← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 76

Sashe 39

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai datai mintina biyu a kwancen tana kallan kofar da sakinah ta fice kafin ta tashi Zaune a hankali tareda ziro kafafunta qasa ta miqe tsaye slippers masu taushi a kafarta ta nufo kofar ta fito sanye da doguwar rigar qasar me kyau black kanta rufe da qaramin Gyale me hade da niqap din dayake da adon sarka me rawa ta zinari sbd tasan da zaa kawo masu dubata sbd zazzabinta amma bata San abinda zasuyi Bayan hakan ba kuma doka ce me karfin gaske babu namijin dazai iya ganin fuskarta tinda ta zama imebētin sultan me BOYEM gaba daya.

Ko data sako Kai a palon Qamshinta ne ya fara cike palon kafin fitowanta data saka likitocin biyu dauke kansu gaba daya daga kallan hanyar datake tahowar,

Tenya ce take kallanta su sakinah ma gabaki dayansu ficewa sukai kansu a qasa zuwa kitchen ayyukansu,

Sakinah hankalinta gabaki daya kwata kwata yana kan abinda zai faru a palon tana tsananta adduar Allah yasa Ayanah bata dauke da jinin boyem a cikinta,

Cikin nutsuwa likitocin suka nutsu suka gudanar da bincikensu Akan Ayanah wadda dukkanin tambayoyinsu ta amsa a sanyaye.

Bayan dan lokaci suna bincike da bin harbawan jijiyanta suka bar bangaren dan tafiya da sample dinta da zaa auna dan tabbatarwa kafin bude baki ga fadar kowane irin sakamako ne.

Ayanah bata buqatan sanin menene yake damunta sbd ba damuwanta bane ta rayu ko sabanin hakan,
Tenya kuwa Miqewa tayi itama ta fice ta aika aka saka mata ido sosai a cikin sirrin dan tsaro da kiyayewa batason kowa ma yasan da duk abinda zaa fada.

Jiran wuni guda tenya tayi tana jiran sakamakon Wanda ya hanata dukannin sukuni da nutsuwan zuciya hankalinta na kan koma menene,
Daga qarshe tenya da kanta ta isa bangaren lafiyyyar clinic din dake cikin masarautar,

Sai dare ta isa batareda barin kowa yasan da inda ta nufo din ba sbd tasan sosai akwai Idon HAILE Akan duk wani motsinta da abinda ya shafi Ayanah.

Ko data iso Kai tsaye babban likitan ne da kansa ne ya zauna suna fuskantar juna ya sauke Numfashi ya koro mata bayani Kai tsaye ciki ne da Ayanaah qarami.

Ajiyan zuciya da Numfashi mai karfi tenya ta sauke tareda kallan likitan Wanda ta ciro silan danyan zinari ta ajiye gabansa matsayin tukuicin zancen sa ta miqe ta juya ta fice tana Jin yanayi na farin ciki da samun nutsuwa dan Kuwa adduarta a yanzu zata sauya zuwa Allah yasa wannan Karan haihuwan LEUL BOYEM ne tazo mai albarka dazai zamo abin alharinta da uwarsa dan kuwa shine karshen baqin ciki da haukar da zata Kama HAILE dan samun namiji a gurin wata macen da ba ita ba yana nufin zarewanta.

Koda tenya ta isa babu Wanda ta sanarwa da maganar cikin imebēti Ayanaah sbd fitar zancen cikin tamkar miqa rayuwar Ayanah ce ga halaka dan haka ta zabi tayi shiru ta Hana kowa sanin cikin saiya bayyana.

Sakinah Jin shiru kwana daya kwana biyu harma kwanaki babu sakon labarin samun ciki ga Ayanaah ya sakata Jin dan sassaucin abinda take ji na tsoro da tashin hankali ta dan kwantar da hankalinta duk da kullum sake sauyawa Ayanah ke yi alaman mace me ciki yana sake bayyana gareta batareda itama tasan cikin ne yake dauke dashi ba.

A haka satikan hutunta suka cika aka fara shirin fara zuwanta tiraka sedai wannan Karan tenya bata bada umarnin anyi mata shiri me karfi ba Wanda hakan ya tado tsoron sakinah sedai kuma indai har cikin ne da Ayanah dole Ayau zasu sani kuka kowa ma dake masarautar zai gane dan bazata qara zuwa ba,

A al’adance duk macen data samu cikin sultan matiqar an tabbatar tenya ce takeda ikon sanar masa idan takai mace kwanan karshe shi kuma daga wannan ranar zai sallamota ne ta hanyar alamar rashin bata tukuicin kwanciya Wanda hakan na nufin ya gama da ita kenan shikenan kota haihu kawai matsayinta dayane ta haifar masa jininsa,

To wannan alamar ce take sakawa kowa dake masarautar yake sanin mace ta samu ciki sai kuma Bayan lokaci nai dan tsayi kafin a fara shirin zabar masa wasu imebēti din,

Tenya duk wani shiri na nutsuwa da qamshi me sanyi na bankwana da tirakar sultan shi tayiwa Ayanah tanajin damuwan sanin cikin da zuwa yanzu kowa zaiyi,

Karfe goma sha Dayan dare suka iso tirakar tasa wadda kowannensu ya tsaya cak inda shine gurin tsayuwarsu,

Silan zinari dayake da adon hoton tafin kafar jariri a jiki tenya ta bude hannun Ayanah ta saka mata batareda cewa komaiba,

Wucewa ciki Ayanah tayi batareda ta bude hannunta ba bare tasan sakon menene amma dai sanin yawancin sakon masarautar da alama a silan zinari suke Aikasa dan haka a sanyaye ta isa dakin Wanda yayi sanyi sosai qamshin sa datai sati uku bata shaqa ba yayi shiga hancinta yana ratsa kanta cikin sanyi ta dan Lumshe idanuwanta t bude a natse kafin ta fara Takawa da sanyinta sautin karar sarkar kafarta dayake daban dana matansa yana tashi a kowane takunta yana shiga kunnensa da sautin yakewa dadi,

Isowa tayi har inda yake Zaune sanye da Riga da wando masu dan kauri farare qal d suka sakasa komawa tamkar matashin saurayi,

Kanta na qasa ta zube qasa ta miqa masa gaisuwanta da muryanta da babu hayaniya a cikinta ko kadan,

Amsa gaisuwar yayi yana kasa dauke idanuwansa daga kanta dan kuwa zuwa yanzu ya gama yadda da koma menene Ayanah na basa nutsuwa da sukuni fiyeda kowa dan kuwa ko yayansa baida Wanda zaice gashinan shine yafi so ko ji a zuciya,

Bayan kujeran mulkin BOYEM yanajin a yanzu ne ya sake samun abinda bazai taba iya bawa wani ko barin yafita hannunsa dan Hak…….

Bai qarasa abinda yake zuciyarsa ba ta dago hannuwanta biyu sama kadan ta bude masa su sakon na bayyana kan idanuwansa kanta na qasa.

Qurawa tafin hannun nata ido yayi batareda y kyafta ba dan kuwa wani abin da bai taba ji ba yaji ya soki kirjinsa yana ratsawa na asalin girgiza da mamaki,

Bai taba mamakin samun ciki ga mace dayake kwana da ita ba sai kan Ayanah GHAZ wadda ya dauke idanuwansa daga tafin hannun nata ya maida Akan fuskarta data dago ahankali itama Jin shiru idanuwansu suka shiga cikin na juna ya tsareta tsaf da idanuwansa yana kasa motsawa,

Duk hadarin dayake cikin samun cikinsa Reno da haihuwansa ya sani Shiyasa sai kakkarfan tsarin Allah suke labari,
HAILE batada imani ko tausayi ko kadan Akan kishi da tsananin cika burin duk abinda take so amman bai taba damuwa ba dan itace macen da ikonta yakai tayi duk abinda take so dan itace uwargida kuma mace mafi daraja a BOYEM kasancewanta matarsa kuma bazai taba goge hakan ba amma kuma bayajin Ayanaah GHAZ zata iya wannan rayuwar hadarin,

Hannunsa ya miqa ahankali Akan tafin hannunta ya dauki silan ya damqe a tafin hannunsa ya bude Baki cikin nutsuwa sosai yace

‘Ina tayaki Murnar daukan jinin BOYEM,
Ina maraba da duk abinda zaki Haifa Ayanah Ghaz.’

Zuru tayiwa idanuwanta akansa sbd kasa fahimtar abinda yake nufi ta kuma kasa bude Baki ta tambaya sedai ta samu kanta a tsananin son fahimtar me hakan ke nufi sbd Wani irin nauyin da kirjinta yayi

Abinda ya fada mata shine abinda ake fadawa kowace macen amma ganin irin dauke wutar datai ya sakasa Dora mata da cewa

‘Ina fatan cikin dayake jikinki ya zamo na cikar burina dana qasata gabaki daya’
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali

[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

36
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******

Wani irin jiri ne ya dibeta me karfin gaske daya sakasa tarota jikinsa yana rungumeta sosai a cikin jikinsa Wanda a yake yaji yana Jin tamkar karfin Mararta datai tudu.

Ajiyan zuciya ya sauke yana miqa hannunsa ahankali cikin rigarta zuwa mararta da taurinta ya tokaresa ya shafi cikin a Karan farko kenan rayuwarsa daya shafi cikin tsatsonsa,

Lumshe ido yayi tareda jan wani Numfashi mai dumi ya bude ido tamkar yana buge a kanta,

Jajir idanuwanta sukai zuciyarta na wata irin harbawan datake nunawa har a kirjinta ya zubawa kirjin ido,

Wasu irin hawaye masu tsananin Zafin gaske ne suka gangaro daga idonta suka sauka Akan fatar hannunsa yana kallo bai motsa ba baice komaiba sai kawai yaji sautin kukanta mai tsananin ratsa zuciya ya fasu ta qamqamesa tana kukan jikinta har wata rawa yakeyi tana cusa kanta a kirjinsa.

Bai motsa ba baice komaiba kukan ne kadai sautin dayake tashi a dakin Wanda ya sakasa tinani Kala daban daban sautin kukan na ratsa kunnuwansa zuwa cikin kansa da babu komai a cikinsa yanzu Bayan na saiya tabbatarda ta Haifa jininsa koda bazai zo da rai ba saiya kuma mata Wani cikin amma tabbas yanason jininta a cikin yayansa.

Kuka sosai tayi a jikinsa har karfinta ya qare tayi lahu dukkanin tinaninta ya toshe babu komai a cikin Kanta empty yake tas,
Chapter 39 · 0% Book details