← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 46

Sashe 37

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_21_

A hankali Jawad ya zame hannayenta a jikinshi ya juya yana kallanta ya ce "And why are u crying?" Ba tare data kalleshi ba ta ce "Naga kamin fishi ne" ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Shiga mu tafi ya wuce" dan murmushi tayi ganin shima ya mata murmushi, ta zagaya ta bude front seat ta shiga sannan ya tada motar suka bar clinic din, juyowa Jawad yayi yana kallanta ya ce "U didn't wipe your face clearly" turo baki tayi tana kallansa ta ce "Na share mana" murmushi yayi yaci gaba da driving ya ce "Ohk, i called u but u refuse to pick" dan zaro ido tana goge sauran hawayen idanta ta ce "Why did u used the word refuse?" Ya ce "Uhum naga kamar yanzu bakyasan daukan wayana ne" girgiza masa kai tayi ta dan hade rai, ya sakar mata murmushi yana kallanta ya ce "To kiyi hkr, amma meyasa baki daukan wayana?" A hankali ta juyo tana kallansa idanuwanta tap da hawaye, kamar batasan yin magana ta ce "Is not like u think Barrister, jiya Imaan tayi tamin kuka ban kwanta da wuri ba, inaga sanda nayi bacci ka kira, yau ma kuma wayar na hannunta na taho" Ya ce "Ohk, how is she?" Ta ce "Lafiya take" daga haka ta share kwallan idanta. A bakin gate dinsu yayi parking ya jiyo yana kallanta ya ce "I will come back in the night" ta ce "Allah ya kaimu, baza kaga Imaan ba?" Ya ce "No, ina sauri zan koma office ne yanzu, idan nazo anjima zan ganta" ta ce "Thank u" ya ce "Mention not" fita tayi ta daga masa hannu sannan ta shige gate, ya danyi murmushi yaja motar ya wuce.
bayan sallah Magrib aka sallami Yusuf, Daddy yazo ya daukesu suka koma gida, suna isa Ammi ta hada masa ruwan wanka ya shiga yayi, da towel ya fito a kunkuminsa ya zauna bakin gado, Khariyya ta bude kofar dakin ta shigo hannunta rike da fruits salad cikin dan bowl, zaro ido tayi ganinsa a haka ta juya da sauri, ya danyi murmushi ya tashi ya dauko kayansa ya shirya, kwanciya yayi akan gadon ya kunna AC ya limshe idanuwansa. Bude kofar dakin tayi a slowly tana lekawa, ganin ya shirya ta karasa cikin dakin ta zauna a gefensa tana murmushi ta ce "Yaya" ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce "Me zakaci na dafa? na hada maka fruits salad" murmushi yayi yana kallan bowl din ya ce "Thank u, ba sai an dafa komai ba wannan ma ya isa" ta dora hannunta akan goshinsa ta ce "Allah ya sauwake" ya ce "Ameen" daga haka ta ajiye masa bowl din a gefensa. Rafi'ah na zaune a dakinta tana shafa powder kiran Jawad ya shigo wayarta, ta danyi murmushi tayi picking call din, ya ce "Dear" ta ce "Uhm" ya ce "Nazo amma zan shiga mosque, an kira isha" ta ce "Ohk to sai ka idar" ya ce "Alright" katse wayar tayi ta ajiye a gefenta taci gaba da abinda take, sosai tayi mungun kyau sai kamshi take, ta dora dankwalinta sannan tasa hijabi tayi sallah, tana idarwa tayi addu'a ta cire hijab din ta yafa babban veil, call din Jawad ne ya kara shigowa phone dinta, tayi picking hade da sallama, ya ce "I'm done" ta ce "Ohk ka karasa BQ" ya ce "Why not inda muka saba zama?" Ta ce "Akwai sanyi a waje ai kuma da hadiri" ya ce "Ohk to" hanging call din tayi ta fita a dakinta zuwa dakin Ummi, a hankali ta tura kofar dakin ta shiga, suna zaune akan gado ita da Imaan, Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Dama yazo ne?" Ummi ta ce "Waye?" Dago kanta tayi ta kalli Ummi sannan ta ce "Ya Jawad ne" Ummi ta ce "Ohk" mikewa Imaan tayi ta nufeta da gudu ta ce "Fita zakiyi?" Rafi'ah ta kama hannunta suka fita a dakin. Har suka isa BQ Imaan na tambayarta fita zasuyi, bude kofar parlorn tayi suka hada ido dashi, tayi saurin sauke kanta tana murmushi, Imaan ta nufesa da gudu ta dale jikinsa ta ce "I missed u Daddy" ya rungumeta yana kallan Rafi'ah dake tsaye ya ce "How are u beauty?" Ta ce "Fine Daddy" ledan chocolates din daya kawo mata ya mika ya ce "This is yours beauty" tana dariya sosai ta ce "Thank u Daddy" daga haka ta mike a jikinshi tana kallan Rafi'ah ta ce "Bari na nunawa Ummina" daga haka ta fice a parlorn. Kallan Rafi'ah yayi dake tsaye bayan kujera ya ce "Yau a tsaye zamuyi hiran ne?" Ta sauke kanta kasa bata ce komai ba, ya ce "Ko saina daukoki?" Taki kallansa kuma bata ce komai ba, ganin ya taso yasa tayi saurin zagayowa ta zauna akan kujera, ya zauna a gefenta ya ce "Kinyi kyau sosai" silently ta ce "Thank u" ya dan wara ido ganin ring din daya bata ne a hannunta ya ce "Ya maki kyau" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Bayan oversize ka bani sai kwanan nan yamin dai~dai" ya kamo hannunta yana kallan ring din ya ce "Uhm, ai ba laifi bane tinda dama bansan size dinki ba then, amma yanzu duk abinda zan siya ma..." Hannunta tasa ta rufe bakinsa ta ce "Ai naga dai ba kai na gayawa ba Anty Na'ima ne" zame hannunta yayi a bakinsa ya ce "Aita fadamin, kuma dani ake zuwa siyo komai" dan harara ta mishi ta kauda kanta gefe, ya danyi murmushi yana shafa kansa ya ce "Let me ask u something, banasan kuma ki fadamin abinda ba haka bane a zuciyarki" a hankali ta juyo tana kallansa, ya ce "Kinasan ki koma gidan Yusuf?" With shock ta kara kallansa sai kuma ta sauke kanta kasa, ya ce "Talk to me Fatima" fadawa tayi jikinshi ta fashe da kuka, ya bubbuga bayanta ya ce "I didn't ask u to cry, tashi ki fadamin" dago kanta tayi a kirjinshi ta ce "Ni banaso kuma" ya ce "Are u sure?" ta daga masa kai hawaye na sakko mata ta ce "Insha Allah i will finish my whole life with u, I thank God every time because He gave me you, ka sani farinciki a lokacinda bani da kowa, duk da ba laifinsa bane wallahi i can't stay with him anymore" ta kara maida kanta kirjinsa cikin sanyin murya ta ce "I had my heart broken during my first love, But when I think of it....." Kuka sosai ta fashe dashi, yana jin yadda hawayenta ke sauka a jikinshi, ya bubbuga bayanta ya ce "It's ok, ni bance kimin kuka bafa" silently ta ce "My future will be Good with u insha Allah, shima Allah ya bashi wacce zata so shi tsakani da Allah" sai kuma ta dago tana kallansa ta danyi murmushi ta ce "You are my first love and you will certainly be the last". Murmushinsa me yayi ya kara bata light hug ya ce "I luv u more" ta sakar masa murmushi ta matsa a gefensa ta ce "Dama kenan haushina kakeji ko?" Ya wara ido yana kallanta ya ce "No niba haushinki nakeji ba" ta dan turo baki ta ce "Hakane mana" matsowa yayi kusanta ya zaro handkerchief a pocket dinsa ya shiga share mata sauran tears dinta, bayan ya gama goge mata tass ta juyo tana kallansa ta ce "Inasan kamshin perfume din nan" silently ya ce "Nasa maki a kayan auranki ma" tayi saurin rife idanuwanta tana dariya a hankali, murmushi yayi ya mike ya ce "Zan tafi Baby, akwai abinda zanyi sannan kuma gobe karfe 6 zan fita" ta bude fuskarta ta ce "Safe, amma pls Yaya Anty Na'ima ta fada maka maganan da mukai da ita" ya ce "Ehh mana, ta fadamin komai" pillow ta wurga masa ta ce "To wallahi bada kai za'aje siya ba" ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce "Na nawa kuma, har mun gama cika akwatin ma" pillow ta sake jefa masa ta ce "To nayi fishi ma" ya durkusa dai dai fuskarta yana dariya ya ce "Gobe da Yamma zamuje ki gaishe da Mami" ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ya nufi kofa tabi bayansa, har mota ta rakashi tana ta daga masa hannu ya tafi. Washegari Yusuf na zaune a daki bayan yayi breakfast Khairiyya ta shigo, ya dago yana kallanta ya ce "Ina zakije?" Ta ce "Kamar ya?" Ya ce "No naga kinyi kwalliya ne" ta danyi murmushi ta zauna gefensa ta ce "Yaya kasan menene?" Ya ce "Sai kin fada" rife idanuwanta tayi ta ce "Dama fa wanine na hadu dashi a wajen Jamb, he's so kind and humble so shine yace wai zaizo mu gaisa, na bashi address" tinda ta fara magana yake kallanta, ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Kin fasa yin karatun ne kika fara soyayya?" Bude fuskarta tayi ta ce "No ban fasa ba, amma yace wai zaijira na gama" Yusuf ya danja tsaki ya ce "Karya yake, ba namijin da zaice zai jira mace ta gama karatu bayan ba farawa tayi ba kuma nasan babbane" ta ce "Yess he's 33 but yace wallahi zai jirani" ya girgiza kai ya ce "That won't be possible, idan auranki zaiyi ya aureki sai kiyi karatun a gidansa idan kuma ba haka ba ya tafi ya kyaleki" da mamaki take kallansa ganin yadda yaci serious, ta ce "Amma Yaya ni sai nayi aure yanzu, i'm just 17 fa" harara ya dalla mata ya ce "And if u are just 17 what makes u to fall in love with someone" ta dan zaro ido sai kuma ta ce "To ai na kai" ya ce "Aurene baki kai ba kenan?" Ta ce "Uhm" mikewa tayi jin wayarta na ringing a dakinta, ta dan kalleshi ta ce "Amma pls Yaya karka gayawa Ammi, yau ne first day da zamu hadu kuma na kasa gaya mata" ya ce "Baza taji ba" daga haka ta juya tana murmushi ta fita, tana fita ya mike ya wuce parlor ya kulle kofar da key sannan yasa key din a pocket dinsa ya dawo ya kwanta, hanging wayar tayi ta yafa dan karamin veil dinta sannan ta fito a daki, leka dakin Yusuf tayi ta ce "Yaya saina dawo" ya daga mata kai yana murmushi ya ce "My regards to him" daga haka ta juya ta koma parlor, murda handle din tayi amma taji a rufe, ta duba taga ba sakata key ne, kamar zatai kuka ta koma dakin Yusuf ta ce "Dan Allah ka bani key din Yaya" ya ce "Key din me?" Ta ce "Na kofar parlor" ya ce "To bansan inda yake ba" ta tsaya tana kallansa irin na rashin yardar nan ta ce "Wallahi kaine ka rufe" ya mike tsaye yana kallanta ya ce "May be Ammi ce ta rife" ta kalli wayarta dake ringing ta ce "Na shiga 3 Ammi dake bacci kuma Yaya, daga nifa sai kaine Ya Sameer baya nan" ya ce "May b taji kina fada" ta durkusa a kasa tana hawaye ta ce "Yanzu ni mezance masa Yaya" ya ce "Bani wayar" ya kar6a wayar ya bar wajen ya koma parlor, picking call din yayi ya kai kunne, mutumin ya ce "Baby" Yusuf ya ce "U pls stay away from my wife, wani satin za tai aure sbd haka ka kyaleta karka sake kiranta, if not duk abinda ya faru fa kai is your fault" bai jira yaji abinda zaice ba yayi hanging call din ya koma daki, a zaune ya sameta akan carpet tana ta share hawaye, ya ce "Na bashi hkr" ta ce "Da gaske, ya kuma hakura?" ya daga mata kai ya ce "Ehh" bell sukaji an danna Yusuf ya mike ya fita parlor yaga ta biyo bayansa, juyawa yayi ya ce "Daukomin wayana a daki" ta ce "To waye Yaya?" Muryar Daddy sukaji yana fadin "Open the door Fatima" da sauri ta ce "Bari na tashi Ammi ta bani key di..." Ganin Yusuf ya zaro key a pocket dinsa yasa ta saki baki tana kallansa, bude kofar yayi Daddy ya shigo, Yusuf yayi kasa da kansa ya ce "Sannu da dawowa Daddy, ina kwana" Daddy ya ce "Lafiya Yusuf, naje morning meeting ne kana bacci" ya ce "Sannu da dawowa" kallan Khairiyya Daddy yayi ya ce "What's wrong with u?"
Chapter 37 · 0% Book details