← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 76

Sashe 8

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya sukeyi bame cewa komai ba kuma me kuzari dan haka har rana ta fara ketowa zafi na ratsa su ga babu me takarma a kafa dan haka wahala ta faro sako kai amma duk da hakan babu Wanda yace komai har lokacin.

Wuni guda sukai suna tafiya sai gab da magrib suka fara hango ruwa daga nesa dan haka suka dan sauke ajiyan zuciya kadan Sai a lokacin Ayanah ta kalli kafafun yan uwanta taga kowa kafarsa ya fashe sosai jini sukeyi dan haka tace su zauna su huta.

Guri suka nema suka zauna babu me kuzari a jiki,
Nurat da Zuhrah ne suka kwantar da kansu a kafadunta suna rufe idanuwansu hawaye masu dumi suna gangarowa daga ciki,

Abaas kuwa gefe ya zauna tareda sunkuyar da Kansa yana kafawa qasa jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumburi.

Har duhun dare yayi suna Zaune gurin salla ma a haka sukai da taimama ba ruwa,

Nurat ce me tsoron cikinsu dan haka duhu na qarawa hankalinsa yana sake tashi dan haka dole suka miqe a hakan suka sake bin hanya cikin hudun dare babu motsin komai koda kuwa na dabba ne daman hakan dajin yake shiru babu motsin komai gwanin tsoro da firgita.

Tafiya sosai sukai har dare ya sake tsalawa sosai karfinsu gabaki daya ya qare ga yunwa da azaba Zuhrah Amanta uku a hanya.

Duk wannan tafiyar da sukeyi suna maqale da juna sun kasa sake juna,

Fitsari Nurat tace zatai dan haka suka tsaya ta dan matsa gefe kadan ta durqusa tayi ta gama kenan tana miqewa taji Mutum ya cafkota gabaki dayanta batasan lokacinda ta fasa wani irin mummunan ihu me karfin gaske ba daya saka Sauran kusrawan dake gurin tahowa gurin da sauri suna ihun daya saka fitsari kufcewa Sakina.

Cikin mummunan tashin hankali da tsananin tsoro Su Ayanah sukayo gurin sedai Asamah da sakinah riqe su sukai da karfi suna hanasu tafiya sbd kada Ayi biyu,

Sama kusrawan su shida sukai da Nurat suna dariyar farin ciki suna tsalle tana ihu da wani irin kukan mafi tashin hankalin rayuwanta.

Kwacewa Ayanah ta fara yi tareda bude baki zata kwala kiran Nurat Asamah suka rufe musu baki take suka fara kokawan kwacewa sbd ganin zaa tafi da Nurat batareda an gansu ba dan haka Abaas ya bude baki ya kira sunan Nurat din karfi sbd sunfi son a tafi dasu dukansu koma inane da a dauke dayansu abar saura su rabu.

Cikin rashin Imani kuwa kusrawan suka juyo tareda biyo su Ayanah din wainda da kansu suka fito suna nufar Nurat da gudu suka rungume junansu su hudun suna fashewa da kuka.
#MAMUH
#ROYALTY
#BEST LOVE
#BOYEM
#BOYEM PALACE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

8

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********

************
Wani irin kuka mai tsananin ratsa kunnuwa Ayanah ta fasa itada Nurat a lokaci daya suna rungume juna da tsananin karfin gaske jikinsu na wata irin rawa mummunan tsoron da basu taba shiga ba,

Abaas da Zuhrah ma dukansu kukan sukeyi suna rungume junansu gabaki dayansu kowannensu jikinsa kakkarwa yakeyi musamman Nurat datafi shiga matsanancin tsoron dayake Neman juyar da kanta ita data shiga hannun kusrawan,

Asamah da sakina ma qarasowa sukai da gudu suna kasa barinsu suka rungumesu kowannensu kuka yakeyi sosai sbd sanin rayuwa kuma ta tsaya musu daga wannan daqiqar.

Magana Nurat ke son yi amma yanda jikinta ke fizga bakinta na kasa budewa sbd bata hayyacinta gabaki daya yasa Ayanah dake wani irin kuka mai tsanani itama jikin na rawa sake qanqameta jikinta tana kasa maganar itama,

Hannunta daya ta saka ta sake qanqamo su Abaas da Zuhrah tana ambatar sunan Abaansu da karfi tareda Neman dauki daga ubangiji sbd bazasu iya rayuwan nan me cikeda tsoro ba basuda kowa a duniyar.

Wata irin dariyar Jin dadi me karfi da ban tsoro tareda firgitarwa kusrawan sukeyi suna zagaye su tareda wani irin tsalle kaman sunga nama.

Duk dan Adam din dazai sauke idanuwansa Akan kusrawa saiya shiga tsoro me tsananin gaske sbd kamanninsu da yanayinsu da rahamar Allah ta gama fice wa a rayuwansu sbd girma da yawan rayukan da suka raba da duniya babu tausayi ko Imani ko kadan,
Ganinsu ko mafarki mummunan tashin hankali da tsoro ne sbd Al’adarsu ma da kadai yanayin shigarsu da wasu irin hudan kunnuwa dana hanci dake tattare dasu ga gashinsu da basa Daurewa a sake yake ga wainda basada gashina kuwa wani irin kitso ne me tsoro ga zane a jikinsu da shima alama ce ta kusrawa ga kowace kusra.

Asamah ce ta bude hannuwanta tana karesu dan basu kariya itama jikinta koina rawa yakeyi tana jin wani iri kaman haukacewa zatai sbd yanda zuciyarta da kirjinta ke tsananin nutso a cikin qunci da tabarbarewan rayuwa data samu kanta na halin data saka rayukan da basu adadi tareda maida yara sama da daruruwa marayu,
Tareda saka mata sama da daruruwa rasa mazajensu zasu zamo bayi,
Yaya da iyaye sama da daruruwa sun rabu babu ranar haduwa har abada sbd kowa da inda ya gudu da kuma inda zaa siyar dashi.

Juyawa kanta yaci gaba da yi zuciyarta da kwakwalwanta na sake kasa dauka idanuwanta na rage gani sbd haqqin ran daruruwan mutanen dake kanta,

Rintse idanuwanta tayi tana sake ganin duhu kanta na Juyawa sosai amma har lokacin karesu takeyi da hannuwanta,

Jin kaman zuciyarta na Neman bugawa ta juyo tsoronta da tsananin tausayinta akansu na qaruwa sbd sun riga sun rasa yanci da gata harma da asalinsu tareda rayuwansu batareda sun San yaya duniyar take ba a wajen gidansu,a kuma wajen garinsu,a Bayan ran iyayensu,
Basusan yaya zasu gudanar da rayuwarda babu iyayensu a cikinta ba koda iyayensu na raye bare yanxu da basa duniyar,

Ko a darasin ilimin rayuwa da iyayensu ke musu tareda tarihi da labarun rayuwar dake gudana a duniya wadda baa cikin ANJOM ba baa taba fada musu menene asalin zamowa bawa ba da ukubar dake cikin bauta wadda bakasan karshentaba ko Ka samu yanci wata rana kokuma Ka mutu a cikinta.

Wani irin Jan rikitarwa idanuwanta suka tana saka hannunta daya a kirjinta tana dafewa Ahankali ta kalli Ayanah tareda bude bakinta ahankali ta Ambaci sunanta kafin ta maida idanuwanta Akan Abaas datafi shaquwa dashi tareda tsananin kauna a tsakaninsu me karfin gaske ta qura masa ido wasu irin hawaye masu tsananin ciwo na gangaro mata ta sunkuyar da kanta qasa tana jin rayuwarta kwata kwata bata da sauran amfani.

Dagowa tayi ta kalli kusrawan da sukayo kansu kowannesu na zaro mummunar wuqar da zata yanka Mutum a qanqanin daqiqu fit ta rabaka da ranka.

Lumshe idanuwa Ayanah tayi suna sake rungume junansu dukkaninsu suna samun nutsuwa da saukin a rabasu da ransu su bi iyayensu yafi musu saukin rayuwan da basusan yaya ake gudanar da itaba,
Rayuwar da babu tabbacin ko zasu take ko wahala da gagari zasu yi karshe su mutu a cikin garari dan haka gwara tin a qasar garinsu batareda sun bar garin da gawar iyayensu take ba subar duniyar.

Abaas dayansu ya fizgo da karfin gaske yana Dora wuqa mai tsananin kaifi da wani mummunan fadi a wuyansa zai fizge jijiyar wuyansa da wuqar
Asamah ce da idanuwanta ke cikowa da hawaye masu radadin gaske ta bude baki jikinta na saki tace

‘Inada damar alfarma guda daya tak da khams ya bani a matsayin abinda zaa biyani dashi kuma dukkaninku kun San da hakan’

Cikin rashin Imani Wanda yake riqe da wuqar a wuyan Abaas yace

‘Damarki guda daya ce tak kina fadarta shikenan kin rasa kowace irin dama……

Katsesa tayi muryanta na sake raunana da cewa

‘Kar a kashe ko dayansu shine abu daya tak danake so……

Dukkanin kusra dariya me karfi suna kece da ita kafin babban cikinsu ya kalleta cikin tinatar da ita babban gangancin da zatai wa rayuwarta sbd Ana cika mata wannan buqatar ita rasa nata ran zatai yace

‘Kina sane a dama daya tak da aka baki zaki iya zabar abarki da rayuwarki kitafi duk inda zaki ki Gina sabuwar rayuwa?
Kina sane da hakan?
Sannan Kina sane da idan kika zabi rayuwarsu ke bazaki rayu ba???

Gangarowa hawayen cikin idanuwanta da sukai jajir sukai ta juya sake kallansu babu Wanda jikinsa baya kakkarwa cikin wani irin mummunan halin daya saka zuciyarta sake nauyi,

Abaas ta zubawa idanuwanta idanuwansa na rufe yana jiran barin duniyar kafin ta dawo da idanuwanta Akan Ayanah dake kallanta cikin yanayin da suka fi buqatan mutuwan Akan rayuwar

Zuhrah ce ta iya bude baki da tsananin kuka me ratsa zuciya tace

‘Asamah mun zabi bin iyayenmu dan Allah karki zabi barin mu kema sbd kece wadda a yanzu muke kallan zaki zame mana ido a wannan rayuwar da muke makafi bamusan komaiba dan haka munfi tsananin buqatan komawa ga mahaliccinmu kaman iyayenmu……

Ayanah data kasa magana sbd tsananin shidewan datake sbd tsananin tashin hankali da kukan da hawaye basa fita a cikin dare daya da wuni hawayenta sun kafe kallan Asaman takeyi tana girgiza kai dukkanin jikinta na rawar da bata hayyaci bace.

Rintse idanuwa Asamah tayi ahankali tana bude su Akan su duka tace
Chapter 8 · 0% Book details