Sashe 41
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Slowly ta bude idanuwanta tana bin dakin da kallo, ta mike a hankali ta shiga toilet, After few minutes ta fito daure da towel tana kallan agogon dake jikin wall, dan zaro ido tayi ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga ta saka sannan tayi packing smooth hair dinta tasa hijab ta tada sallah, bayan ta idar ta jima tana addu'a sannan ta kifa kanta akan gado tana tuno rayuwarta right from the beginning till now, batasan lokacin da wasu hawaye masu zafi suka sakko mata ba, jin an bude kofar tayi saurin goge idanta ta limshe idanuwanta, Jawad ya karaso inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "How are u sweetheart?" ba tare data dago kanta ba ta ce "Fine, good morning" ya danyi murmushi yana dora hannunsa a kanta ya ce "Morning" dago kanta yayi yana kallan fuskarta ya ce "Open your eyes?" Ta noke kafada, ya dan shafa beard dinsa yana kallanta ya ce "Kunyana kikeji?" ta girgiza kai ta ce "No, just that..i'm not..feeling fine" yadda tayi maganar yasa ya danyi shiru yana kallan cute face dinta, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Now tell me what's wrong with you" sai lokacin ta bude idanuwanta suna hada ido ta sauke kanta kasa, ya danyi murmushi ya kai bakinshi kunnenta yayi mata magana, daga masa kai tayi, ya bata light hug yana murmushi ya ce "Just like your first experience?" ta daga masa kai, ya rungumeta ya ce "I'm sorry, pardon me pls" ta zame jikinta a nashi ta mike ta ce "I want to sleep" ya mike yana kallanta ya ce "Breakfast fa?" Ta dan turo baki ta ce "I'm not hungry" ya zauna bakin gado yana kallanta ya ce "No u have to eat ko kadan ma, kinga tin dazu na tashi nake ta faman hada maki breakfast" kanta a kasa tana kallan dogayen yatsunsa dake kan kafarta, ya dan 6ata rai ya ce "So u won't appreciate?" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya tashi tsaye ya dagata tayi saurin nokewa ta ce "Ai zan iya" ya ce "To naga kinaso na daukeki ne" ta dan turo baki tana kallansa ta gefen ido, ya kafe ta da ido ya ce "Kuma aciremin himar din nan" ta dan zaro ido ta ce "Yaaayaaahh" ya ce "Yes now, ni baza kimin yawo da himar a gida ba" ta zauna bakin gado ta ce "Tona fasa yin breakfast din" zama yayi gefenta ya ce "To naji tashi muje" mikewa tayi tana turo baki ta fita a dakin, ya shafa gashin kansa yana murmushi yabi bayanta. _3 weeks ltr_ Jawad ne zaune a parlor yana operating laptop, daga kansa yayi ya kalli time sannan ya mike ya haura upstairs, dakinsa ya bude ya samu Rafi'ah na kwance tana waya, suna hada ido ta turo baki tayi hanging call din ta juya masa baya, ya danyi murmushi ya karasa kan gadon ya ce "U haven't eat dear, ya jikin ki?" a hankali ta ce "Na koshi" ya dagota zua jikinshi ya ce "Are u still angry with me?" Ta girgiza masa kai a hankali sai kuma ta kifa kanta a kirjinsa tana sharar hawaye, cikin rarrashi ya ce "Ki bari next week sai muje i promise u this time around kinga shekaranjiya da zazzabi kika kwana" cikin muryar kuka ta ce "Ni wallahi na gaji u are always saying next week, 3 weeks banga Ummina ba banga Abba ba banga kowa ba sai Abdul daya zo min sallama ya koma school, ko Imaan sau biyu Khairiyya ta kawota" fashewa tayi da kuka ta kankameshi, shi dai kasa cewa komai yayi, caan ya dan bubbuga bayanta ya ce "Tashi ki shirya na kaiki, u meet me downstairs" daga haka ya janyeta a jikinsa ya dauki car key dinsa ya fita a dakin. Kwanciya tayi ta dinga share hawayen idanta bata kuma tashi ta shirya ba, bayan 20 minutes ya shigo dakin ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Are u not going?" Ta dago jajayen idanuwanta tana kallansa ta ce "Ba fishi kakemin ba" ya dan zaro ido ya ce "Niiiii?" ta ce "Ehh" ya ce "A'a niba fishi nake maki ba, kawai rigimarki ne tayi yawa, idan kinyi hkr ma na karasa da case din nan sai in kaiki gida harki kwana, amma kince ke bakyaso, then sai muje na kaiki anjima na dauko ki" sakkowa tayi akan gadon tana kallansa ta ce "Amma ba fishi kamin ba?" Ya daga mata kai yana kashe mata ido daya ya ce "In the next 2 weeks zaki koma school ma ai" toilet ta shiga ya bita da kallo yana dariya, fuskarta ta wanke tass sannan ta fito ta goge da clean towel ta fita a dakin zuwa dakinta, press dinta ta bude ta dauko atampa doguwar riga ta saka, sosai dinkin ya zauna mata tayi dauri me kyau tayi light make-up sannan ta yafa veil ta fashe jikinta da turare, tana juyawa suka hada ido da Jawad dake bakin kofa yayi folding hannayensa, ta sauke kanta kasa ta fara kwashe kayan data cire ta shiga toilet tasa a washing machine, a hankali ta karaso kusa dashi ta ce "Na gama" ya rungumeta yana limshe ido ya ce "U looks more beautiful wife" a hankali ta ce "Thank u" sakinta yayi ya kama hannunta suka sauko downstairs sannan yayi switching sockets suka fita ya rufo kofar, side hug ya bata suka karasa parking lot ya ce "Yaushe zan dauko ki?" Ta ce "Da daddare" ya ce "No ban yarda ba" ta ce "Allah Yaya zanyi hira da kowa sosai na dade fa bangansu ba" ya ce "After Magrib zanzo" ta dan tsaya tana kallansa ta ce "Why not 9pm or 10pm Yaya?" Murmushi yayi ya bude mata motar ya ce "Bismillah" bayan ta shiga ya rufe ya zagaya mazauninsa. Khairiyya ce kwance akan gadonta tana rokon Yusuf karya mata allura, gaba daya fuskarta ya wanku da hawaye, injection din hannunsa ya ajiye a gafe yana kallanta ya ce "It won't pain you lil sis, kinga jikinki yayi zafi" cikin kuka ta ce "Ai Daddy yace magani zan sha" ya ce "To bakiji sauki ba kinga sai allura kenan, bari na kira Ammi ta rike ki" sanin Ammi baza ta mata da dadi ba yasa ta danyi kara ta ce "Wallahi zata min fada dan Allah karkamin me zafi zan tsaya" ya ce "A hankali zan maki" daga haka ya dauki injection din ta juya jikinta na rawa, yana mata ta saki kara ta kankame hannunsa, yasa mata cotton wool a wajen yana murmushi ya ce "Allah ya baki lafiya" harara ta maka masa ta ce "Ba amin ba" ya fashe da dariya ya ce "Ameen din dai, in kuma kikaiwa kanki addu'an haka ni kuma naita maki allura" Ammi ne ta shigo dakin rike da cup ta ajiye a gefen gado ta ce "Anyi alluran?" Ya ce "Ehh" ta ce "Ga tea idan zaki sha" daga haka ta fita a dakin. Zama yayi a gefen gadon ya dauko tea din ya kai bakinta ya ce "Kar6i kisha" ta noke kafada tana jujjuya ido ta ce "Nina koshi" ya ce "To haka zamuyi auran kina harara na" ta ce "Aini ban harareka ba" ya ce "To kwanta kiyi bacci" a hankali ta zame jikinta ta kwanta ta ce "Yau kace zaka kaini na kaima Imaan abinda ka siya mata" ya ce "Not today, sai idan kin samu sauki" ta ce "Da yamma dan Allah" ya ce "Sai naga idan kin samu sauki kafin nan". Parking Jawad yayi a kofar gidan Abba yana kallan Rafi'ah ya ce "Mun karaso" kafin ya rife bakinsa ta bude motar ta fito ta shige ciki da sauri, tana bude kofar parlor ta dan ja baya ta wara ido ta ce "Saudat" Saudatu dake murmushi ta ce "Anty Rafi'ah" Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Long time, sai waya kawai, ya mutanen garinku dasu mamanku, wannan babynki ce?" Rafi'ah ta dauki 'yar farar yarinyar da batafi 3 months ba tana jujjuyata ta ce "Masha Allah, ta girma sosai, me sunanta?" Saudatu na murmushi ta ce "Sunanku daya, nima wayana ne ya fadi banda numberku" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Allah ya raya ta da Imani, shiyasa bama saminki ashe?" fitowa Ummi tayi a kitchen Rafi'ah ta nufeta da sauri tayi hugging dinta ta ce "I missed u Ummina, ina Abba?" Ummi ta ce "Abba ya fita dazu, bakimin waya zaki zo ba, da yanzu zan sauke Saudatu a gidanki na wuce aiki" ta danyi murmushi ta ce "Nima ina shigowa kawai na ganta, i was so surprise ashe zata kawo mana ziyara" Saudatu dai ta danyi murmushi, Sakkowa Imaan tayi da gudu ta nufi mahaifiyarta ta rungumeta, Rafi'ah tayi hugging dinta tana kallanta ta ce "Kinga na samu wata babyn, do u like her?" Imaan ta daga mata kai, murmushi tayi ta koma kan kujera ta zauna Imaan ta zauna a gefenta, jin knocking yasa ta dan zaro ido, Ummi dake kallanta ta ce "Tare kuke ne?" Ta mike da sauri ta ce "Ehh" parlorn Abba Ummi ta shiga sannan Rafi'ah ta bude masa kofar, ya shigo hade da sallama ya zauna akan carpet, amsa gaisuwar da Saudat ke masa yayi, ya kalli Imaan dake kallansa ya ce "Come to me daughter" ta karaso da sauri ta rungumeshi harda hawayenta wai ya gudu ya barta, chocolate ya bata masu yawa hakan yasa ta hakura da mitan tayi shiru, bayan few minutes Rafi'ah ta masa jagora yaje ya gaishe da Ummi sannan suka fito, daga haka ya koma mota. Parlorn Abba Rafi'ah ta shiga ta zauna gefen Ummi ta ce "Dafa yini nazo kuma kince zakije aiki" Ummi ta ce "Why didn't u call me and ask? Test kuma zan musu, sai kije gidan Mummy ga Imaan nan, idan na gama zan biya na dauketa" ta dan hade rai ta ce "To, wani satin saina dawo" Ummi dai bata ce mata komai ba ta fita a parlorn, mikewa tayi itama ta fito a parlorn ta samu Saudatu na goya Babynta suna sallama da Ummi, ta ce "Tafiya zakiyi ne" ta ce "Ehh wallahi zanje gidan wata Innarmu anan zan kwana" Rafi'ah ta ce "To