← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 76

Sashe 12

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsakiyar dare sosai Ayanah itama ta some gabaki daya bata numfashi sakina data rage sama sama taji magana akansu Ana cewa

‘Muna buqatan hada wa dasu tinda sunada Sauran rai idan anje can zasu farfado tinda kams yace duk wani dan Adam koma dabba ce idan har tanada rai a tattaro a kawo masa sbd yaune ranar mu tanada qarshe a wannan nahiyar Bayan tsawon shekaru idan muka tafi yau har abada munbar nan tinda a yanzu babu gari anan sedai a tarihi kuma.,

Daukansu sukai dukansu tsaf suka bar gurin dasu suna dorawa Akan dokuna masu karfi bakyan gani suma sbd abubuwan da duk suka Shafa musu da adon ban tsoro.

Suna barin gurin itama sakinah ahankali numfashinta ya tsaya bata sake sanin inda take ba.

Mutane sosai suka tattaro a dajin duk sun galabaita wasu kuma sun mutu harsun bushe wasu kuma suna gap da mutuwar wasu kuma macijai sun kashesu wasu kuma sun zare sbd gane ganen Masifa hadda jinnu.

Fiyeda Rabin tarin yawan rayukan garin ANJOM sun kashesu dan haka wainda suka mutu sunfi wainda suka Kama sosai dan haka basu wani samu yanda suke so ba Shiyasa ya bada umarnin a sake shiga dajin da zagayensa a kamo wainda suka tsira sbd ya samu tarin bayin da zai siyar wannan Karan su haura daruruwa dan yanada wasu tarin bayin dasuka safaro daga nahiya daban daban a cikin jirginsa me kamar gari guda.

Bayan gari ya waye har rana ta keto tukuna suka samu gama hada bayinsu a cikin bangarensu daban can qasan jirgin wanda kowace bawa kafafunsa a daure suke da kaca hannuwansu ne kadai a sake,

Su Ayanah da ire irensu da suka gama lalacewa mutuwa kawai suke jira daban aka ware su Ana zuba musu ruwa duk bayan dan lokaci.

Yamma sosai kusrawa suka daga daga nahiyar gabaki dayanta har abada sbd basa maimaicin zuwa gari komai nasarar da suka samu akansa,

Sun dauki shekaru a nahiyar ANJOM din wanda daga karshe sun samu abinda suke samu dan haka kai tsaye daga nan nasararsu da cikar burinsu zai cika sbd wainnan bayin na kaiwa MASARAUTAR BOYEM ne,
Masarautar da duk suka samu ta karbi bayinsu to tabbas burinsu ya gama cika na duniya.
Masarautar da babu kamarta a iko da tarin mulki da arzikin dayafi na kowace Masarauta tarihi,

Idan har BOYEM ta karbi bayinsu to tabbas zasu shiga cikin littafin tarihi da ko Bayan shudewansu zaa San kusra.

Jirginsu ahakali ya daga daga nan yana keta wa tareda Kama hanyar ruwan da zasu tsallake sama da nahiya hamsin kafin su isa nahiyar BOYEM.

********* tafiya me nisa akai ta kwana da wuni baa gama fita nahiyar dajin ANJOM ba wadda a qalla sai sunyi kusan sati kafin su fita dajin.

A wannan kwana da wunin babu wanda ya farfado a cikinsu Ayanah saida aka kuka wuni tukuna suka fara farfadowa shima sbd ruwan da aketa zuba musu ne masu tsananin sanyi.

Suna bude idanuwansu cikin Ayanah ce ta fara bude ido taga inda take cikin wani irin rikitaccen karfin da baifi ma jaririn rago ba ta yunkura tana tashi amma bata iyawa sosai,

Sunan Abaas tafara ambata cikin dan karfin datake dashi tana dudduba gefenta dataga mutane barkatai sama da Dari duk wasu a kwance.

‘Zuhrahhh,Abaas,Nurat,Sakinah……..

Haka ta ringa jerosu tana kiransu jikinta na Wani irin mummunan rawar tashin hankali.

Zuhrah ce ta fara jiyo Ayanah din da sauri itama t bude idanuwanta tana kwala sunan Ayanah din da dan karfi hankalinta a tashe ko gani batayi ta miqe tana kokarin takawa ta kife sbd kacar dake kafarta.

Bude ido tayi a inda ta fadi sai idanuwanta suka sauka Akan Abaas cikin sauri ta cakumosa tana kwala kiran Ayanah.

Ayanah gurin ta rarrafo ta iso suka rungume juna da karfin gaske suna jin sassauci.

Nurat suka fara kira itama tareda sakina sai kuwa gasu sun gani a guri daya take suka rungume juma kaman Ana partyn ‘yayan aljanu sbd yanda suke hada qasusuwan jikinsu suna rungumewa.

Can Kurya suka rakube inda baida haske sbd basason Abaas na bayyana sosai kada tsautsayi yasa a gane duk da bazaka taba kallansa kai tsaye kace ga ba macen bane suka maqale juna a zazzaune kowannesu da kaca a kafansa.

Tsoro ne zuciya da gangar jikinsu sbd sun gama tabbatarda sun Riga sun zama bayi,
Sun zama bayinda har abada basu yancin rayuwarsu sai yanda akai dasu,
Sun rasa sunansu,sun rasa asalinsu rayuwa kuma yanzu sedai wadda aka zaba ko hukuntar musu.

Bude kofar qaton dakin da suke akai daga sama kofar take.

Kallo wanda ya bude kofar yayi musu tsaf kafin ya fara Jeho musu daurin gayar tuwon alkama da akai da nono.

Masu dan karfin cikinsu take suka fara ruguwan Abinci suna tura Bakinsu cikin tsananin yunwa da ficewa hayyaci.

Sakinah ma cikin karfin Hali ta yunqura tana wawaso abincin tana jefo musu take jikinsu na rawa suka fara sararsa suna Turawa Bakinsu hannuwansu na rawa.

Zuhrah dataji kaman bazata iya tsayawaba yake itama ta rarrafa ta fada cikin wawason tana Turawa bakinta a haukace.

Abaas ma fadawa yayi hakama Ayanah da Nurat
Take suka zama kaman mahaukata kowa wawa yakeyi yana Turawa bakinsa a haukace.
#MAMUH
#BEST STORY
#BEST LOVE
#ROMANCE
#ROYALTY

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

12
A cikin Hali na wawason suka ringa Turawa Bakinsu ko taunawa basa yi hadewa kawai sukeyi yana wucewa maqoshinsu da wani irin karfin gaske,

Wani irin kuka hanjinsu keyi na samun abinda suka dade basu samuba wato abinci,

Danne juna ake yi sosai Ana yiwa juna rauni da hakan suka samu suka cika cikinsu sedai kusan dukkaninsu sun samu rauni dan haka suka rarrafa gefe suka rabe suna dunqulewa sbd tsananin ciwon ciki daya taso musu.

A kwance suka wuni ba lafiya sosai sbd ciwon ciki da lafiyarsu da daman babuta yanzu,

Tsakiyar dare haka aka sake zuwa aka kawo abincin Ana jeho musu suna wawaso sedai wannan karan ba kowane ya iya tasowa ga abincin ba sbd kusan duka dakin basa da lafiya dan kuwa duka kusan ciwon su daya ne ciwon ciki sbd dade wa me tsayi ba abinci,

Zubewa suke son yi kwance su jujjuya ko azabar ciwon cikin zai rage amma dakin babu gurin da kowa zai samu ya kwanta sedai suyi rayuwar zama a cikinsa ko bacci sedai kayi daga Zaune.

Dan haka su Ayanah babu Wanda ya iya zuwa cin abincin tsakar Daren se Nurat data fada cikin masu wawan tayita ci da hauka itama sbd rashin cikakken hankali ne kuma duk anji mata ciwo sosai hada bakinta aka fasa yana jini suna kallo babu me iya motsawa saida ta koshi dan kanta ta dawo cikinsu.

Kwantar da kansu sukai a kafadun juna suna sake lafewa jikin juna da babu wani sauran taushi na tsoka sai qashi amma su a gurinsu hakan shine mafi nutsuwa da kwanciyan hankali Jinsu a jikin juna,

Amai wasunsu suka fara wanda ya hargitsa numfashin dasuke shaqa a gurin,

Amai sosai kowa yakeyi haddasu Ayanah din saida dukansu suka galabaita amma a hakan baa bude su ba saida safe gari ya waye sosai aka bude su haka aka ringa zubo musu ruwa masu yawan gaske daga sama Ana wankesu kaman dabbobi,

Bakinsu suke budewa ruwan na shiga har sukasha sosai kafin ruka zauna ruwan na dukansu da ake zubowa har jikinsu ya wanke tas.

Kowa saida jikinsa ya wanke kafin aka fara Fiddosu daya bayan daya daga dakin ana Jere su a fili.

Babu me iya miqewa tsaye sosai sbd yunwa da wahalar data gama cinyesu,

Hasken sararin samaniya suke kalla yana kashe musu idanuwa sbd duhun da suka fito cikinsa,

Kirgasu aka fara yi Ana daya bayan daya Ana raba maza daban mata daban Wanda anan hankalinsu ya tashi tsoro da fargaba suka shigesu Ayanah ta miqa hannu cikin na Abaas da dukkanin jikinsa yake rawa sbd fargaban kada a ganesa,

Su duka rawa jikinsu keyi dan Ana gane Abaas mutuwa ce tahau kansa,

Qanqame hannunsa Ayanah tayi shima qanqame nata tayi Zuhrah kuwa mannewa tayi a jikinsa itama tana riqe sa suna kokarin hana bayyanar tsoronsu da fargabansu.

Shi Kansa Abaas zuciyarsa cikin wani mummunan Hali take na halin da zasu shiga idan asirin hakan ya tonu.

Duk Wanda aka Kirga sai an masa sheda a gefen hannunsa da wani karfen wuta.

Ana zuwa kansu Nurat aka fara fizgo wa aka kirqa baa tsaya komaiba aka manna mata karfen wuta a gefen hannu Wanda ya sakata qwalla wata gigitacciyar qara tana zubewa a gurin.

Cikin firgita Ayanah tayi kanta zata tarota tayi mummunan kife wa kanta na buguwa da katon drum din ruwan dake gurin Wanda ake watsawa duk Wanda ya sume gurin ruwa sbd azaba.

Wani Juyawa kanta ya ringa yi sbd bugawan da yayi bata dawo hayyacinta ba taji saukar azababbiyar azaba Akan gefen hannunta Wanda ya sakata somewa a gurin itama.

Motsawa Abaas yayi da sauri yana yin kanta itama shima ya kife sbd sarkan dake kafarsa hakama Zuhrah.

Anan aka mannawa kowa tasa Shedan cikin azaba suka dunqule suna fidda Wani irin zufa Zuhrah saida ta yanka Wani irin Ihun azabar da bata taba jiba,

Abaas duk tsananin azabar dayaji rana ratsa jini,tsokar jiki,qashi da kwakwalwansa kasa ihu yayi sbd Alkwarin da sukaiwa juna na har abada idan basu fita wannan ukubarba bazai taba magana aji sautinsa ba na namiji dan haka daga lokacinda ya aka saiya jinsa zuwa na mace ya koma kurman da baya magana sedai nuni.

Wasu irin hawaye masu Zafin radadi a ido da zuci ne suka gangaro masa na tsananin azabar dake ratsashi gashi shi ya kasa somewan.

Bulala aka daga me kaurin gaske ta fatar dabba aka zabga masa yayi daurin rintse ido numfashinsa na sarkewa akace ya tashi.

Da rarrafe ya koma gefen wainda akaiwa Shedan numfashinsa har lokacin na kokarin yankewa hakama yanason fasa kukan azabar dake ratsashi amma fitan sautin kukansa zai bayyana sautin muryansa datake da dan kauri ta maza dan haka haka yaci gaba da danne azabar yana hadiyewa jikinsa na wata irin muguwan rawa.
Chapter 12 · 0% Book details