Sashe 4
Life Partner Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read
_08103810398_
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._
_By FATIMA ✍🏻_
_2_
Shiru Rafi'ah tayi ganin Mami ta shigo parlorn, ta mike a hankali tana goge hawayen idanta ta ce "Sannu da zuwa" Mami ta zauna kan kujera kamar bazata amsa ba, sai kuma ta ce "Sannu, ya karfin jiki?" silently ta ce "Naji sauki" Mami ta dago kai tana kallanta ta ce "A hakan?" Rafi'ah ta daga mata kai, sai kuma ta ta6e baki ta ce "Aike da jin sauki sai kin haife wannan jarabar ta cikinki, bayan haka kin samu me auranki, shine zaki ce kin fara samun sauki, dan mace ta zamu zama agidan miji ma wani falala ne, kinga idan kika kara fitowa ai ciwo ya koma baya" kara goge hawayen idanta tayi ta dan turo baki ta ce "Niba aure kuma zan sake yi ba" daga haka ta nufi upstairs, Mami ta mike ta ce "To kya gaisheta daman jikinki nazo dubawa" daga haka ta mike ta fice a parlorn Rafi'ah ta bita da harara. Very gentle ta dinga taka steps din harta gama hawa, ta shige dakinta ta rufo kofa, har zata kwanta aka bude kofar dakin, Abdul ya karaso yana kallanta ya ce "Sannu" ta ce "Thank u" ya ce "We just came back with Abba, na siyo maki grapes da Apple and shawarma" dan murmushi kawai tayi dan ita yanzu ta tsani komai idan ba dan~wake ba, kwanciya tayi tana kallansa ta ce "So much thanks bro, nagode" gyara mata blanket din jikinta yayi ya ce "Allah ya baki lafiya" ta ce "Ameen" ganin ta limshe ido yasa ya mike ya fita a dakin ya jawo mata kofa a hankali. Ammi ce zaune a parlornta Sameer na gefenta a zaune, gaba daya jikinsa yayi sanyi jin abinda dan~uwansa ya aikata, shida yake murna zai dawo gida yaga 'yan uwansa cikin farin ciki amma kuma yaji abunda ko a mafarki bazai yarda ba, Ammi ta dan goge hawayen idanta ta ce "Yarinyar nan ta sha wahala Muhammad, idan ka ganta gaba daya ta rame" Sameer ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Allah ya kyauta, kenan bai gayawa kowa inda zaije ba" Ammi ta ce "Ba wanda ya sani, wadanda ya kamata su sani su suka daukeshi suka tafi dashi, nasan Yusuf dina bazai iya butulci da wulakanta mace haka ba, wallahi Sameer akwai abinda yake faruwa" kamo hannunta Sameer yayi ya ce "Stop crying pls mother, in sha Allah wata rana zai dawo, na miki alkawarin zan kula da yarinyar da kuma abinda zata haifa" Ammi ta kara share hawayen idanta ta ce "Allah ya baka iko, zamuyi ta addu'a Allah ya bayyana shi" a hankali ya ce "Ameen, yanzu dare yayi kuma na dawo da ciwan kai, gobe insha Allah zanje na dubata" Ammi ta ce "Allah ya kaimu goben" ya ce "Ameen, amma dan Allah ki daina kuka".
Karfe 12 na dare Jawad ya dawo gida, bayan yayi parking sai daya tabbatar gate man ya rufe gate sannan ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din kofar yaji a kulle, ya ciro wayarsa a pocket dinsa yayi dialing phone din Sadeeq, bugu biyu ya dauka hade da sallama, Jawad ya ce "Open the door for me, na parlorn Abi" da to kawai ya amsa sannan yayi hanging call din, few minutes Sadeeq ya bude masa kofar, ya shigo sannan Sadeeq ya rufe kofar ya koma dakinsa, har zai shige dakinsa Abi ya bude kofar part din Mami ya ce "Who's that?" Jawad ya juyo a hankali ya ce "It's me" Abi ya ce "Ya sai yanzu zaka dawomin gida Ahmad, is exactly past 12 now" kafin yayi magana Mami ta fito tana masa wani kallo ta ce "Gashi nan saiya gaya maka gidan ubanwa yaje daya kai dare haka bai dawo ba, tin bayan isha dana je gidansu yarinyar nan na samu shi yana fita, daga nan ko gidan uwarsa wa ya tafi ban sani ba" Abi dake kallansa ya ce "Where have u been Ahmad? Kaje gidan su Fatima ne" a hankali ya ce "Ehh, but i left there since 8, naje wajen Aliyu ne baya nan, shine naje asibiti wajen Umar anyi admitting dinsa ne, anan na zauna sai yanzu" Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya koma ciki, Mami dake tsaye tana kallansa ta ce "Kai ko tsoro bakyaji a tattaraka ubanka yana dan siyasa" a hankali ya ce "Ba abinda zai faru by God grace Mami" ta wurga masa harara ta ce "Aini gara kayi auranka ka barmin gida, idan yaso ka kai karfe 1 baka koma ba, wacce ka aura ne dai sai dai tayi hakuri" dan murmushi yayi yana kallanta ya ce "Sai da safe" daga haka ya shiga dakinsa ta bishi da harara.
Washegari ya kama Monday, da safe Ummi ta gama hada komai da taimakon Saudatu, bayan ta shirya ta shiga dakin Rafi'ah ta sameta a kwance tana bacci, rufo kofar tayi ta koma dakinta, Abba dake zaune yana rubutu ya ce "Haka zaki fita ki barta at this condition kenan?" Dagowa tayi tana kallansa ta ce "I'm not staying long, 2 hours lectures kawai zan musu, sai meeting daza muyi, amma idan kace na zauna ba damuwa" Abba ya ajiye pen din hannunsa ya ce "No, idan kinga dai ba matsala kije kawai, amma kinsan tana bukatar me kula da ita ko?" Ummi ta ce "I knew, amma ga Saudatu ai, komai takeso zata bata" Abba ya ce "Ohk, Allah ya kiyaye" ta ce "Ameen, 2 days per week kawai nake da lectures din" ya ce "Alright, a dawo lafiya" Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Allah yasa" daga haka ta fita a dakin, bayan ta sauko kasa ta zauna akan kujera tayi kiran Saudatu, cike da ladabi yarinyar ta karaso ta zauna a kan carpet ta ce "Gani Ummi" Ummi ta ce "Zan je aiki ne, idan Rafi'ah ta tashi ki bata tea first, after then akwai dan wake cikin warmer idan zata ci, kuma karta taita kwanciyar nan dan Allah, idan kin gama abinda kike zaki iya zama da ita" Saudatu tayi kasa da kanta tana murmushi ta ce "To Ummi insha Allah, a dawo lafiya" Ummi ta ce "Allah yasa" daga haka ta mike ta fita a parlorn.
Karfe 10 Rafi'ah ta tashi, ta dinga bin dakin da kallo kafin ta mike a hankali ta zauna, yau kam Alhamdulilah jikinta ba zafi sosai, kuma batajin ciwo a ko ina, mikewa tayi ta dauki towel ta shiga toilet, kusan 15 minutes tayi taking a ciki kafin ta fito da towel daure a kirjinta ta zauna gaban mirror, Yusuf kawai ta tuna a lokacin, dan mostly idan ta fito a wanka shi yake tsayawa a bayanta ya taje mata kai ya taya ta shiryawa, jin kirjinta na bugawa yasa ta limshe idanta tana addu'a, bayan minti 2 ta bude idanta sannan ta shafe jikinta ta mike ta bar wajen, doguwar riga na atampa ta saka sannan ta daura dankwalinta ta shafa white powder sai lip gloss, sosai tayi mungun kyau duk da ramar da tayi, ta jawo phone dinta dake kan gado ta kira Mummy, sosai sukai waya, kuma jin muryarta yasa hankalin Mummy ya kara kwanciya, bayan sunyi sallama ta ajiye phone din sannan ta fara gyara gadon. Tana cikin gyaran Saudatu ta bude kofar, ta danyi murmushi ganinta ta ce "Anty Rafi'ah bari na gyara miki" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "A'a Saudat bari nayi kawai" Saudatu ta danyi shiru tana kallanta, sai kuma ta ce "Bari na kawo miki tea" ta ce "No, zan sakko kasa yanzu, Abbana ya fita ne?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Gaskiya banga fitan shi ba, amma Ummi ta fita" ta ce "Ehh jiya tacemin zata koma aiki yau" fita Saudatu tayi a dakin tana murmushi, ita kanta dadi taji ganin Rafi'ah a haka, ta wuce kitchen ta fara hada mata dan~waken kamar yadda taga Ummi nayi, Bayan Rafi'ah ta gama gyara dakin ta shiga dakin Abbanta da sallama, ya dago yana kallanta ya ce "Mother" ta danyi murmushi ta zauna gefenshi ta ce "Abbana" murmushi yayi shima yana kallanta ya ce "Alhamdulilah, jiki ya fara sauki" ta ce "Good morning" ya ce "Morning, how are u dear" a hankali ta ce "Banajin komai yanzu Abba, thanks for the care" hannunta ya kama suna shaking, tayi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi, Abba ya ce "Allah ya kara miki lafiya" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta mike tana kallan warmers din dake gefensa ta ce "Abba u haven't eat" ya ce "Yanzu zan gama naci Mamana" daga haka ta danyi murmushi ta fita a dakin ya bita da kallo cike da tausayi. Tana sauka downstairs ta samu Saudatu ta hada mata komai, ta zauna akan carpet ta ce "Sannu da kokari" Saudatu ta ce "Haba dai Anty Rafi'ah, ai indai ke zanyiwa abu zan iya yini inayi ba tare dana gaji ba" Rafi'ah na murmushi ta ce "To banaso kina kirana da Anty, just Rafi'ah pls" Saudatu ta ce "Wallahi bazan iya ba" ta ce "Zaki iya, kin ta6a ganin inda ka cewa wadda ka girma Anty?" Ta ce "Ehh mana, nidai koma menene bazan fasa fada ba, ya karfin jiki?" Ta ce "Yau kam Alhamdulilah, kawai inajin weakness ne" Saudatu ta danyi murmushi ta ce "Dama haka zakiji saboda cikin dake jikinki" Rafi'ah ta dan kalleta ta ce "How do you know that? taya kika san hakan" ta ce "Nima nayi kuma naji" Rafi'ah ta dan zaro ido tana kallanta ta ce "Kin ta6a aure?" Ta ce "Ehh, tin ina shekara 13 aka min aure a garinmu, inaga shekarana 14 da watanni na samu ciki, ina da tsohon ciki Allah yayi wa mijina rasuwa, a ranar daya rasu ranar nima na haihu amma dan yazo ba rai, ni kuma tawa kaddarar kenan" Rafi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallanta ta ce "Subhanallah, Allah ya jikansu" Saudatu ta ce "Ameen, amma tin daga lokacin ban sake aure ba, naci gaba da karatuna na islamiyya har nayi sauka, shine wata kawar mahaifiyata ta samar min aiki anan, nidai shekaruna 19 a duniya, amma wallahi ban ta6a haduwa da mutanen kirki irinku ba, Umminku, Abbanku, kema da Abdul ba wanda ya ta6a min abinda zanji ba dadi, Allah ya saka da alkhairi ya biya ku da gidan Allah" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "Ameen".
Suna zaune suna dan hira aka danna bell, Saudatu ta gyara hijabinta zata bude kofa Rafi'ah ta ce "Wait Saudat, ki fara tambayar waye" Saudatu ta ce "Waye?" Sameer ya ce "Nine" jin muryar namiji yasa ta mike ta dauka hijab dinta akan kujera ta saka sannan Saudatu ta bude kofar, Sameer dake tsaye yayi folding hannayensa ya shigo parlorn yana kallan Rafi'ah ya zauna, itama zama tayi kasa ta ce "Sannu da zuwa" ya ce "Yauwa sannu" Saudatu ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya mai jiki?" Ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta wuce kitchen ta kawo masa drinks da cup sai table water, Rafi'ah dai na kallanta harta ajiye ta bar wajen, a hankali ta dan kalleshi ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya karfin jiki?" Ta ce "Da sauki sosai" ya ce "Allah ya kara sauki" shiru duk sukayi na kusan minti 5, Sameer yayi breaking silent din ta hanyar cewa "Allah ya baki lafiya, jiya da daddare nayi landing, Mother told me all what happened, Allah yasa haka shine mafi alkhairi" a hankali ta ce "Ameen, nagode" ya ce "God knows best Fatima, shi yasan dalilin daya sa hakan ta faru, but i think hakan ya faru ne saboda shi din ba alkhairi bane a tattare dake, may be u will find someone better than Yusuf, so forget all what happened, i'm there for u, insha Allah i will take care of the Baby before and after his birth" Sameer ya karashe maganar yana kallanta, kin dagowa tayi ta kalleshi jin abinda yace is very similar to Jawda's speech, Sameer ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya raba lafiya" a hankali ta ce "Ameen, nagode" mikewa yayi yana kallanta ya ce "I'm going" ba tare data kalleshi ba ta ce "Ko in kawo maka tea?" Ya ce "No, i'm going with this" daga haka ya dauki Fanta daya ya rike a hannu ya ce "Ammi tace sunyi waya da Ummi wai bata nan ko" ta ce "Yes she's out" ya ce "Ohk, i will come back ltr" ta ce "Till u come, Allah ya kiyaye" daga haka ta tura kofar bayan ya fita, hijabin jikinta ta cire ta dauko dan~wakenta akan dinning taci gaba da ci tana kallan TV.