← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 46

Sashe 29

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

_08103810398_

*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_16_

A hankali Khairiyya ta dago ta kalleshi kafin ta ce "Zan gaishesa idan na shiga" Jawad ya shafa beards dinsa yana kallanta ya ce "Promise" ta daga masa kai daga haka ta juya ta koma ciki. A kan gado Ammi ta sameshi ya dora Imaan a cinyarshi, ta zauna bakin gado tana kallansu ta ce "Gobe insha Allah zamu fara zama a kotu" yayi kasa da kansa yana rike da Imaan ya ce "Allah ya kaimu" shiru ne ya biyo baya sai karan game din da Imaan keyi in a low volume, Ammi ta sake kallansa ta ce "Yaushe zaka maida musu da yarinyar?" sai lokacin ya dago kansa ya kalle ta ya ce "Gobe insha Allah but..." Shiru yayi ya kara sauke kansa kasa, Ammi ta ce "But what?" Da kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce "They're giving me my daughter Ammi" murmushi ta danyi ta ce "Why? Meyasa baza ta zauna inda ta saba ba" ya limshe idanuwansa ya ce "Zamu koma gidana tare, i don't think zan iya zama babu ita" Ammi dake kallansa ta ce "All these years da kai spending baka nan kasan da ita ne? Kaga karka sake jawomin wani rigimar Yusuf, ka barta kawai ta xauna da mahaifiyarta, sai dai kuma idan ita da Fatiman zasu koma gidanka" da sauri ya juyo yana kallanta ya ce "I don't think so Ammi, ita din dai ita ce mallakina so i'm going with her no matter how" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce "Allah ya za6a mana abinda yafi alkhairi, that's all my wish" a hankali ya gyarawa Imaan zama a cinyarsa ya ce "Ameen" Ammi ta mike ta nufi hanyar fita ta ce "Bari a kawo maka abinci" daga haka ta fita ta rife masa kofar, dakin Khairiyya ta shiga ta sameta zaune akan gado tana danna waya, Ammi ta ce "Are u done with the food?" Ta ce "Yes" Ammi ta ce "Sai ki kaiwa Yayanku" hade rai tayi ta ce "Nafa daura akan dinning Ammi, kuma yanzu 7 minutes past 12 ai lokacin lunch bai yi ba" Ammi ta dalla mata harara ta ce "Ai inada hannu ba sai na kai masa ba" daga haka ta juya, da sauri Khairiyya ta sauko akan gadon tabi bayanta, a wajen dinning ta samu Ammi zata dauki warmer tayi saurin riketa ta ce "Pls Ammi ki kawo zan kai" Ammi ta mika mata ta ce "Rashin hankali ne banaso, ba sai nayi da kaina ba wani abu ne" dan 6ata rai tayi ta nufi dakin Sameer da Yusuf ke ciki, ciki ciki tayi sallama ta ajiye warmer din a kasa ta juya ta fito, ta dauki dan karamin warmer da miyar ke ciki sai cabbage da cucumber cikin wani dan bowl shima ta kai, sake fitowa tayi ta dauki serving spoon guda 2 da spoon sai table water da plate hade da cup, duk akan plate din ta dora sannan ta koma dakin ta ajiye masa, har ta juya zata fita ya ce "Khairi" ta hade rai ta juyo tana kallansa ya ce "I need to talk to u" dawowa tayi ta tsaya caan gefe, ya ce "Zoki zauna" ta dan kalleshi sannan ta wuce ta zauna ganin kallan daya ke mata, ya ce "Mena miki da bakya kulani, or do u think saboda kin girma yanzu sai ki daina gaishe da mutane" tayi saurin saukar da kanta kasa ta ce "No" ya ce "To menene?" nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa, ya ce "Idan ba zaki magana ba u can go" share hawayen daya gangaro mata tayi ta ce "I'm seeing what u did to Anty Fatima up till now, anytime i saw u, or i heard ur voice inajin ba dadi, that's why banasan na ganka, i feel hurt deep down me" kallanta kawai yake baice komai ba, caan ya sauke ajiyar xuciya ya ce "After mun gama da court i will apologize insha Allah" da sauri ta juyo ta ce "Bana tinanin zata yafe maka Yaya" ya ce "I don't care, as far as ba laifina bane babu abinda zai dameni, koba laifina i will still apologize saboda Imaan, after all zan kar6i yarinyana suje suyi auransu" Khairiyya ta sake kallansa ta ce "Ai an kusa dama, baifi 2 months ba" ya mike yana gyarawa Imaan zama ya ce "Allah ya sanya alkhairi" daga haka ya nufi toilet yana nade hannun rigarsa, juyowa yayi yana kallanta ya ce "Zanyi alwala ne" daga haka ta mike ta fita a dakin tana share sauran hawayenta.
Karfe 1 Rafi'ah ta dawo daga exams dinta ta samu Mummy ta tafi, duk ji tayi babu dadi gidan, ta wuce dakinta tayi wanka tayi sallah sannan ta sauko downstairs, abincinma kansa kasa ci tayi, ganin phone dinta na haske yasa ta jawo wayar tana kallan screen din, da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi picking tayi shiru, on the orther side Jawad yayi sallama cikin cool voice, dan ta6e baki tayi sannan ta amsa, ya ce "After 26 miseed calls sai yanzu kika dauki wayana" nan da nan idanta ya cika da hawaye, ya ce "Ina waje" ta share hawayen daya sakko mata da bayan hannunta ta ce "I'm coming" daga haka tayi hanging call din, mikewa tayi ta xura hijabi sannan ta fita a parlorn, tana fita gate ya bude back seat yana kallanta ya ce "Bismillah" kamar iska zata dagata ta karasa inda yake ya ce "U come in" daga haka ya matsa mata ta shigo ta rife kofar, rife fuskarta tayi da hijabin jikinta ta ce "Where is my daughter Barrister?" daga haka ta fashe da kuka, Jawad dake kallanta ya danyi murmushi ya ce "Is that what makes u not to pick my calls?" Bude fuskarta tayi hawaye na sakko mata ta ce "Ai is all your fault, ka bari ya tafimin da yarinyana" Ta karashe maganar tana turo baki, ya kamo hannunta cikin rarrashi ya ce "Is not my fault sweetheart, na barta wajen Abba ne bayan DPO yayi kirana, i don't know how he managed to go with her" ta fara bubbuga kafa with serious ta ce "Allah saiya bani Imaan dina, ai ba shiya haifamin ita ba, ko yasan wahalan dana sha na haifeta ne" daga haka ta kara fashewa da kuka, rungumeta Jawad yayi unexpected, ya bubbuga bayanta ya ce "U stop crying love, ki barta a wajenshi ki gama exams dinki peacefully" ta dago kanta a kirjinsa hawaye na sakko mata ta ce "Did u said peacefully?" Ya ce "Yes" ta ce "Ni rashin ganinta shine yake sani kuka inajin ba dadi, kuma ai naga gobe zan gama exams din" kallan lips dinta yake dake motsi a hankali kamar ba magana take ba, ya ce "Nasan gobe zaki gama, sai kuma ki bari idan an gama zaman court sai ya baki idan har ya yarda, kinsan shine yake da iko a kanta bake ba" kuka ta sake fashewa da shi ta ce "After all i gone through sabida shi, wallahi bazan yarda ba, da kaina zanje na dauko yarinya na" jin bakinshi kawai tayi akan lips dinta, tayi shiru zuciyarta na bugawa da karfi, da sauri taja baya tana kallansa ta ce "Ni banaso" ya danyi murmushi yana shafa gashinsa ya sauke kansa kasa, wani mungun kunyarta yaji lokaci daya, ta ce "Pls help me and get my daughter back" jin yayi shiru ta kifa kanta jikin kujera tana share idanta ta ce "Pls Barrister i can't do without her, bata da mahaifin daya wuce kai wallahi, nina baka Imaan har abada" sai a lokacin ya dan kalleta yayi murmushi ya ce "Kin ta6a ganin anyi kyautar diya da ubanta?" Ta turo baki ta ce "Ni dai na baka" hannunta duka biyu ya kamo yana kallan cute face dinta data 6aci da hawaye ya ce "Let him go with her Fatima, wallahi court shi zata bawa yarinyar nan, sai dai kuma idan ta sameshi da wani hali wanda zai iya 6ata tarbiyyar Imaan, shine kadai abinda zaisa a baki ita" kwace hannayenta tayi ta fara rera kuka, ya matso gefenta ya bata light side hug ya ce "Bakya sona kenan?" Ta dago da sauri tana kallansa zuciyarta na bugawa, ya ce "Idan kina sona to ki yarda mu bashi Imaan, i promise u 2 weeks after our weeding zamu samo baby" ta dan wara ido tana kallansa saam bata manta da hawalan da tasha a cikin Imaan ba, ta maida kanta gefe, ya ce "Are u with me love, ko bakya so?" ta kara kauda kanta gefe bata ce komai ba, Jawad ya ce "Karfe nawa gobe zaki gama exams din?" Ta ce "12" ya ce "Alright zan dauko ki and we are going straight to the court" ta juyo tana kallansa kamar xata kara fashewa da kuka ta ce "I'm scared Barrister, banasan kallan Doctor again" murmushinsa me kyau yayi ya ce "Ba sai ki kauda kanki ba" ya kara kamo hannunta cikin rarrashi ya ce "Don't be scared Fatima, inaso ki zama barrister kema, idan kina tsoro ai bazaki iya ba" ta sauke kanta kasa ta zame hannunta a hankali ta ce "Ohk, kuma bazan dawo gida ba" ya ce "Ehh, kafin ki gama kowa yaje" ta dan 6ata fuska ta ce "My Imaan" ya ce "Goben zaki ganta ai" ta share dan guntun hawayenta ta ce "Kuma bata da kaya ko daya ma" Jawad ya kashe mata ido daya ya ce "Zai siya mata ai" ta turo baki ta bude kofar motar zata fita ta ce "Zaka zo da daddare?" Ya ce "Sure, insha Allah" ta danyi murmushi bayan ta fita ta ce "Kuma kayi kyau sosai" daga haka ta rife fuskarta ta juya ta shige gida ya bita da kallo yana murmushi, fitowa yayi a back seat ya koma gaba ya kunna motar ya bar layin.
Anty Amina ce zaune a parlorn gidansu ta buga uban tagumi, Anty Rahama ta kalleta da kyau ta ce "Ba zakije gidan Ikleeman ba?" Anty Amina ta girgiza kai ta ce "Bazanje ba" Anty Rahama ta saki baki tana kallanta ta ce "Zaki kashe kanki fa Amina, kawai daga ji Yusuf ya dawo kin bi kin daga hankalinki, ni wallahi Jawad dinma shiri nake na kada shi yace ya fasa" Anty Amina ta juyo tana kallanta ta ce "Ai tinda ya dawo nasan asirin Khadija ya karye, kuma ni bani da numbernta bare na kirata, ni tinda Ya Muhammad yace min Yusuf ya dawo naji ba dadi, kuma bansan meyasa ba da fargaba nake kwana, karfa asirinmu ya toni Anty" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "To sai me? Ai wallahi ko kama su akayi tace dasa hannunmu koda rantsuwa sai mun kwaci kanmu, tinda dama sun nuna basanmu suke ba, kinga ko munce karya suke yarda za'a yi" Anty Amina ta ce "Kuma hakane, Amma jikina yana bani wani abu yana faruwa, tin bayan dawowar Abban Rafi'ah da nace zanzo gida ya barni, kinga yau kwanana 3 baice na koma ba, sai waya, kuma innace akwai abinda yake faruwa sai yace babu, abun daya fadamin shine Rafi'ah ba lafiya kuma Yusuf ya dawo" Umma dake kwance tana jinsu tayi murmushi ta ce "Yoo dama dole tayi ciwo mana, balle ma ga ciwan da yake daminta ai dole ya tashi idan taga bawan Allah nan, ki dai kwantar da hankalinki a gama komai caan ki koma gidan mijinki" Anty Rahama ta ce "Ai bazan bari tayi auran jin dadi ba, wallahi koda ta auri Jawad dinma sai ta fito, saina san yadda nayi ta kara fitowa" Anty Amina tayi murmushi kawai tana danna wayarta.
Chapter 29 · 0% Book details