Sashe 2
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance Ummi ta sameta ta rufo da blanket, jin motsi yasa tayi saurin goge hawayen idanta ta tashi ta zauna, Ummi ta zauna gefenta cike da damuwa ta ce "U haven't eat dear" dan turo baki tayi ta ce "Na koshi Ummi" shiru Ummi tayi tana kallanta ganin yadda ta kara mungun rama akan da, ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To me zakici?" Tayi saurin girgiza kai ta ce "Banasan abinci kuma" Ummi ta ce "Me zakici to idan ba abinci ba, or do u need tea?" Ta girgiza kai, Ummi ta ce "Conflask?" Ta kara girgiza kai ta ce "Awara nakeso" Ummi ta ce "To bari na bawa Saudatu ta samo maki, tashi muje kasa" dan noke kafada tayi kamar zatai kuka ta ce "Ummi bacci nakesan yi" Ummi ta kamo hannunta ta ce "Sai kiyi a kasan ai, zakuyi sallama da Mummy ne, beside that ma banasan kina zama ke kadai" dan kwalinta Ummi ta daura mata sannan ta kama hannunta suka fito a dakin. Very slowly ta dinga bin Umminta har suka sauko a steps din, Mummy dake kallansu ta ce "Lafiya dai?" Ummi ta ce "Wai Awara zata ci" gefen Mummy Rafi'ah ta zauna ta ce "Mummy tafiya zakiyi?" Mummy ta kamo hannunta ta ce "Insha Allah, ina jiran driver ne, but kullum zan dinga zuwa kallanki harki samu sauki sosai, abinda nakeso dake shine ki daina kukan nan, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu mahalukin daya isa canzashi, shi kuma Yusuf ki watsar da kashin sa, ki saki jikinki ki daina damuwa dashi, banda hauka irin naki ma mutum yaci amanarki haka amma ki zauna kina kuka akansa" share hawayen idanta tayi tana kallan Mummy ta ce "Ni bana san shi kuma, i hate seeing him, ko mai kamarsa banasan na gani, what is making me to cry is..." Fashewa tayi da kuka ta kasa karasawa, Mummy ta bata side hug ta ce "Dan ya barki da ciki a kanki aka fara? Ke dai ki kula da kanki ki haife abinda yake jikinkin ki kawai, ina guje masa ran da zai zo yana blaming abinda kika haifa dan dansa ne, wallahi babu me rabani dashi duk duniyar nan, saina wulakantashi kamar yadda yayi mana, sai na sa shi kuka da kunci na har abada, kuma d'a ba nasa bane, kece uwarsa kece ubansa" ita dai Rafi'ah sai share hawayen idanta take, bayan haka ta zame akan sofa ta kwanta akan carpet ta rufe idanta tana addu'a, wani zafi da takaici take ji deep down her, ba dan ba dan ba da tayi addu'a Allah yasa cikin ya bare itama ta hutawa rayuwarta. Bayan 10 minutes Saudatu ta shigo da warmer a hannunta, Ummi dake zaune suna hira da Mummy ta ce "Kin samu?" Saudatu ta ce "Ehh na samu" Ummi ta daga Rafi'ah ta ce "Dear, ga Awaran an kawo maki" a hankali ta bude idanuwanta tana kallan Ummi ta ce "I'm sleepy" Ummi ta ce "I know, try and eat ko kadan ma, tin safe bakici komai ba" gyara zama tayi ta jingina da jikin kujera sannan ta bude warmer din, fork Saudatu ta mike mata ta fara cin Awaran, daga Ummi har Mummy kallanta suke, kai kace tayi sati bataci komai ba, na bakinta baya karewa take saka wani, su kam hakan yayi musu dadi, indai zataci ai komai zaizo da sauki, kusan rabin warmer din ta cinye sannan ta rufe ta ajiye a gefenta ta ce "Anjima zanci wannan" Ummi ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Ba wanda zai ta6a" daga haka ta kwanta ta limshe ido, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Ba jimawa driver yazo daukar Mummy, a hanyarsu zuwa gida yake fada mata Jawad ya dawo, with surprise Mummy ta ce "Har sunyi landing?" ya ce "Wallahi Hajiya, kafin naje daukoshi wani abokinshi ya kawo shi gida" Mummy ta ce "Inaga dai sanda ya kirani yayi rabin tafiyar". Anty Amina ce zaune a parlorn Ummanta tana shan exotic, lokaci~lokaci takan kalli Anty Rahama dake ta trying number Anty Khadija amma yaki shiga, Anty Amina tayi murmushi ta ce "Maman Leemah wai menene damuwarki akan Khadija ne? Naga randa abin ya faru munyi magana da ita tace sun bar kasar" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Duk tasu?" Anty Amina ta ce "Ehh mana, ni lokacin kaina ya dau caji ban gaya miki ba, ga zaman dole na asibiti" Anty Rahama ta ce "Amma tace tayi aure a Kaduna da mijin ta wuce kenan?" Anty Amina tayi dariya ta ce "Kema kinsan ba zata harshi ba ai, mijin da aka zautarwa hankali ya bar matarsa da manyan 'ya'yansa ya aureta ta ina zata barshi, ai suna caan ko wacce kasa Allah masani, amma dai ni banga abin tada hankali dan baki sameta a waya ba, ina dai burinmu ya cika, shikenan sai mu barta ta sha iska" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Hakane kuma, Allah ya raka taki gona" daga haka suka tafa Anty Amina ta ce "Atooh, haushinama yarinyar da tai ciki, koba komai zasu danganta d'an da Yusuf" Anty Rahama ta mata wani kallo ta ce "Taab ai kuwa wannan yayar uwartan ba yarda zatai ba, lokacinfa da mukaje da Yah Muhammad gidan Yusuf wuka ta dauka tana nemansa daki daki wai saita kashe shi, nasan dai ko zafin haushine ya sata haka baxa dai ta bari ya kar6i abinda Rafi'ah zata haifa ba, ke nifa mamaki abin ya bani, banyi tinanin wannan figigiyar zata daukar ciki da wuri ba, gaki nan zabgegiya dake shekara kusan 5 ba labari" nan da nan Anty Amina ta hade fuska ta ce "Dan Allah kimin cikin nan idan zaki iya, ba dai Allah ke bayar ba, nayi maganin harna gaji babu labari, kema naga a shekaru 22 da kikai gidan mijinki 'ya dya kawai kika haifa" Anty Rahama ta ce "Amma dai na haifi dayar ko, to dan Allah kema kiyi zuciya ki haifo ko nakashashshe ne" Anty Amina ta mike ta ce "Sai dai ke ki haifo, gashi mun fara gani kin haifo mai cuta" cushion Anty Rahama ta cilla mata cikin 6acin rai ta ce "Ki shiga hankalinki Amina, karki kara kiramin Ikleemah da mai cuta" fitowa Umma tayi a daki taja Anty Rahama tana bata hakuri suka shiga ciki, bayan nan ta fito ta rarrashi Anty Amina ma, wai ai sai ace basu da hadin kai, kuma abin kunya ne suyi fada a junansu, ita dai Anty Amina baki kawai ta ta6e taci gaba da shan exotic dinta. Fuskarsa dauke da murmushi ya shigo parlorn, Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Mutanen Cyprus" ya dan shafa tulin gashin dake kansa ya ce "Ina yini Mummy" ta ce "Lafiya kalau, have a seat, ashe harka dawo?" ya ce "Ehh kusan awana 1 ma, fatan na sameku lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah" mikewa yayi yana kallanta ya ce "Zan answer call ne" ta ce "Alright no problem" daga haka ya fita a parlorn, part din Maminsa ya shige hade da sallama, Abi na zaune a gefen Mami sai Ikram dake kan carpet a zaune, Jawad ya danyi kasa da kansa ya ce "Ashe ka dawo, na dauka zaka kirani na dauko ka" Abi ya ce "U don't have to worry son, kai da ka dawo a tafiya, Sadeeq ya daukoni" kan kujera Jawad ya zauna yana kallan TV, Abi ya kalli Mami data dan hade fuska ya ce "To meyasa bakije yau ba?" Ta juyo tana kallansa ta ce "Naga dai an sallameta har sun koma gida, gidanma kullum zan dinga zuwa kenan?" Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "U have to go, asibiti da ban gida da ban, don't make me repeat my self kije kawai ki duba ta" tashi yayi ya fita a parlorn Mami ta bishi da wani irin kallo. Jawad dake kallanta ya ce "What's going on Mami?" Dan karamin tsaki taja ta ce "Ina kana da labarin auran Rafi'ah wanda akayi bayan kwana biyu da tafiyarka" ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba, ya daga mata kai yana kallanta, Mami ta ta6e baki sannan ta ce "She's divorced" with shock ya juyo yana kallanta ya ce "Divorced" ta ce "Saki ba, ya saketa saki daya" innalillahi Jawad ya dinga furtawa yana kallan mahaifiyarsa, Mami ta ta6e baki ta ce "Wallahi sakin wulakanci, daya bata takardar ya bar gidan shida matarsa, har yau ba'a san inda yake ba, ya tafi ya barta da karamin ciki, inka ganta kamar ka hureta ta fadi, ni cewa nayi ma da zubar da cikin sukai, yarinyar dako 18 bata cuka ba, sanda naje sunanta Ikram dina tafi shekara 1" kasa daina kallan Mami yayi, lokaci daya yaji komai nasa ya tsaya musamman data ambaci ciki, Mami ta gyara zamanta ta ce "Ni gani nake saboda cutarta ya gujeta, yanzu a zamanin nan yaushe zaka auri mata mai ciwan zuciya, duk wata fa sai sun kar6i magani ga uban tsada, shi kuwa inaga yayi na Allah yace ya gaji, ba dan ubanta nada dukiya ba inaga gidan da zasu zauna ma sai ya gagaresu" Tashi Jawad yayi ya shige daki, yana rufo kofar idanuwansa suka cika da hawaye, bai bari sun zuba ba saima murmushi da yayi ya dauki key din motarsa dake kan mirror din dakin, jin an bude dakin yayi saurin juyawa, Mami ta ce "Ya muna magana zaka tashi ka barni ba excuse" ya ce "Na tina akwai inda zanje ne" ta ce "Ina?" Ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce "Wajen aiki, akwai papers din da zan kai musu wanda na taho dasu" Mami ta ta6e baki ta zauna bakin gado ta ce "Haka dai kullum aiki aiki, idan dai kayi aure barin wannan kotun zakayi ka nemi wata" a hankali ya ce "Ohk, saina dawo" daga haka ya fita a dakin. Driving kawai yake amma gaba daya tinaninsa ya tafi wajen Rafi'ah, minti 10 ya kaishi kofar gidan, yayi parking a waje sannan ya fito walking gently ya tura gate din, ganinsa yasa Mustapha ya kara bude kofar yana masa sannu da zuwa, daga masa hannu yayi ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din yaji kofar a bude, ya shiga parlorn da