Sashe 3
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
sallama, Saudatu dake jera dinner akan dinning ta ce "Ina wuni" ya ce "Lafiya kalau, Ummi na nan?" Ta ce "Ehh bari in mata magana" upstairs ta nufa ta kwankwasa dakin Ummi, bayan an bata izini ta bude dakin ta shiga da sallama, Rafi'ah na kwance akan gado Ummi na rarrashinta, dan wani saban kuka ta kafa musu tinda ta tashi a bacci, Ummi ta kalli Saudatu dake tsaye gefe ta ce "Kin gama abincin ne?" Ta ce "Ehh na gama, kinyi bako ne a kasa" Ummi ta ce "Bako kuma at this time? Babbane?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Ehh babbane, dogo dan fari haka, yana da gashi me yawa a kansa" sosai zuciyar Rafi'ah ya buga, dan tinaninta ko Yusuf ne, ta ruko hannun Ummi kamar zatai kuka ta ce "Dan Allah karkije Ummi" Ummi ta ce "Why Rafi'ah, bari na gani ko waye" daga haka ta zame hannunta ta nufi kofa ta fita, saukowa akan gadon Rafi'ah tayi tana kallan Saudatu ta ce "Fari ne?" Saudatu dake tsaye tana kallanta ta ce "A'a amma dai ba za'a ce masa baki ba" ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta kwanta, dan tasan Yusuf yana daya daga cikin mutanen da za'a kira su asalin farare, a hankali Saudatu ta ce "Allah ya baki lafiya" daga haka ta fice a dakin. Tana saukowa ta sami Jawad da Ummi suna gaisawa yana mata jajen abinda ya faru, Ummi ta danyi murmushi ta ce "Toya zamuyi, haka Allah ya tsara mana, da munsan haka zai faru ko auran baza ai ba, to amma Allah shi yake tsara komai a duk lokacin daya so" Jawad da kansa ke kasa ya ce "Hakane" Ummi ta ce "Bari na turo ta ku gaisa" daga haka ta mike ta wuce upstairs, kwance ta sameta tayi shiru ta kurawa window ido, Ummi ta kamo hannunta ta ce "Daughter" kifta idanta ta danyi sannan ta kalli Ummi ta ce "Who was d visitor Mum?" Ummi ta ce "Ahmad ne, kije ku gaisa" tsayawa tayi tana kallanta bata dai ce komai ba, Ummi ta ce "I mean Jawad" a hankali ta ce "Ohh" daga haka ta mike, hijab Ummi ta dauko mata tasa sannan ta ce "U wash ur face, duk idanki ya kumbura" a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta goge idanta with clean towel sannan ta fito, daga haka ta fita a dakin ta wuce downstairs, tin tana sakkowa yake kallanta ko kiftawa babu, ita dai kanta na kasa ta karaso parlorn da sallama, zama tayi akan carpet ta ce "Ina yini" ya ce "Fine, how are u then?" Silently ta ce "Same" Jawad yayi shiru yana kallanta, dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin dauke kanta, a hankali taji muryarshi ya ce "Ya karfin jiki?" Ta goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah" tinda ta rife bakinta hawaye suka dinga sakko mata tana sharewa da hijab dinta, Jawad ya danyi kasa da murya ya ce "Destiny, kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa, so u don't have to cry, one day one time u will laugh" fashewa tayi da kuka ta ce "I will never laugh again Ya Jawad, to laugh for what? Kasan zafin da nake ji deep down me, ni kadai nasan abinda nake ji, so nobody should tell me i will laugh one day" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta, kallanta ya dinga yi daga inda yake zaune, jiin ta sausauta kukan da take ya ce "May be shi din ba alkhairi bane a tattare dake, Allah ya raba ku ne saboda ki samu wanda ya fishi alkhairi, just erase all ur bond together with him, ki manta dashi a rayuwanki, so don't cry for him pls" ta share idanta ba tare data kalleshi ba ta ce "I have to cry Yayah, he divorced me without any reason, ya azabtar dani a gidanshi ban gayawa kowa ba, after all ya tafi ya barni da cikinshi..." sarkewa muryarta tayi, hakan yasa tayi shiru tana kuka kasa kasa, Jawad ya ce "No, u don't have to, ai shi d'a na kowa ne, i can take care of the unborn child and still after his birth, so u forget about that man i beg u" a hankali kawai ta daga masa kai, ya ce "Promise u won't cry again" ta ce "Yes" ya ce "Yes what?" Ta ce "I can't make a promise to u, nasan sai nayi, saboda yin kukan kadai zai yi preventing dina from heart attack, inajin dadi idan nayi" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "To kiyi kadan" dagowa tayi tana kallansa, yana bude idanuwansa tayi saurin sunkuyar da kanta, ya ce "I think i have to go, kiyiwa Ummi sallama, Allah ya kara maki lafiya" silently ta ce "Ameen, nagode" daga haka ya mike ya fita a parlorn ta bishi da kallo, yana fita compound aka bude gate, motar Sadeeq ta shigo compound din, sosai Mami ta hade rai tana dalla masa harara, yayi karfin halin ya karasa parking lot din yana kallanta ya ce "Dama na gama abinda nake ne shine..." Wucewa tayi ta barshi nan wajen a tsaye, ya juyo yana kallan Sadeeq da fitowanshi a motar kenan ya ce "Till u come back" daga haka ya nufi hanyar gate Sadeeq ya bishi da kallo.