← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 76

Sashe 65

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka Koda ya fito sallar asuba sukai sallah a tare daga nan geamin suka shiga dakin da aka tsara masa dan hakan suka fara geamin har lokacin suna iya ganin fushinsa da bacin ransa bai gama sauka ba dan haka a kiyaye da shirye da kowane shirin suke hakama kaman yanda baice komai gameda tafiyarsu datake a ranarba babu Wanda ya tada maganar sbd a shirye suke da qarasa rayuwarsu anan matiqar baice ga ranar da zaa wuce ba su a inda ya zabi rayuwa acan tasu rayuwar take suma dan haka bangaren tsit yake babu wulgawan kowane bawan da baa nan yake aikin hidimar NUAB ba Wanda ko ruwan shansa basu cika barin kowa na basa ba idan ba su din ba sbd tsaro.

Tenya da Maa sakinah kuwa tinda garin ya waye suke juya yanda zasu isar da sakon sultan ga Ayanah wadda ta tashi da tsananin kulafucin son ganin NUAB sbd tafiyarsa da zaiyi a ranar ya tafi da ita dasu sakinah dan haka Ayau din ma koda bayinta suka gama hada mata ruwan wanka tana tsaye jiran su gama tayi ta shirya dan kuwa haka take Jin tsananin kewan Abaas Wanda a zuciyarta tana barin masarautar take ganin zata hadu dasu.

Karfe tara na safe Ayanah ta gama dukkanin shirinta tana Zaune tana jiran NUAB Wanda ya kasa zuwa inda take dan baisan tayaya zai iya kallanta ba ya sanar mata ya daga tafiyar tasu data saka aranta sosai,
Shi kansa tsoron Wani ciwon ya sameta ko jikinta ya rikice ya saka ya rasa ta yaya zai kalleta,

A Karan farko rayuwarsa da Wani ya sakasa a matsatsen yanayin da komai nasa ya tsaya cak batareda ya kaddamar da danyen hukuncin akansa ba,
Maganar data shafi mahaifiyarsa tafi masa business deal din billions na dollars a rayuwarsa,
Akan lamarin da duk ya shafi mahaifiyarsa baya masa garaje hakanne ya saka sultan yakeson ya quntata masa ta hanyar bullo masa ya nuna masa karfin ikonsa dayake kanta shima.

Karfe sha daya da rabi ya shirya cikin black fendi wears da black geometric shape glasses na tom ford qamshinsa na tashi a hankali ya fito ya tinkari bangaren mahaifiyarsa Aleey na gefensa yana waya a natse shima Akan Wani business dinsu Yaransa biyu ne a bayansa da umbrella sai bayi kusan goma a can Bayan yaran nasa da suke bayin da aikinsu basa Rakiya da tsaro na cikin masarautar Wanda Sarkin bayi ne ya tanadar masa su masu karfin gaske ya aiko a matsayin bayinsa.

Ko kafin ya iso a daidai wannan lokacin Ayanah ta dauko wayarta zata saka kiran NUAB dabai taba kaiwa wannan lokacin bai taho gareta ba hakama a saninta yace da safe zasu wuce amma gashi har rana tayi babushi Wanda hakan ya saka zuciyarta rasa sukuni hankalinta ya fara tashi da shiga firgici.

Tana kokarin saka kiran Sakinah ta kalleta tareda saka hannu ta karbi wayar ta ajiye gefe ta kalleta tareda zama kujeran datake kusa da ita ta sauke Numfashi tana kallanta ta bude Baki zatai magana tenya da itace takeda alhakin isar da sakon ta kalli Ayanah data zuba musu ido zuciyarta na Wani irin nauyi tana jiran Jin abinda zasu fada ta katse sakinah da zubewa gaban Ayanah kanta na yin qasa sbd cike al’adar isar da sakon sultan ga wishimah dinsa ta bude Baki da murya me sauti dake yankar zuciyarta ga abinda zata fada tace

‘Allah ya qara miki lafiya da tsawon rai da zaki sheda aure da mulkin LEUL BOYEM NUAB ALMAZZ me BOYEM da Moscow,
Allah ya qara miki girma da daraja wishmah uwar NUAB,Zakin BOYEM,Sarkin BOYEM,diamond din BOYEM,
Ina fatan Allah ya bakin karfin zuciyar da zata karbi sako me daraja daga me daraja sultan me wishmah da LEUL NUAB ALMAZZ boyem wato sarki YASAR ALMAZ me boyem,
A Daren jiyan sakon me daraja ya iso sultan mai boyem yace a miki albishirin ya maida miki martabarki ta wishimarsa ya maida miki karban kwananki a tirakarsa daga Daren jiyan Wanda Ayau zaki far………

Cikin wani irin sauti da basu taba ji ba a muryar NUAB da basu taba tsammanin ganinsa lokacinba kaman saukar aradu sukaji cikin nutsuwa yace

‘What?
Maa?

Sakinah ce ta dago jiki a matiqar sanyaye ta kalli kofar idanuwanta na sauyawa sbd Wani dandanon zallar daci da bacin rai tareda baqin ciki me tsananin gaske da suka jiyo a muryansa da idanuwansa dayake zarewa glass,

Kafe idanuwansa yayi Akan Maa tenya din wadda ta sunkuyar da kanta zuciyarta na ‘daci itama dan basuyi farin ciki ko kadan da hakan ba amma ba yanda zatai dole ta isar da sakon sultan ga wishmah dinsa a darajance.

Ayanah data dauke wuta a Zaune sbd kwakwalwanta data kasa digesting komai zuwa hankalinta dataji yana gushewa ta dago ta zubawa NUAB din idanuwanta dake sauyawa suka ja ahankali tareda tahowan wasu hawaye masu tsananin zafi a cikinsu ta miqe tsaye tana girgizata Kai da sauti me karfi tafara cewa

‘HAYATEEM Karka tafi Ka barni,
Bazan iya zama idan Ka tafiba..
Kayi mun alkawarin tafiya dani inda zaka mu rayu acan tare,
Sultan zai rabani dakai ne,
Bazan iya rayuwa babu kaiba a kusa dani Hayateem,
Hayateem kada Ka tafi Ka barni kaima,
Baa ya tafi ya barni,Ammah ta tafi,Nurat ta tafi Zuhrah ta tafi Abaas ya tafi kaima zaka tafi Ka barni??

Wata irin rawa da fizga jikinta ya fara yi mai tsanani tana ja baya tana maganar da karfi idanuwana jajir bakinta na wata irin rawa.

Mummunan tashi hankalin tenya da sakinah yayi suka miqe tsaye dukkaninsu suna kokarin nufarta tayi baya da karfi tana kafe idanuwanta Akan NUAB tana maganganun dake tada tsigar jikinsa gabaki daya idanunwansa na yin jajir sbd kallanta tana ficewa hayyacinta Akan idanuwansa yana gani mafi muni na rayuwarsa gabaki daya.

Riqota yayi da sauri yana son bude Baki yayi magana amma Ayau Rauninsa yana Neman bayyana

‘Ya Ammi’
ya furta da Wani irin mataccen sautin daya saka gashin jikinsu tenya tashi suna dakatawa cak jiki mace.

Riqota yayi jikinsa yana kokarin rungumeta amma gabaki daya fita takeyi hayyacinta tana ture sa da karfin gaske tana cewa mutuwa zatayi itama bazata iyaba kowa yabarta itama zata tafi batason zaman duniyar.

Yanda taje maganganun koina jikinta yana fizga da jijjiga ya saka abinda yakeji yana tsananta a jininsa tareda Wani irin mutuwar jiki sbd bai taba ganin mahaifiyarsa a wannan yanayin ba dan haka ya rungumota jikinsa da karfi yana rungumeta ta fasa wani irin kuka me tsananin karfin gaske da tsima zuciya Wanda ya saka su Sakina sake shiga mummunan Halin tsoron dawowan tinaninta tin daga lokacinda ta fara ambatar sunayen ahalinta data bata taba ambata ba a lokaci daya tinda memory dinta ya samu matsala.

Kukanta ya sakasa bude bakinsa da yayi mummunan nauyi shima nasa jikin kakkarwar yakeyi da sautin daya ratsata yace

‘Ammi bazan taba tafiya koina na Barik ba,
Zan rayu guri daya dake kaman yanda nayi miki alkawari,
Zan tafi dake insha Allah ko ba yanzu ba……

Rufe idanunwata tayi tana fasa sabon kukan dayake gigita nutsuwa da rikita jinin jikinsa tace

‘Idan Ka tafi mutuwa zanyi bazaka sake ganinaba Hayate…..

‘Ammi babu inda zan tafi na miki wannan alkawarin matiqar ba dake ba to Hayateem yana nan babu inda zai tafi wannan alkawarina ne gareki Ammi……

Girgiza Kai takeyi tana sake rikicewa sbd wannan Alkwarin dayake yana sake haukatar da kwakwalwanta ne sbd haka ya fada a farko zai tafi da ita amma yanzu a karo na biyu zai sake tafiya yabarta kaman yanda kowa ya barta dan haka kwakwalwanta tafara kokarin dawo mata da memories dinta sa suke buga kwakwalwan tata gangar jikinta fa lafiyarta na kasa dauka fizga tafara me tsananin gaske tana Wani irin Ihun da batasan tanayiba wasu azababben radadin dayake Dakatar da bugawan zuciyarta suna dawo mata tana tsananta ihunta daya saka NUAB qanqameta a jikinsa wasu irin hawayen da tinda yake duniya basu taba zuwa idanuwansa ba suna taruwa a cikin manyan idanunwansa da sukai mummunan ja yanajin yakushinta da dukanta na sauka jikinsa ya Lumshe idanunwansa yana sake rungumeta da kyau sbd taci gaba da illatasa Akan ta illata kanta.

Sakinah ma kuka takeyi sosai Wanda ta manta rabon dataisa sbd clearly memories din Ayanah dinne suke kokarin dawowa baqin ciki da quncin rayuwanta zai dawo kenan Wanda yanzu zuciyarta bazata iya dauka ba sbd girma dayazo gangar jikin batai karfin daukan baqin ciki da quncin rayuwar dasuka dauka ba abaya.

Bangaren tsit yayi gabaki daya kowa ya shiga Wani irin sanyi da tsananin tashin tsigar jiki musamman bayinta kaf da suka koma kofar shigowa suka jeru kansu a qasa cikeda dacin zuciya da mutuwar jiki.

Cikin wani irin mummunan yanayi NUAB yace Maa tenya ta sanar da Aleey yana buqatan manyan likitocin qasar boyem cikin awa daya zuwa biyu a cikin masarautar.

Labarin abinda yake faruwa take ya isa kunnen sultan Wanda zuciyarsa ta sosu da Wani irin daci me kaifi amma bai nuna ba saima kiran likitanta da shi kadai ya yadda dashi akanta kuma shine mai bata kowane irin magani Akan umarnin sultan din.

Koda aka kira likitanta labarin zaucewanta da ciwonta ya isa kunnuwan kowa dan haka su HAILE dake cikin jimamin baqin ciki har lokacin suka dan samu sassauci suna dasa sabon zaman jiran labarin cikawarta sbd tsananin gaske jikin nata yayi.

Kamar abinda zuciyarsa zata iya jikin nata ya fara sai gashi a lokaci daya cikin mintinan da basu gaza uku ba ta fice hayyacinta tana rasa numfashinta gabaki daya Wanda hakan ya saka kowane motsi ya dauke cak masarautar sbd kokarin ceto ranta da ake Neman likitoci suyi da gaggawa.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

60
Cikin qanqanin lokaci Aleey ya fara zuba kwararren bincikensa na Neman manyan doctors da suke qwararri a qasar boyem din gabaki daya,
Chapter 65 · 0% Book details