Abi yake kallanta ya ce "Me zakiyi to? Ke ina ruwanki kina mace a matsayinki na uwa, in dai wannan maganar ne kima barta, when the time comes zakiji komai, jeka abinka Ahmad" a hankali ya ce "Sai da safe" daga haka ya fice a parlorn Mami ta bishi da harara, zama tayi akan kujera ta fara share hawayen idanta cikin kuka ta ce "Meyasa kake min haka Honorable, sai kace bani na tsuguna na haifi Jawad ba, akwai wanda yake da iko dashi duk fadin duniyar nan idan bani ba, amma duk sanda nazo da bukata ta saika dinga sawa yana bijiremin" Abi ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Nasan ke kika haifeshi, kuma kina da iko akan Ahmad, ba wai ina sa shi ya bijire miki bane, yanzu menene naki na neman address din yarinyar da yake nema? So kike ki zubar da girmanki a gaban 'ya'yanki ne, Ahmad yana miki biyayya iya iyawarsa but wallahi am assuring u this duk ranar da kika kaishi karshe kar kiyi mamaki, banda abinki ki kyaleshi mana, shiba yaro bane yanzu, ya san duk abinda ya dace da wanda bai dace da shi ba, so duk abinda kika ga yayi ki masa addu'a kiyi fatan Allah yasa shine alkhairi a gareshi, amma ba ki zauna kina kara daga masa hankali ba" share hawayen idanta tayi ta ce "To shikkenan, na hakura amma wallahi idan wacce nake zargi yake so yama sa a ransa babu aure a tsakaninsu" daga haka ta mike ta shige daki Abi ya bita da kallo.
Chapter 11 · 0% Book details