← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 46

Sashe 6

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaye suke duk tasu a kofar room din da Rafi'ah ke ciki, kana ganinsu kasan suna cikin babban tashin hankali, musamman Ummi data kasa controlling tears dinta, tausayin Rafi'ah kawai take idan ta tuno azabar haihuwa, Mummy dai na jingine da pillers din wajen ta limshe idanuwanta, banda salatin Rafi'ah da kiran Ummi da take ba abinda su ke jiyowa, Abba dai na tsaye yana ta addu'a sai kaiwa yake yana kawowa a area din wajen, bayan few minutes Dr Hisham ya fito a room din, Ummi ta mike da sauri tana kallansa ta ce "How is she Dr?" Ya ce "Alhamdulilah kenan, amma gaskiya ba zata iya haihuwa da kanta ba, zamuyi mata CS but sai mijinta yayi signing" Ummi ta share hawayen idanta ta zauna, Abba ya ce "Let me sign Dr" Dr Hisham ya girgiza kai yana kallan Abba ya ce "U can't sign both yallaboi, mijinta zai fara signing sai kuma kai" a fusace Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Wane irin miji kake magana bayan ga mahaifinta nan, shekara nawa ana kawota asibitin nan kunfi kowa sanin danginta, mijin da shekara daya ba'a san inda yake ba, idan baza kuyi abinda ya dace ba mu kaita wani asibiti mana" sauke idansa Dr Hisham yayi ya ce "Kiyi hakuri Madam, rules din aiki ne ba wai nina fada ba" daga haka ya kalli Abba ya ce "Muje sai kayi signing din" daga haka Abba yabi bayansa zuwa office, cikin 20 minutes aka gama komai aka shiryata, ko magana bata iya yi sai kallon Ummi da take hawaye na sakko mata har aka turata cikin dakin. gaba daya jikinsu ya gama sanyi musamman Ummi da hawaye ya ki daina sakko mata, addu'a babu irin wacce batayi.
Kusan 1 and half hour suna tsaye a wajen sannan Dr. Hisham ya fito, Abba ya kura masa ido yana kallansa, ya danyi murmushi yana kallan Abba ya ce "It was successful Sir, an samu cute baby girl" ajiyar zuciya suka sauke, a tare duk suka amsa da Alhamdulilah, Abba ya ce "Can we see her?" Ya ce "Not yet, za a mata allura ne bayan awa daya zata tashi, but u can see the baby, zasu kawo muku ita soon" daga haka ya wuce office dinsa yana cire hand gloves din hannunsa. Kafin a fito da Baby Mummy ta yiwa mutane sunfi 30 waya cewa tayi jika, bayan minti 10 nurse din ta fito da Baby a hannunta, sai kamshi take saboda yadda aka gyarata sosai, Ummi tayi saurin mikewa ta kar6eta sannan ta bude fuskar Babyn dake rufe da towel, sai da zuciyarta ya tsinke ganin kamannin Yusuf karara, ta sauke ajiyar zuciya ta mikawa Abba Babyn, shima same thing abinda ya gani, ya danyi murmushi ya kai bakinshi saitin kunnen Babyn ya mata kiran sallah hade da addu'a, hanging wayar Mummy tayi ta kar6a Babyn tana murmushi ta ce "Gata kamar shashashan ubanta kuwa" Abba dai ya kalli Ummi ya ce "Bari naje sallah na dawo" ta ce "Safe" Mummy ta ta6e baki ta ce "Wallahi da ana canza halitta dana canza miki kamannin Yusuf, dan bai kamata ki dauko kamarsa ba, baki sanshi ba bai sanki ba, banda ma hukunci na Allah taya zakiyi kama da Yusuf, uban me ya tsinana miki a rayuwa" goge dan hawayen idanta tayi ta ce "Allah ya taimakeshi watarana yazo yana kirarin shine mahaifinki, wallahi saina yaga masa rigar rashin mutunci, sai ya kwammace bai sanni a rayuwa ba, balle dangi na" Ummi dai bata ce komai ba, tasa tissue ta goge hawayen daya ke kokarin gangaro mata. Dakin da Rafi'ah take kwance suka shiga, bacci take sosai banda numfashi babu abinda take saukewa, Ummi ta kamo hannunta tana kallanta ta ce "Allah ya baki lpy daughter" Mummy ta ajiye Babyn a gadonta ta zauna gefen Rafi'ah tana mata addu'a. Kafin ta tashi mutane sunzo ganin Baby, makwabtan Mummy da Ummi sai kuma friends din Ummi, Anty Amina da 'yan gidansu sai daga baya suka zo, Ammi kam ita ce farkon zuwa ita da Sameer, Mami ma tazo sai murmushi take tana yaba kyan yarinyar kamar da gaske, duk da itama batasan Yusuf sosai ba amma taga kamanninsa da Babyn, Sameer dai ya dinga kallan Babyn dake kwance tana bacci, bayan 5 minutes Rafi'ah ta fara motsa karfarta, duk occupants din dakin suka dawo kallonta, ta fara bude ido a hankali tana salati, Ummi ta mike tana kallanta ta ce "Rafi'ah" kokarin tashi take amma ta kasa, Mummy ta dagata ta zauna ta ce "Sannu, kinajin ciwo ne?" A hankali ta nuna mata dai dai inda aka mata surgery din, Mummy ta ce "Sannu" limshe idanuwanta tayi ta budesu, sannan ta fara bin katon dakin da kallo, kowa na dakin take kalla amma bata ga Jawad ba, he once told her that duk lokacin data haihu tana bude idanta zata ganshi a gefe, but he is absent now, suna hada ido da Mami tayi saurin kawar da kanta gefe, the same thing daya faru lokacin data kalli Umman su Anty Amina, Ikleemah na zaune kan carpet tana ta danna phone dinta, jin Mummy ta ta6a ta yasa hankalinta ya dawo waje daya, ta sauke ajiyar zuciya kawai, Mummy ta ce "U didn't ask for ur Baby daughter" sauke kanta ta kara yi tana wasa da ring din hannunta, Mummy ta ce "Bari na dauko miki ita" kan gadon Babyn ta koma ta dauko Babyn, sai kallon towel din da Babyn ke ciki take, Mummy ta mika mata ita ta ce "Congratulation for having her, Allah ya kare miki ita daga sharrin masu sharri" zaro ido Rafi'ah tayi ganin fuskar Babyn, her eyes, lips, the fair skin, nose gaba daya is exact as Yusuf's own, fashewa tayi ta kuka ta rungume Babyn a jikinta kam kam tana fadin "Why didn't u resemble me Habibty, i was the one who take care of u since from the day i got u, i suffered for 9 months, i cried several times because of u dear, isn't all this a prove to resemble me dear? bana bacci da kyau, bana ci da kyau just because of u, meyasa ni baki yi kama dani ba" share hawayenta tayi ta kara kurawa Babyn ido, sai kuma ta kara rungumeta ta ce "Anywhere, i luv u Habeebty, ba wanda zai miki irin son da zan maki a duniya, i still remain ur mum and Dad, nice komai naki a rayuwa, if anyone's to blame, he's mistaken dear, i'm only yours, ke tawa ce ni kadai na, i luv u Habeebty" ta kara rungumeta tana kuka sosai da sosai, duk jikin mutanen dakin sai yayi sanyi, musamman Ammi data kasa tsayuwa sai ficewa tayi a dakin.

_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_4_
Chapter 6 · 0% Book details