← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 46

Sashe 18

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya kamo duvet din kan gadon yana kokarin tashi amma ya kasa, hakan yasa ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, mikewa Jiddah tayi ta hau kan gadon tana kallan idanuwansa dake limshe kamar dazun, ta kai fuskarta kan nasa tana kuka kasa kasa, Umma ta mike ta koma dakinta inda ta samu Anty Khadija ta shirya da babban hijab dinta tasa nikab, Umma ta bata ATM card ta ce "Take care, kar ki sauka a hotel din dake kusa" Anty Khadija ta ce "To Umma, saina dawo" Umma ta ce "A dawo lafiya" daga haka Anty Khadija ta fita a dakin. Shiru Jiddah tayi tana sauraron yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri, ta mike a jikinsa ta sauka akan gadon da sauri tana kiran Umma, a bakin kofa suka ci karo, Jiddah ta rungume Umma ta ce "Na shiga uku Umma Yaya mutuwa zaiyi ya barni" kama hannunta Umma tayi suka koma dakinta ta zaunarta a bakin gado ta ce "Kinga yanzu na kira Dr kiyi shiru ki daina kuka zai samu sauki" Jiddah ta share hawayen idanta ta ce "To Umma yanzu idan yace ina Rafi'ah mai zamu ce masa, kinsan fa lokaci daya komai zai sake shi, i'm sure asirin ya bar jikinsa by now, kawai ciwansa ne ya tashi" Umma ta kamo hannunta ta ce "Asiri kam ya bar jikinsa amma Khadija ta koma ai, kuma bai manta da abinda suka faru a baya ba, yana sane da komai sai dai baisan meyasa yayi hakan ba, Allah na tuba da baya tuna komai ai sunanta ma bazai kira ba" Jiddah dake zare ido ta dan kalli Umma ta ce "To idan ya tambaya fa?" Umma ta ce "Barmin amsar a wajena" mikewa duk sukai jin ana knocking, Umma ta bude kofar parlorn tana kallan DR dake tsaye ta ce "Bismillah" ya shigo da sallama yana kallan Jiddah da idanuwanta sukai jaa suka kumbura, Umma ta ce "Ka shigo nan dakin" Dr ya bai bayanta zuwa dakin da Yusuf ke kwance, bayan ya duba shi sosai ya masa allurai sannan ya cire masa drip din da karewarsa kenan ya ce "Zai samu bacci na awa daya sai ya tashi, and i'm sure he will wake up fine" Umma ta ce "Ba wani matsala kenan?" Ya ce "Insha Allah, tinda anyi allura gobe da safe zan kawo magungunan da zai fara sha" Umma ta ce "Nagode sosai Dr, zan maka transfer yanzu nan" ya ce "Nine da godiya Hajiya" daga haka ya kalli Jiddah dake zaune gefen Yusuf ya ce "Madam Allah ya sauwake" kamar batasan magana ta amsa da Ameen, daga haka ya fita a dakin ya wuce. Rafi'a ce kwance akan sallayan data idar da sallan magrib, jin an bude kofar yasa ta mike a hankali, Ummi ta zauna bakin gado tana kallanta ta ce "Rafi'ah" a hankali ta ce "Na'am" Ummi ta ce "Kan naki bai daina ciwo bane?" Ta girgiza kai ta ce "Ya daina yanzu" Ummi ta ce "Toh Alhamdulilah u come down for dinner" ta ce "Toh" daga haka Ummi ta fita a dakin, kifa kanta tayi akan gado ta limshe ido, saam batajin dadin jikinta musamman yadda zuciyarta ke bugawa, mikewa tayi a hankali ta cire hijab din jikinta tasa hula sannan ta dauka phone dinta ta fita a dakin, kallan Imaan take dake zaune saman kujera tana bawa Ummi labarin Daddynta, Rafi'ah ta limshe ido ta wuce dinning ta zauna, Imaan ta sakko akan kujeran ta nufeta ta ce "My Daddy loves me so much ko Mom?" Rafi'ah ta dan kalleta bata ce komai ba, yarinyar ta dan hade gira tana kallanta ta ce"We just make call with Uncle Abdul, and shine yace wai Daddy baya sona wai shine yake sona, Daddy used to kiss and hug me, he bought ice cream for me, pizza and shawarma, he sometimes drop me to school or he picked me, Daddy loves me much ko Momma" daga mata kai Rafi'ah tayi ta share guntun hawayenta daya gangaro fuskarta, Imaan ta dan zaro ido ta ce "Are u crying Mom?" Girgiza mata kai tayi ta ce "No, something just enter my eye now" da damuwa Imaan ta rungumeta ta ce "Sorry, is it painful?" Ta girgiza kai ta ce "No, go and sit down" Imaan ta ce "I want to eat with u" Rafi'ah ta danyi murmushi ta daurata akan cinyarta ta ce "Alright dear" har suka gama cin abincin Imaan bata sake magana ba, saboda kullum Ummi na hanata magana idan tana cin abinci, sakkowa tayi akan cinya tana kallan Ummi ta ce "Ummi Momma didn't well" Ummi ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, kan kujera Ummi ta nunawa Imaan ta ce "U sleep there" Imaan ta hau kan kujeran ta kwanta, bata fi minti 10 ba tayi bacci, Ummi ta mike tana kallan Rafi'ah data kifa kanta akan dinning ta ce "Fatima" dagowa tayi tana kallan Ummi dake kokarin zama a kujeran dake gefenta, sauke kanta tayi kasa tana wasa da botton din doguwar rigarta, Ummi ta ce "Are u with me Rafi'ah?" Ta daga mata kai a hankali, Ummi ta ce "Duk wannan tinanin da kike ba shine mafita a gareki ba, sau nawa zance miki ki dinga addu'a ki manta da komai daya faru a baya, shekara 4 fa ba sati 4 bane, bazaki godewa Allah ki kar6i kaddararki a haka ba?" A hankali tayi wiping tears dinta ta ce "Na hakura Ummina, na kuma gode masa a haka, but ni Imaan used to makes me cry, musamman idan na tuna ba Ya Jawad bane mahaifinta, taya zanyi watarana na gaya mata haka Ummi" daga haka ta fashe da kuka, Cike da tausayinta Ummi ta ce "Shiyasa nace miki kowa da nasa kaddaran, ita nata a yadda yaxo kenan" Rafi'ah ta share idanta ta mike ta koma parlor zata daga Imaan Ummi ta ce "Ina zaki kaita?" Kanta na kasa ta ce "I want to spend the night with her" Ummi ta ce "To kisa tayi fitsari, sai ki shiryata" a hankali ta ce "Toh" daga haka ta wuce upstairs Ummi ta bita da kallo, a dakinta ta kwantar da Imaan saman gado sannan ta wuce dakin Ummi inda kayanta suke ta dauko mata kayan bacci da sucks da hula, rigarta ta fara cire mata sannan ta dagata suka shiga toilet, bayan few minutes suka fito ta saka mata kaya da socks tasa mata hula sannan ta kwantar da ita, cikin bacci ta ce "Ummi" Rafi'ah ta matsa gefenta tana shafa bayanta ta ce "It's me dear, do u need something" a hankali ta bude idanta tana kallan Rafi'ah ta ce "Dake zan kwanta?" Rafi'ah ta daga mata kai ta ce "Yes dear, is better u sleep with ur Mom, sai ki barmin Ummina ta huta" Imaan ta rungumeta ta ce "I love u momma" Rafi'ah na shafa bayanta ta ce "What do u want?" Ta ce "Water" kwantar da ita tayi sannan ta mike ta dauko ruwa ta tsiyaya mata sannan ta bata a baki ta sha, bayan ta ajiye cup din ta ce "Ki kwanta, zanyi sallan Isha" Imaan ta dan turo baki ta ce "That's not how Ummi used to makes me sleep" Rafi'ah dake kallanta ta ce "What do u want then?" Ta ce "She used to hug me nd we said a du'ah together" jawota tayi jikinta ta rungumeta sannan sukai addu'ah, suna a haka har tayi bacci sannan Rafi'ah ta zame jikinta a hankali ta sauka saman gadon ta shiga toilet. A hankali Yusuf ya bude idanuwansa saboda hasken wutan dake dakin, ya mike gently yana dafe da kirjinsa ya zauna, bin dakin ya dingayi da kallo ganin akwatinansu duk a tsakar dakin, mikewa yayi a hankali ya zura hannayensa cikin pocket ya tsaya bakin kofa, jin an bude toilet yasa ya juya da sauri suka ido hudu da Jiddah, ta sakar masa murmushi ta ce "How are u?" Silently ya ce "Fine?" Komawa yayi ya zauna a bakin gadon dan jiri yakeji kawai karfin hali yake, Jiddah ta zauna gefenshi ta rungumeshi tana murmushi, taji dadin ganin ya tashi kuma jikin da sauki, a sanyaye taji muryarsa ya ce "Sallah nawa nayi missing" ta dago tana kallansa ta ce "Tin dai na asuba da kayi shine jikinka yayi tsanani" ya dan kalleta ya ce "Wanda nayi a jirgi fa?" Ta ce "Isha na jiya kayi fa" ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya shiga toilet ta bishi da kallo, bayan few minutes ya fito ya shimfida sallaya ya tada sallah. Bayan ya rama duk sallolinsa yayi addu'a sannan ya mike, Jidda ta ce "In kawo maka abinci?" Ya ce "No" daga haka ta fita a dakin, a parlor ya samu Umma tana zaune, ya karasa gefenta ya zauna yana kama kansa ya ce "Umma" ta dago tana kallansa ta ce "Ya jikin?" Ya ce "Da sauki, is it true that na saki Rafi'ah?" Umma ta kafeshi ta ce "Ni kake tambaya ne kowa?" Ya zuba mata jajayen idanuwansa a takaice ya ce "Eh" ta ce "Shekararka nawa a Egypt?" Ya ce "Almost 4" Umma ta ce "To shekarun sakinta kenan" a hankali ya ce "Subhanallah, Umma mai tamin haka na saketa Umma, inasan matana wallahi" Umma ta ce "Kai zan tambaya wannan kuma" shiru yayi yana kallan Umma da itama shi take kalla, caan ya sake furta innalillahi kafin ya ce "Ni bansan me tamin ba, nasan dai by that time na tsaneta fiye da kowa, and i remembered when i divorced her, she's lying down on the floor and she's vomiting then, yes i remembered she was sick, but what comes over me?" Umma ta ta6e baki tana kallan Jiddah dake tsaye bakin kofa ta ce "Amma meyasa baka nemeta ba har tsawon wannan lokacin?" Ya ce "I don't know, nina manta da ita cikin rayuwa na Umma, all i know is ina tare dake da Jiddah da kuma khadija and nasan mun koma Egypt where i continue working with them with the help of ur classmate Alhaji Sunusi, after then rayuwana kawai nasa a gaba, ban ta6a tinata ba sai sau, Umma meyasa baku yi komai a kai ba kuka barni na saketa" Umma ta ce
Chapter 18 · 0% Book details