← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 76

Sashe 11

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abaas da Zuhrah din tare suka miqa hannu ta kallesu tana miqa hannunta ta Kama nasu zata miqe Sakinah tayi saurin riqeta tana girgiza mata kai tace

‘Idan kun zabi mutuwa Akan rayuwa zan biku Nima na zabi mutuwar sedai idan kukai hakan sadaukarwar iyayenku dan kawai ku rayu ta zama ta banza,
Sadaukarwar Asamah ta zama ta banza itama,
Ayanah ki tina su Abaa basu da burin daya wuce ku rayu kota yayane,
Ku tsira kota yaya ne,
Duka duniyar kowa dake gwagwarmaya yana yi dan cika burin magadansa da magabatansa amma ko kwanaki masu yawa baa yiba zaku kashe kanku sbd kasa rungumar jarabawa.,

Idan har jinin iyayenku ne jinin GHAZ yake yawo a jinin jijiyoyin jikinku to tabbas zakuyi kowace irin gwagwarmaya ku jure ku rayu dan tabbatarda burin iyayenku ya cika kun tsira sun rayu kun samu rayuwa da zaku tina baya ya zama tarihi,
Wannan shine ya kamata ya zama sabon Alkwarin jini da duk wani jinin GHAZ zai taso a cikinsa na duk zuriar GHAZ da zasu zo a gaba wato juriya ga dukkanin tsananin rayuwa kowane iri ne ka tsira ka rayu,

Karku manta kune jinin GHAZ na karshe Wanda kuna barin duniya dukkaninku to shikenan jinin GHAZ Yazo Yazo karshe kun shafe a duniya sedai a tarihi idan an ambaceku dan haka Kuyi hakuri Kuyi juriya Kuyi gwagwarmaya kuci gaba da jagorantar GHAZ ku yada zuriar da zata ci gaba da jan sunan GHAZ a duniya.’

Kuka Zuhrah keyi sosai da maganganun da suka shige su amma ita har lokacin tana jin tafi son mutuwar sbd bazata iya rayuwar da dabbobi ma sunfi su yanci da gata da rufin asiri tareda kwanciyan hankaliba,

Kallan Ayanah dake kuka sosai kaman ranta zai fita cikeda da gajiwa take kukan idanuwanta sunyi kumburanda kaman zasu fado su tsiyaye.

Maida kallanta kan Abaas tayi Wanda shima kukan yakeyi sosai hannuwansa na kakkarwa,

Nurat ta juyo itama ta kalla wadda ta koma abar tausayi yanzu sbd bata iya cewa komai zuru tayi da idanuwanta dake bayyanarda tsananin qunci da Neman Hutu na barin duniyar sedai batada tinani na kanta yanzu sai yanda akai da ita.

Itama Zuhrah jin tayi kaman kanta da zuciyarta bazasu dauka ba dan haka ta fara ja da baya tana hawaye.

Miqewa Ayanah tayi batareda tasan tanada Sauran karfinba tayi kan Zuhrah din da sauri sedai Juyawa zuhran tayi tana nufar ruwan da gudu zata fada,

Abaas ne shima yayi kanta da gudu hakama sakinah Ayanah
Sakinah kuwa Nurat ta riqe sbd kada itama ta juye ta bisu ta fada ruwan.

Har Zuhrah ta fada ruwan Abaas ya Riga Ayanah isa gareta ya riqota tana fizge wa tana kuka me karfi tana rokonsu su tafi.

Rungumeta Abaas tayi sosai jikinsa yana bude baki cikin karfin Halin dake zuciyarsa data fara bushewa yace

‘Zuhrah zamu jure,zamu jajirce,zamu tsira,zamu rayu insha Allah zaku ma mu sake amsa sunanmu GHAZ wata ran….

Girgiza kai takeyi tana cewa

‘Aa Aa Abaas bazamu sake amsa sunanmu ba har abada gwara mu tafi dan Allah’

Girgiza mata kai yakeyi shima yana sake daurewa kukan dayake zuwar masa

Ayanah ma rungumesu tayi dukansu tana maimaita abinda Abaas ya fada Akan sun rungumi hukuncin ubangiji duk tsananin tsanani zasu jure zasu jajirce zasu rayu a cikin kowane Hali dadi ko wuya.

Kuka Zuhrah keyi sosai tana girgiza kai a hakan haka har suka fito ruwan suna samun guri suka zauna suna yin shiru tsawon lokaci kafin suka kalli juna suka sake daukanwa kansu alkwarin jurewa da rungumar kaddara tareda kasancewa da juna sbd duk masifa da munin rayuwan da zasu fuskanta idan suna tare da juna zasu jure dan rabu wa da junansu shine mafi muni da girman kaddarar da suke tinanin zai samesu Wanda gwara musu mutuwa Akan hakan.

Fitowa rana ya saka suka miqe suna sake cika cikinsu da ruwan sosai suka bar gurin Bayan sun jiqa kayansu sosai da ruwa har suna tsiyaya ta yanda zasu yi tafiya me tsayi basu azabtu da tsananin Zafin rana da kishirwa ba.

Komawa sukai cikin dajin suna kallan hanyar gabas suka miqa suna riqe hannun juna
Nurat kuma tana hannun Abaas ya riqe hannunta gam cikin nasa.

Wuni sukai suna tafiya har rana ta fadi duhu yayi suka nema guri suka zauna babu me iya numfashin arziki sbd wahalar yunwa da kishirwa.

Dukkaninsu sunyi galabaitar da baa magana dan haka tinda suka zube a gurin babu Wanda ya sake motsi kaman matacci har gari ya kuma wayewa yayi haske.

Numfashinsu fara Neman gagararsu yakeyi amma a hakan suka tashi suka sake bin hanya suna kasa ko riqe juna wannan Karan,

Wuni suka sake yi suna yawo a dajin batareda ma sun San inda suke jefa kafafunsu ba gashi kaman dajin dayake da wani sirri dan baka iya gane gurin fita..

Kwanaki suka dauka suna ragaita a mummunan dajin Wanda zuwa lokacin tini suka fara cin ganyen duk icen da suka samu Wanda yafara maidasu kaman wasu dabbobi,

Kamanninsu sun sauya daga mutane zuwa wasu kalar,
Fatar su ta koma kaman busashiyar dabinon daya fito cikin qasar sahara,

Bakinsu ya bushe ya far fashe jinin dayake fitarwa shi Kansa ya bushe,

Wata irin dauda da qasa tareda qazanta ce kala kala a jikinsu Wanda bushewan da sukai qayau yake rage warin dake tashi a jikinsu,

Zuwa lokacin dukkaninsu sun gama cire rai daga rayuwa harda Sakina kanta me basu kwarin gwiwa wannan Karan mutuwar take fata da son ta dauke su sbd rayuwa dai ta qare musu a inda ko gawarsu basuda me kalla yayi musu fatan rahama sedai tsutsa su cinye namansu iska ya busar da saura sbd ko dabbar da zata cinye namansu a dajin babu.
#MAMUH
#BEST STORY
#ROYALTY
#SLAVERY
#BEST LOVE
#BOYEM

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

11

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********

Idanuwan Ayanah da suka koma manya sbd gabaki daya naman fuskanta daya tafi babu shi sai qashi zalla Wanda Kana kallanta zaka dauke idonka akanta sbd gabaki dayansu haka suka koma babu Kyan gani sbd babban cin kamannninsu da wanda qwarangwal fata ne da dan abinda baa rasa ba sai Sauran rai dayake jikinsu,

Kallan kannenta dake kwance gefenta dukansu kaman gawar dataqi rami takeson yi amma ganinta yayi Raunin da bata iya gane wa sosai dan haka bushashen hannunta ta motsa daqyar yakai kan fuskan Abaas wanda wasu haqoran wahala kawai ta iya Ji a fuskan tasa wainda sune kadai a tsaye sbd babu komai a fuskan tasa idanuwansa sunyi zurfin data kasa iya tantance ramin ido ne ko kuwa ramin bakinsa dan haka ta sauke wani wahalallen Numfashi daqyar tana taba Zuhrah wadda cikinta ya hade da bayanta ta koma halittar da zata iya firgita qananun yaran gata.

Hawayen da babu su ne a jikinsu Ayanah ke kokarin hada wa amma babu yanda zasu taho sbd basu da Sauran ruwan komai a jikinsu sbd fitsarinsu ya dade da komawa baqi qirin sukeyinsa alaman babu Sauran ruwan komai a jikinsu.

Nurat wadda kowane lokaci ranta zai iya fita jikinta ta sauke hannunta akanta tana Jin kanta ba komai sbd gashin kanta data ringa figewa a kwanakin sbd azaba da rashin cikakken hankali.

Rufe idanuwanta tayi tana Rokan Allah ya kawo musu daukin da shine ya kamacesu.

Sakina ta dan kalla daqyar bata gane kamanninta tana fatar ko a Aljannah Allah ya hada su guri daya da Sakina sbd ta zama jininsu koda basu hada jinin gaske ba.

Zafi garin ya sake dauka sosai da tsananin azaba har rana ta fadi suna kwance har duhun dare yayi,

Tsakiyar dare ruwan sama ya sauko wanda da ruwan saman ne daman suke samun sauki a wasu lokutan.

Yanzunma ruwan saman ne dayake sauka kansu sosai ya dan saka wasu daga cikinsu motsawa amma ba wanda ya iya tashi har saida ruwan ya dauke da safe tukuna dukkaninsu suka bude idanuwansu amma babu me iya tashi.

Zuhrah ce kunnuwanta suka fara jiyo mata takun mutane me dan karfi kadan kadan sai ta Lumshe ido tana fatar abinda take Jin da gaske ne dan kuwa suna buqatan koma masu kashe su ne a yanzu suzo su kashe su tinda a yanzu basuda ma karfin yi da kansu.

Hanyar ta qurawa ido daga kwancen datake duk da bata gani sosai gabaki dayansu dishi dishi suke gani ganinsu ya samu matsala wanda kaman illar ganyan da suke ci ne kaman dabbobi.

Ayanah ma ahankali ta fara jiyo takun amma bazata iya Juyawa ba bangaren ta kalla sedai Lumshe idanuwan datai na jiran tsammanin koma menene sbd su yanzu kusan tsoro ya cire daga rayukansu.

Sauran ma dukansu suna jiyo takun da sautin sa ke amsawa a dajin ta nan bangaren da suke,

Sakina ce tafara daga hannu Daqyar tana fatar a hangosu su samu koma wane irin dauki ne.

Shiru shiru baa nufo ta bangaren da suke ba har yamma basu Dena jin hayaniya sama sama ba,

Duhu ya fara harsun cire rai da tsammani ita Zuhrah da Nurat harma da Abaas duka sun some babu me Sauran numfashi a jikinsu.

Sakina da Ayanah ne keda Sauran numfashi amma suma idanuwansu a rufe koma sun bude basa ganin komai se duhu ga kuma dare.
Chapter 11 · 0% Book details