← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 46

Sashe 16

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Dai~dai bakin gate yayi parking ya juyo yana kallanta ya ce "U come down" ta dan turo baki ta ce "Kai zaka budemin" Jawad yayi murmushi yana kallanta ya ce "An gama Madam" daga haka ya fito ya zagayo ya bude mata ya ce "Ur wish is my command Baby" fitowa tayi a motor tana dariya zata rife kofar ya ce "Wait! Bari na karasa ladana" daga haka ya tura kofar motar ya rife, a tare suka jera suka shiga gidan, sai da suka kusa balcony ta dan ja baya ya wuce gaba sannan tabi bayansa, ya murda kofar parlorn ya shiga da sallama, Imaan najin muryarsa ta sauko a kan dinning da gudu ta nufeshi, ya dagata sama yana dariya ya ce "Is this my Imaan?" Ta washe masa baki ta ce "Yess Daddy, where have u been?" Ya bata light kiss ya ce "Momma bata ce miki nayi tafiya ba?" Imaan ta girgiza kai tana kallan Rafi'ah dake zaune kan sofa tana danna wayarta, Jawad ya juyo yana kallanta ya ce "Why Momma?" bata ko kalli inda yake ba ta ce "Ai nima saida ka tafi ka kirani" fitowa Mummy tayi a kitchen tana kallansu ta ce "Ha'a yana ganku tare?" Ya ce "Ita na fara daukowa, Ina wuni" ta ce "Lafiya kalau, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulillah" daga haka ya daura Imaan akan shoulder dinsa ya ce "Let me see Mami" ganin ya nufi part dinsu yasa Rafi'ah ta tashi tabi bayansa a hankali, da sallama ya shiga parlorn yana kallan Ikraam dake zaune tana kallo, ta mike zaune tana kallansu, sai kuma ta dan daure fuska ganin Rafi'ah ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Sannu" zama yayi akan kujera yana kallanta ganin taci gaba da canja channel ya ce "Ke" ta juyo tana kallansa, ya ce "Did u great her?" dan turo baki tayi ta ce"Who?" Ya ce "Your Aunt" kanta ta maida gefe kamar baza tai magana ba, sai kuma ta ce "Ina wuni" ba tare da Rafi'ah ta kalleta ba ta ce "Same" Jawad ya ce "Let's go inside Fatima" Rafi'ah ta mike ta ce "Ohk" daga haka tabi bayansa suka shiga bedroom din Mami. A tsaye take tana shirya gogaggun kayanta cikin press, da sallama suka shigo dakin, ta amsa tana kallan Jawad dake rike da Imaan ta ce "Har ka dawo?" Ya sauke Imaan a wuyansa ya ce "Ehh wallahi, ina wuni Mami" ta ce "Lafiya kalau, ya hanya?" Ya zauna bakin gado ya ce "Alhamdulillah" a kan carpet Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" ba yabo ba fallasa Mami ta ce "Lafiya kalau, ya karatu?" silently ta ce "Lafiya kalau" Mami ta kalli Jawad dake wasa da Imaan ta ce "Akwai abinci akan dinning" ya ce "Thank u, but i want to take my bath first" daga haka ya mike ya nufi hanyar fita, tashi Rafi'ah ma tayi ta ce "Sai anjima Mami" Mami ta ce "Mu jima da yawa" daga haka suka fita a dakin. Suna fita Rafi'ah ta wuce part din Mummy, Jawad ya ajiye Imaan ya ce "Follow ur Momma dear" ta tsaya tana kallansa kafin ta ce "Daddy are u leaving?" Ya ce "No, i want to take my bath sweetheart" hannu ta mika masa suka tafa sannan ta juya ta shiga parlorn Mummy, abinci Rafi'ah taci bayan tayi sallah sannan ta kwanta akan sofa tana kallan cartoon din da Imaan ke kalla, tana nan kwance har bacci ya fara daukanta, lokaci daya taji Imaan na bubbugata, ta bude ido a hankali tana kallan Jawad dake tsaye a bayan kujera, ya daga mata gira daya ya ce "Let's go" ta mike a hankali ta mayar da hijab dinta sannan ta shiga dakin Mummy, a zaune ta sameta tana waya, sai data jira ta gama sannan ta ce "Mummy zamu wuce" ta ce "Ohk daughter, sai yaushe kuma?" ta dan juya ido kafin ta ce "Exams zan fara ai Mummy, duk sanda na gama" Mummy ta ce "Ohk Allah ya kaimu, kin yiwa Mami sallama ne?" Ta girgiza kai ta ce "Yanzu dai" Mummy ta ce "Safe, ita wannan mai surutun fita tayi bako sallama ko?" Rafi'ah ta danyi murmushi ta jawo mata kofa, dan tin tini ta dale bayan Jawad sun fita, tana fitowa main parlor ta nufi part din Mami, ta shiga a hankali hade da sallama, Mami ta dago tana kalleta ta ce "Baku wuce bane?" A sanyaye ta ce "Ehh yanzu zamu tafi, mungode sai anjima" Mami ta ce "Allah ya kiyaye" juyawa Rafi'ah tayi ta fita a part din sabida bata iya hada ido da Mami yanzu, tin abubuwan da suka faru shekaru biyu baya da suka wuce wanda ya kai har Abi ya saketa tayi kusan wata 9 a gida, dan tsaki Ikram tayi ta ce "Mami wai yanzu kin hakura kenan Yayanmu ya auri wannan yarinyar?" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Idan itace matarsa Allah ya sanya alkhairi Ikram, ni dai Allah na gani bana bin boka, nama tsani duk matar da xata kai sunan wata ko wani wajen boka, kina gani yadda na shiga jarabar rayuwa akan hana shi auranta, da kyar na samu nawa auran ya gyaru, saboda haka babu ruwana addu'a kawai zan bisu dashi Allah ya sanya alkhairi, na zagi 'yar mutane bansan ya nawa 'ya'yan zasu tashi ba, na mata sharri kala kala duk dan na cimma burina amma daga karshe Allah bai yi ba, to menene ribata anan Ikram? Allah ya yafe mana gaba daya kuskurene kam nayi shi, na tauyewa Jawad hakkinsa da yawa a rayuwa, badan uwa uwa bace nasan da wuya ya yafemin, amma ko sau daya bai ta6amin abinda zanji ba dadi ba, dan meyasa nima bazan so farincikinsa ba" Mami ta share guntun hawayenta sakamakon tuno baya da tayi, dauke kai Ikram tayi daga kallanta ranta a 6ace ta mike ta shige dakinta, Mami ta bita da harara ta ce "Haryanzu ke yarinya ce Ikram zuwa gaba zaki gane komai, bana fata na cuci wani yanzu balle watarana ya juyo kaina".
one thousand Imaan ta fito dashi a pocket din wandanta tana nunawa Rafi'ah ta ce "Mami gave me this" Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Kince kin gode?" Ta ce "Yes, ko Daddy" Jawad ya shafa kanta ya ce "Exactly" kallan Rafi'ah yayi data maida kanta gefe tana kallon titi ta window, a hankali ya ce "Dear" ta juyo a sanyaye tana kallansa, ya ce "What's wrong with u?" Ta ce "Nothing" cigaba yayi da driving lokaci lokaci yana kallanta ta gefen ido har sukaje gida, a waje yayi parking ta juyo tana kallansa ta ce "Meyasa anan Barrister?" Ya ce "Kinsan na tsani idan ba jimawa zanyi ba na shigar da mota" ta ce "Ohk" daga haka ta fito ta tura gate ta shiga, dauko Imaan Jawad yayi a shoulder dinsa suka shigo, a baya suke bin Rafi'ah har suka shigo parlor, ya ajiye Imaan sannan ya samu waje ya zauna a kan lallausan carpet, fitowan Ummi kenan a parlorn Abba ta tsaya kallansu, saam bata lura da jawad ba, sai da taji muryarsa yana gaisheta, ta saki murmishi ta ce "Lafiya kalau, yaushe ka dawo" ya ce "Dazu, ya aiki" ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta koma parlorn Abba Imaan tabi bayanta, zama Rafi'ah tayi akan sofa tana kallansa ta ce "Me zan kawo maka?" Ya danyi murmushi yana shafa kansa ya ce "You" ta dan harareshi sannan ta mike zata wuce kitchen ya kamo hannunta, ta juyo a hankali tana kallansa ya ce "Kinsan yanzu fa naci abinci, so i'm going" ta ce "Ohk Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen, zakije school gobe?" Ta daga masa kai ta ce "Probably, but u know what Barrister?" Ya kafeta da ido ganin yadda take magana kamar bata sanyi, ya ce "Kina da damuwa Rafi'ah, what's that thing u are thinking of? Tin dazu kike behaving somehow, did anyone hurt u dear?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne yake ciwo, and my chest too, yanzu zan sha magani na kwanta karna samu attack" a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ohk, Allah ya sauwake, ki huta sosai" ta ce "Insha Allah, bye bye and i luv u" a hankali ya matsa kusa da ita tayi saurin sauke kanta kasa, ya bata very light hug ya ce "I luv u too" daga haka ya sake hannunta, daga masa hannu tayi ta ce "Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen" sannan ya fita ya jawo musu kofa ita kuma ta haura upstairs.
Kwance yake a wani daki babba ya kama kansa dake masa mungun ciwo, dakin is well furnished, komai tsaf tsaf a inda yake, hannunsa na dama drip ne a ajiki dayan hannunsa kuma yawo yake tsakanin kirjinsa da kansa, idan yayi minti 2 dafe da kansa sai kuma ya maida kirjinsa ya dafe, mungun zafi zuciyarsa ke masa, gaba daya yayi mungun rama, sai haske daya kara sosai, idan ka kalleshi sau daya ba zaka gane Yusuf bane at once, Anty Khadija ne da Jiddah akansa suna tsaye, bayan 'yan mintuna Anty Khadija ta fito a dakin ta wuce dakin da Umma take, tsaye ta ganta tana ta faman dialing phone din Malaminta, tin jiya da suka dawo Nigeria take ta trying number amma yaki shiga, Umma ta zauna bakin gado cike da damuwa ta ce "Anya mutumin nan bai karya aikin nan ba Khadija? Ki duba fa kiga tin wata daya baya Yusuf baya bin abinda nace masa sosai, yanzu gashi satinsa daya a kwance baya magana sai juyi da yake" Anty Khadija ta karasa wajen Umma ta zauna ta ce "Ba shakka ya karya asirin nan Umma, da bai karya ba taya za'ai Alhaji Usman ya sakeni ya taho ya barni, sannan dama yace idan aka karya masa alkawari abin ba zaiyi kyau ba" Umma ta ce "Toba dole a karya alkawari ba Khadija, taya da auranki zaice ki dinga zuwa yayi lalata dake saboda asara ta mana yawa, anyi wanda akayi a baya amma yanzu kam naga ya isa haka, bazaki kara bashi kanki ba" Cike da damuwa Anty Khadija ta ce "Umma idan ba haka ba zai wargaza min duk wani shirina" Umma ta danyi murmushi ta ce "Ai kudi yana aiki Khadija, yanzu tashi zakiyi, ki dauki driver ki wuce Kano sannan kije kauyan nan ki sameshi, kudade kawai zaki bashi ya gyara komai, kinga ba wanda yasan muna da gida a Kaduna, bayan sati daya idan Yusuf yaji dama dama mu koma Egypt" Anty Khadija ta ce "Hakane Umma, shawara ce me kyau, yanzu bari nayi wanka na shirya, tin jiya da mukai landing nake taya Jiddah daga Yusuf ko wanka banyi ba gashi har kusan magrib" tana fadin haka ta wuce toilet, sai kuma ta juyo ta ce "Umma to a ina zan kwana a kano? kinsan dai ko hauka nake baxanje gidan mu ko gidan Yusuf ba?" Umma ta ce "Ai akwai hotels Khadija, ni dai fatana ki dace, ko nawa ya bukata zamu bashi tinda mu ba matsiyata bane" Anty Khadija tayi murmushi sannan ta shige toilet. A hankali Jiddah ta kamo hannun Yusuf dake saman kirjinsa, ya bude idanuwansa da suka dawo jajir yana kallanta, kuka ta fashe dashi ta rungumeshi ta ce "Pls talk Ya Yusuf, kusan sati daya baka magana dan Allah kace wani abu ko zanji dadi" shi dai kallanta kawai yake yana kwance, ta mike kamar mahaukaciya ta daga masa labule ta ce "Ka gani Yaya, jiya muka dawo Nigeria saboda condition dinka, kuma Umma taki bari a kaika asibiti sai dai a kira Doctor ya duba ka, ka gani Yaya nan Kaduna ne, mun dawo kasar mu" limshe idanuwansa yayi kamar yadda suke dazun, Jiddah ta fashe da kuka ta kara hawa gadon ta rungumeshi sosai ta ce "Nice Jiddan kafa Doctor, nice wacce kake cewa kullum kana sona tin tafiyarmu Egypt, ka manta bakaso kayi nisa dani? dan Allah kayi magana Habibina" bakinshi ya kai saitin kunnenta, har lokacin idanuwansa a limshe suke, ya dora dayan hannunsa da kyar a bayanta, da kyar muryarsa ke fita ya ce "Are u with me Rafi'ah?" Jiddah ta zabura ta mike tana zaro ido, sai kuma ta kwala ihu tana kiran Umma ta ce "Na shiga 3, ya tina ta wallahi Umma, ba Jiddah yace ba wallahi" Umma tayi kansa da sauri tana kallansa, kamar ba shi yayi magana ba, idanuwansa a limshe sai numfashi da yake saukewa daki~daki, number Doctor din daya dubashi daxu Umma ta fara kira, bayan ya dauka ta sanar masa ya tashi yace ga shi nan zuwa, Umma tayi hanging call din ta dago Jiddah zuwa jikinta ta ce "Kiyi shiru, Khadija na komawa komai zai daidaita Jiddah, yanzu haka shiryawa take kinji" muryarsa suka sakeji a hankali ya ce "Fatima" Jiddah ta kara sakin kuka ta ce "Yau na shiga 3 Umma dame zanji, da rashin lafiyarsa koda sunan waccen yarinyar daya ke kira"
Chapter 16 · 0% Book details