← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 46

Sashe 22

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 1 da 'yan mintuna su Yusuf suka iso Kano, bayan an fitar musu da kayansu ya tare napeep a cikin park din, kamar bayasan yin magana ya ce "Sharada" mai taxi din ya ce "To bismillah Alhaji" Yusuf ya bude back seat ya shiga, Jiddah dake tsaye a gefe ta ce "Malam ga kaya fa" mai taxi din ya fito ya dauki trolley dinsu yasa a boot, sannan ya dawo ya kunna motar, kallan Yusuf tayi daya jingina da kujera ya limshe ido, tinda suka taso a Kaduna ko magana ba suyi ba har yanzu, ta danja tsaki a hankali ta dauke idanta a kansa, tafiyar minti 10 sukayi suka iso dai~dai gate din gidansa, bayan anyi parking Jiddah ta dan kalleshi ganin ya bude ido, bude motar yayi ya fito ya tura gate din yaji a rufe, ya juyo yana kallan Jiddah a takaice ya ce "Key?" Ta bude hannayenta alaman itama bata sani ba, Yusuf ya sauke ajiyar zuciya ya kara juyawa yana kallan padlock din dake jikin kofar, mai taxi din ya kalleshi ya ce "Yallaboi ko ana bukatar taimako?" Yusuf ya ce "Makulli nakeso wanda zai bude wannan kwadon" mai taxi din ya ce "To bari na kar6o a nan bakin titi" Yusuf ya kalli Jiddah dake tsaye tayi folding hannayenta ya ce "Ki bashi kudi" ta ciro 1k ta mikawa mai taxi din, mota ya koma ya kunna yana kallan Yusuf ya ce "Saina dawo" daga haka ya wuce, Jiddah ta juyo tana kallansa ta ce "What if he run away?" Yusuf ya kafeta da ido bai dai ce komai ba, kamar daga sam taji ya ce "Kansa yayi wa" ta juyo tana kallansa amma sai yayi kamar ba shi yayi maganar ba. Sun kusan minti 7 sai gashi ya dawo da key har iri buyu, ya fito yana kallan Yusuf ya ce "A cikin daya zamu dace insha Allah, hala kun manta naku makullin ne" Yusuf ya ce "Ehh" ana gwada na farko kuwa padlock din ya bude, Yusuf ya dan kalli Jiddah ya ce "Give him another 1k" daga haka ya kalli mutumin ya ce "Nagode" yaja trolley dinsa ya shiga ciki bayan mutumin yayi masa godiya, kamar bayasan taka kasa ya nufi entrance din gidan, ga wani jiri dake shirin dibarsa, shi dai kawai tafiya yake, tin daga tsakar gidan zaka gane anyi shekaru ba mutane a gidan, saboda duk datti ne ta ko ina, ga ganyen flowers din gidan da suka bushe sun zubo kasa. Yana murda handle din kofar parlor yaji a bude, ya bude ya shiga yana karewa parlorn kallo, ta ko ina kurane tin daga kan kujerunsa TV stand, TV, center table da kuma tiles din, ya nufi part din Rafi'ah ya samu ba komai aciki, sai kura a kasan tiles din, ya karasa dakunan ma ya leka, ko labule babu a ciki, hannunsa yasa ya share hawayen daya gangaro a idansa, ya tabbata kenan dai ya saki Rafi'ah kamar yadda yake tinawa, ya cije lips dinsa still hawaye na sakko masa ya fita a part din ya bude na Jiddah, itakam komai nata yana nan yadda suka barshi, wani abin ma kura ta lullubeshi, ya juya ya fito a hankali kamar bayasan taka kasa, yana fitowa parlornsa ya zauna akan 3 seater saboda jiri dake shirin jefar dashi, Jiddah da shigowanta kenan tabi shi da kallo, gaba daya ya 6ata farin kayansa dake jikinsa, caan bakin kofa ta tsaya tana karewa parlorn kallo, bayan minti 10 ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To yanzu a cikin kurar nan zamu kwanta yaya?" Bude idanuwansa yayi ya kalleta, yayi shiru yana tinanin taya zai fara zuwa gidan Ammi, da wani ido zai kalleta, mai zaice mata Rafi'ah tayi masa ya saketa? Maiyasa bai nemeta ba all this while? Sauke ajiyar zuciya yayi Jiddah ta ce "Doctor magana fa nake maka" ya kara dago kansa ya kalleta, ta ce "A haka zamu zauna dust everywhere?" A hankali ya ce "Ki gyara nan parlorn ki zauna" da mamaki ta ce "Bayan ina dauke da cikinka sannan kace nayi wannan uban gyaran ga kura, mutuwa zanyi kenan?" mikewa yayi gently ya ce "Then kije gidanku, duk ranar da zaki iya gyaran gidan sai ki dawo, i'm leaving too, dama na biyo nan ne na huta in other not to stress my heart again, tinda na samu relief tafiya zanyi" da mamaki ta ce "Ina zakaje to?" bai kalli inda take ba ya mike yana jaan trolley dinsa ya fita a parlorn ta bishi da harara. Umma ce zaune cikin cell ita da Anty Khadija dake faman kuka, babu abinda yake damunta sai rashin zuwa wajen bokan nan da tayi, tasan yanzu ko ta yaya Yusuf kokari zaiyi ya dawo gida, sauke ajiyar zuciya Umma tayi ta ce "Gaskiya bamu ta6a shiga kunci irin na yau ba, kema sai da nace karkije inda za'a ganki amma kika fita, yanzu ga shi nan kotu za'a turamu mu shiga 3" Anty Khadija ta kamo hannun Ummanta ta ce "Abin takaicin bai wuce dawowar Yusuf ba, wallahi Umma ko shekara 10 zanyi anan indai Yusuf zai shiga duniya ba damuwata bane, kuma na fito a hotel zan hau Napeep na tafi tasha kawai naga Alhaji Usman da matarsa, naso guduwa amma ya taramin jama'a Umma, mutane nata zagina haka aka taso keyata har nan, amma duk abin nan daya faru gara ninkinsa ya faru da Yusuf ya dawo" ta kifa kanta akan cinyar Umma tana kuka ciki ciki, Umma ta ce "Ai zamu fita ina nan dake sai na kadashi duniya" jin an shigo yasa Anty Khadija ba tai magana ba, dan sandan ya tsaya yana kallansu ya ce "Ance ku kira mutum daya cikin 'yan uwanku saboda jibi zaku fara zama a kotu, shi zai wakilce ku da wani abin daya kamata" Anty Khadija ta kalli Umma ta ce "Kawu na mararraba za'a kira ko?" Umma ta hade rai ta ce "Allah ya kiyaye wallahi, mutumin daya cimun mutunci gabanki rannan, wallahi gara nayi hayan dan uwa na kawo" Dan sandan dake kallanta ya jefa musu waya daya daga cikin wayoyi uku da suka kwace a hannunsu yayi tafiyarsa, Anty Khadija ta share hawayen idanta ta ce "Na shiga 3,yanzu fa idan asirinmu ya toni duk wasu manyan mutane da nake mingling dasu zasu gujeni, a gujeni wajen aiki, a gujeni a ko ina ma" fashewa tayi da kuka ta ce "Ga Yusuf na dab da bayyana Umma, nasan da an sallameshi zai dawo gida, Allah yasa ya rasa komai nasa a rayuwa, Allah yasa tayi aure mijinta ya kulleshi, ita kuma Jiddah data mareki Allah ne kadai zai rabani da ita wallahi" Umma ta ce "To ga shawara, ba sai mu kira Yusuf din muce masa gamu station ba, kinga yana zuwa zaiyi komai a gama, muna fita kuwa sai kauyen Marke mu kara kada shi" Anty Khadija ta ce "Kina ga zai zo?" Umma ta ce "Sai dai banyi kuka ba, amma muddin na nuna masa ina cikin tashin hankali zuwa zaiyi, kinga ba zai samu kwanciyar hankalin zuwa gidan kanwar uwarsa ba, nan zai taho direct" Dai dai kofar gidan Ammi aka sauke shi, ya zira hannu a aljihunsa ya ciro 100 naira daya gani dazu, ya mikawa mai Napeep din sannan ya tura kofar gate din ya shiga, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, da kyar yake takawa saboda yadda yakeji, a balcony ya sake trolley din ya fadi, ya murda handle din kofar ya shiga ciki, Ammi na zaune akan sallaya ta idar da sallan la'asar, ta juyo da sauri dan tinaninta Khairiyya ce ta shigo, Yusuf ta gani tsaye hawaye sun wanke masa fuska, ta zabura ta mike tana kallansa ta ce "Yusuf, is that really you?" Sai kuma ta fashe da kuka, a daddafe ya karasa inda take ya rungumeta sosai yana kuka ya ce "It's me Ammina, ki yafemin dan Allah bansan meya faru dani ba Ammi, i left without u knowing, i divorced my beloved wife, i lost my job, na rabu da duk masoyana na koma caan wani waje na kafa saban rayuwa, dan girman Allah ki yafemin it wasn't intentional Ammina, i have no one but u, kece komaina Ammi dan Allah ki gafarfeni kimin rai ko zan samu saukin abinda nakeji" Ammi kam banda kuka ba abinda take, jin ya sake jikinsa yana shirin faduwa yasa ta rikoshi da sauri tana jijjigashi amma ina ya sume a hannunta, anan tsakiyar parlorn ta kwantar da shi, ta dauka bottle water dake kan dinning ta zuba masa a fuska, yayi wata ajiyar zuciya ya bude idanuwansa da suka ciko da hawaye, Ammi ta dagoshi cikin tashin hankali ta kira Daddyn Sameer a waya ta fada masa abinda ke faruwa sannan ta katse wayar tana rungume da Yusuf still tana kuka tana kara godewa Allah hade da masa addu'a. *_2 hours ltr_* Kwance yake akan gadon Ammi, Sameer na rike da hannunsa yana masa sannu, Yusuf ya daga masa kai kawai yana kallan Ammi dake share hawaye har lokacin, a hankali Sameer ya ce "Zaka tashi ne" Yusuf ya daga masa kai, Sameer ya taimaka masa ya tashi zaune, zira kafafuwansa yayi kasa yana kallan Ammi ya kamo hannunta cikin sanyayyar murya ya ce "I know it's hurt Ammi, nasan nayi abinda ko a mafarki bakiyi tinani ba, Ammi ban tafi dan nayi rayuwa me dadi ba wallahi, ban gujeku dan bana sanku ba, no one loves u more than i did Ammi, bansan meyasa na tafi ba, i left my wife crying na tafi na barta cikin amai, wallahi Ammi it wasn't intentional, kin fitar da hawaye a kaina yafi a kirga, dan Allah kice kin yafemin Ammi" rungumeshi Ammi tayi tana share idanta ta ce "U never hurt Yusuf, nasan ba laifinka bane, nasan dole watarana zaka dawo indai kana raye, ai addu'ar iyaye bata faduwa banza" hawayen idansa ya share yana kallan Sameer dake hawaye shima, Daddy ya karaso yana masa sannu, Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Ammi ta mike ta fita a dakin Daddy yabi bayanta, a parlor ya sameta tana zaune tana share hawayen dake gangarowa a idanta, ya ce "Aisha ai sai mu godewa Allah daya bayyana shi" Ammi ta
Chapter 22 · 0% Book details