← Book details Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 46

Sashe 31

Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari karfe 8 Ammi ta gama breakfast ta dora akan dinning, dakin Yusuf ta shiga ta sameshi a tsaye ya goyi Imaan suna xagaye dakin, suna hada ido da Ammi ya sauke kansa kasa silently ya ce "Good morning" Ammi ta karasa shigowa dakin tana kallansu ta ce "How was your night?" Ya ce "Fine" Ammi ta kalli Imaan dake bacci a bayan Yusuf ta ce "Ai ta koma baccin ka kwantar da ita mana" murmushi kawai Yusuf yayi bai dai bari sun hada ido ba, Ammi ta ce "To ga breakfast a parlor kasan 11 ya kamata mu tafi court din" ya ce "Alright" Ammi na fita ya sauke Imaan a bayansa ya rungumeta, bude idanuwanta tayi a hankali tana kallansa, ya gyara mata gashinta daya sakko fuskarta ya ce "Sweetheart" ta ce "Papa" ya kara rumgumeta ya ce "Na goya ki har kin sake bacci" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Thank u" hannunta ya kama suka shiga toilet ya wanke mata baki da fuska sannan suka fita a dakin, a parlor suka sami Khairiyya tana zaune, ta juyo tana kallan Yusuf ta ce "Ina kwana" a takaice ya ce "Lafiya" bayan ya zauna ya daura Imaan a cinyarsa yayi serving dinsu. Cikin 10 minutes suka gama breakfast, Yusuf ya mike yana kallan Khairiyya ya ce "Ki mata wanka" ba tare data kalleshi ba ta ce "To sanda kuke hotel waya ke wankanta?" Dago kansa yayi yana kallanta ta mike a hankali ta kama hannun Imaan suka shiga ciki, yayi nodding kansa ya ce "I will surely deal with u" yana zama akan kujera Ammi ta fito a daki, ya ce "Zanje gidana" ta ce "Me za kai kuma?" Ya ce "Zan sa a gyaramin ne" Ammi ta tsaya kallansa ta ce "Why not after everything?" Ya dan shafa kansa ya ce "Ammi inasan na koma can ne" a hankali ta ce "To, sai kayi kokari ka dawo kafin time din yayi" ya mike ya ce "Insha Allah" daga haka ya nufi daki ya dauko key din gidan ya futo, dakin Nabeel ya shiga ya samu Sameer na kwance yana bacci, ya duba kan mirror ya samu key din motarsa ya dauka sannan ya fita, yana fita compound din gidan ya wuce parking lot yayi warming motar sannan yaja ya bar gidan. Cikin minti 10 ya isa gidansa yayi parking a waje sannan ya fito yasa key ya bude padlock din ya shiga ciki, bayan few minutes ya fito ya rife gidan sannan yaja motar ya bar layin, ba jimawa ya dawo da wasu samari su 2, suka fito a motar bayan ya bude gate din suka bi bayansa, bude musu kofar parlor yayi ya nuna musu broom da mop sannan yasa face mask dinsa ya bude part din Jiddah suka bishi a baya, yana tsaye bakin kofa suka gyara dakin tass sukai mopping, baza kace shine ya hada wannan kuran ba, rufo dakin yayi suka fara gyaran parlor, yana nan tsaye bakin kofa yana kallansu, da sauri yasa hannu a pocket dinsa ya ciro phone dinsa dake ringing, ya daga ya kai kunne hade da sallama, Jiddah ta ce "Naga kudin yau da safe, amma dai kasan ba zai isheni ba ko" limshe idanuwansa yayi ya ce "I will call u ltr, ina wani abu ne" daga haka yayi hanging wayar. Cikin 30 minutes suka gyara gidan, har part din Rafi'ah daba komai a ciki saida suka share sukai mopping, bayan sun gama suka fito tsakar gida suka hau sharewa yaja kofar parlorn ya rufe, cikin few minutes suka share tass suka fitar da sharan, Yusuf ya basu 4k yana musu godiya, suka masa sallama suna masa godiya suma suka fita, padlock yasa ya rife gate din sannan ya shiga motar ya dau hanyar gidan Ammi. Bayan yayi horn aka bude gate din ya shiga yayi parking, ya fito ya nufi entrance din gidan, da sauri Imaan ta fito a parlor fuskarta da hawaye ta nufeshi, ya dagata yana kallan idanta ya ce "I'm back sweetheart" cikin muryar kuka ta ce "You ran away Papa" ya shafa bayanta ya ce "I didn't dear, ba gashi na dawo ba" ta danyi murmushi tana kallansa ya shiga share mata idanta, suna shiga parlor Ammi ta ce "Tin dazu take mana kuka" Yusuf yayi murmushi yana kallan Ammi ya ce "Na dawo ai" daga haka ya ajiyeta akan kujera ya ce "Wait for me here" ya shige daki ya barta anan wajen zaune. Cikin kankanin lokaci suka shirya zuwa court, Daddy da Ammi da kuma Khairiyya a mota Yusuf kuma da Sameer sai Imaan, sai da suka biya suka dauko Jiddah a gidansu sannan suka wuce court din, sai kumbura take tana hararan Imaan, kuma tayi alwashin saita tonawa Umma asiri ta wulakanta, suna zuwa Jawad ya kaisu har inda zasu zauna, babban court ne sosai, ba kowa a kan stage din saboda kowa shirye shirye yake, ba jimawa su Mummy suka zo, Yusuf ya karasa har inda suka suka gaisa sannan su Ummi suka taso suka gaisawa da Ammi, karfe 11 da rabi Jawad ya dauki motarsa yayi school din su Rafi'ah, kafin ya karasa har sun fito a exams dinsu, bayan ya isa yayi parking ya fito yana kallanta, juyawa tayi da sauri jin alamar motsi, ta sakar masa murmushi tana kallan kayan jikinsa ta ce "Woow Barrister, kaga yadda kayi kyau, kayan ya maka kyau sosai" yau ne ranar farko data fara ganinsa da kayan sai dai kuma a hoto, ya ce "Thank u sweetheart, muje Fatima we don't have much time" daga haka suka shiga motar yayi reverse suka fita. Within 10 minutes suka iso court din an gama komai Rafi'ah kawai ake jira, tinda suka fara shiga zuciyarta ya hau bugawa kuma ta dauki alkawarin yau sai ta kar6i Imaan dinta, ta sunkuyar da kanta dan karma ta hada ido da Yusuf, Imaan ne ta dan wara ido ta ce "Papa here is my Mom" ta karashe maganar tana nuna masa Rafi'ah data zauna dan nesa dasu taki kallansu, sau daya ya kalleta ya dauke kai, Jiddah ta dallawa Imaan harara hakan yasa tayi shiru ta kwanta akan kirjin Yusuf, signing Jawad yayi sannan ya mikawa na gefensa takardar shima yayi signing, bayan haka Alkali ya bada unarnin a shigo dasu Umma, ba jimawa aka shigo dasu duk sunyi baki, Anty Khadija ta gwalalo ido ganin mutanen dake zazzaune, aka wuce dasu aka kullesu a inda aka tanada dan masu laifi irinsu, bayan komai ya kammala kotu ta bada dan brief na abinda ta sani akan su Umma, Alhaji Usman shima da iyalansa na zaune gefe guda, bayan haka Kotu ta bada dama Yusuf yayi introducing kansa da kuma takaitattcen labarinsa, da kyar Sameer ya rike Imaan dake ihu saita bishi, bayan ya karasa wajen yayi sallama cikin sanyi murya ya fara bada tarihin rayuwarsa daki daki har zuwa yanzu, bai rage koya kara komai ba akan abinda ya faru, harya gama kuwa Rafi'ah bata kalleshi ba kanta na kasa idanta ya cika da kwalla, bayan ya zauna ita ce next da aka kira itama ta taso duk jikinta yayi weak, Jawad da shine zai mata tambayoyi ya dan kashe mata ido daya, silently ya ce "feel free" ta shiga wajen ta tsaya kanta a kasa, itama cikin sanyin murya ta fada musu labarinta tin haduwarta da Yusuf har auransu da kuma rabuwarsu da yadda tasha wahala kan cikin Imaan har aka mata CS, tana kaiwa nan ta tsaya ta share idanta, sai lokacin Yusuf ya kalleta na seconds sannan ya dauke kai. A sanyaye ta koma ta zauna bayan an sallameta, daga nan aka kira Jiddah, dama Allah Allah take a kirata, babu 6ata lokaci ta tashi ta tafi Rafi'ah ta bita da kallo, tana shiga wajen ta fadi alakarta da Yusuf a takaice sannan ta danyi murmushi, hada ido sukai da Umma dake ta kifkifta mata ido amma tayi kamar bata ganta ba, Jiddah ta dan yatsina fuska tana kallanta ta fara bayani kamar haka "Wannan matar dake tsaye ita da 'yarta su suka jefani hanya karkatacciya, kuma su sukai sanadiyyar raba auran Yusuf da waccen yarinyar Rafi'ah, su suka san yadda sukai suka shiga suka fita yaji ba abinda ya tsana a rayuwarsa sama da ita" Jiddah ta danyi murmushi tana kallan Anty Khadija ta ce "Bazan manta ba, shekara 4 da suka wuce Khadija tazo gidana tace in hada mana kayanmu zamu bar kasar sun gama shirya komai, bayanta tafi Umma ta kira Yusuf ta umarce shi daya saki Rafi'ah, shi kuwa ganin a lokacin ba wacce yake jin maganarta sama da ita yayi abinda tace, kamar yadda ya fada ya tafi ya barta tana laulayin wannan yarinyar, a ranar da muka sauka a Egypt wani bawan Allah wai dan ajin su Umma yazo ya taremu ya kaimu masauki, ba mufi sati ba da taimakaonsa Yusuf ya samu aiki, ana haka ana haka duk bayan wata daya sai Umma ta turawa bokanta kudi saboda ya sake dora aikin karna baya ya warware, sannan ya kafa musu sharadi na cewa sai Khadija taje wajensa a shekara sau daya ya sadu da ita, to dai sau biyu ya faru ana ukun suka ki zuwa, duk karshen shekara muna dawowa Nigeria mu sauka a Kaduna amma Yusuf bai ta6a budar baki yace ina Rafi'ah ba, komai kuma normal yake amma cikin ransa ji yake babu mutanen daya keso sama damu, Kwatsam wata sati 3 da suka wuce Alhaji Usman ya saki Khadija, ana haka a karshen shekaran nan Yusuf ya fara ciwo sosai, harta kaiga baya iya magana, ganin haka yasa Umma ta tattaro mu muka dawo Kaduna, anan kuma muka fuskanci tinanin Rafi'ah ya dawo masa yayinda ya fara kiran sunanta, shine Umma ta tura Khadija da tazo wajen bokan ta bashi kudade danya maida mata aikin sabo kuma ta bashi hakuri akan batazo wajensa ya kwana da ita ba, to anan ne na samu labarin an kama ta, yayinda asirin Alhaji Usman ya bar jikinsa shima" tinda Jiddah ta fara magana Yusuf kansa na kasa sai data dasa aya hawayen idansa ya gangaro, nan da nan ya fara furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jawad ya kalli Jiddah dake tsaye ya
Chapter 31 · 0% Book details