← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 76

Sashe 58

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu bata lokaci Kai tsaye aka wuce dasu bangaren nasa me girma Wanda yake part guda mai tsari da kyau,
Duk da baya nan babu shekarar da baa sauya furnitures da komai na bangarensa sbd haka doka da kaidar take,
Komai na sauyin da ake masa ahankali ahankali yana tafiya ne da cigaban zamani da ake samu har zuwa yanzu da aka zuba duk wani luxury na rayuwa da zai basa Hutu da nutsuwa isasu,

Komai a tsare yake da duk abinda zai saka yaji kaman yana gidansa na Moscow kawai dai yar qura ce sosai itama a take Sarkin bayi ya fara bada umarnin a fara gyara.

Dakatar dashi Aleey yayi cikin nutsuwa da buqatar full control na kulawa da komai daya danganci lamarin LEUL komai qanqantarsa,

Babu abinda babu a Masarautar BOYEM na Jin dadi da biyan buqata dan haka take Aleey ya bada umarnin a fara sauya komai dake bangaren a cikin kankanin lokaci dan haka ba bata lokacin Sarkin bayi ya saka a fara fidda Kayan a fara shigo da wasu da suka fisu komai.

******Sultan YASAR a daidai lokacin da sautin qarar dawowan magajin dayayi shekaru yana jiran wannan ranar ta dawowansa a wannan lokacin wayar sa ne da wishmah ayanah ghaz wadda a tare sautin ya shiga kunnuwansu ya isa ga zuciyarsa yana sanyayar da wani gurbi me girma da yayi shekaru a zuciyarsa,

Ahankali sautin yake sake ratsashi ya rufe idanuwansa masu kyau da kwarjini yana jan wani Numfashi me dumi ya saukesa a hankali tareda bude idanuwansa Akan fuskar Ayanah dake bayyane kan screen dinsa shiru ta zuba masa ido a sanyaye bata iya cewa komai.

A natse cikin sanyin nutsuwa ya sauke ajiyan zuciya datake dauke da shirin zartarwa da shirin fuskarta abubuwa da dama a masarautar da wainda suke cikin masarautar dan kuwa wannan ranar yake jira Wanda NUAB ALMAZZ zai kawo kansa masarautar da kansa amma kuma fitarsa da kansa ya rasa kenan saida umarnin sa dan kuwa shine yake riqe da cokalin juya rayuwarsa yanda yaso har sai ya cika masa burinsa daya dauka akansa tin daga ranar daya diro duniya,
Burinsa daya saka ya banzatar da abinda yakeso fiyeda komai da rayuwarsa.

Kallan Ayanah yayi a natse ya Lumshe ido akanta ya sake budesu akanta kafin ya bude Baki cikin mulkin dayake yawo jininsa shima da sautin daya shigeta yace

‘HAYATEEM dinki Zaki me BOYEM ya dawo gareki a matsayin cikakken namijin da BOYEM ke buqata’

Motsa idanuwanta tayi akansa tana Jin maganar tasa ta sauka cikin hankali da tinaninta harma da gangar jikinta dan haka ta motsa tana tashi Zaune da kyau duk da bata karfi ko kadan sbd rashin lafiyan datake cinta,

Juya kanta tayi ahankali zuwa kofar ficewa bedroom din nata datake ciki daidai nan sultan ya kashe wayar yana jinginar da bayansa ga lafiyayyar kujeran dayake Zaune ta bedroom dinsa tareda dake rufe idanuwansa ahankali zuciyarsa na yin dum tareda shiga tinanika da dama.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

53
Ahankali tafara Takawa tana nufar kofar bedroom din nata idanuwanta na kafe kofar da idanuwanta tanajin jikinta na qara rasa karfinsa da kuzari,

Duk takunta daya nauyi kirjinta qaruwa yakeyi ta daga hannunta da baida karfi ta Dora a kirjinta tana dafe sa sbd kaman gangar jikinta bazata iya daukan nauyinba Wanda tsawon shekarun tana jinsa amma Ayau yayi tsananin da jikinta ke sake sakewa ta isa kofar ta zubawa hannun kofar idanuwanta da sukai jajir a take batareda tasan menene takejiba a yanxu kuma,

NUAB kuwa tinda ya doso bangaren bayin dake hanyar gabaki dayansu suke zube qasa kansu na yin qasa dan idanuwansu basuyi darajar da zasu kallesa ba dan haka ko motsi me sauti babu me yi tsit hanyar ta dauka badan babu mutane ba Sedan tsananin bada girma ga jinin BOYEM.

Tinda ya tinkaro din shima kowane takunsa dawo masa da kowane Taku da yayi a ranar barin masarautar yake,dawo masa da takun da yayi a ranar daya rabu da mahaifiyarsa,rayuwarsa sanyi da hasken idaniyarsa wadda se yau ze sake haduwa da ita,

Babu hanyar da zata isar da shi bangaren mahaifiyarsa ko daya data bace masa duk da akwai manyan gyare gyare da sauyi da aka samu me yawa amma dai mahaifiyarsa na nan inda ya barta dan haka babu jiran komai Kai tsaye gurinta yake nufa.

Koda ya iso kofar bangarenta dayake dauke da sunan wishmah Baro Baro a jiki wani irin Numfashi me sanyi ya sauke yana dawo da kallansa kan Maa sakinah datake fitowa a hankali cikeda mutuwan jiki da mamaki idanuwanta na sauyawa da wani irin kallan datake masa zuciyarta na sake narkewa dan kamannin jinin GHAZ dayake bayyane a fuskarsa musamman Abaas Wanda yafi Kama da Ayanah sak dan haka kasa cigaba da kallansa sakinah tayi tana qasa da idanunwata hawaye na taruwa a cikinsu,

Maa tenya ma a sanyaye take fitowa dan tarbansa a matsayinta na jakadiyar Amminsa dan haka saukar da idanuwanta qasa tayi daga kallansa tana jinin Wani irin girmammen farin ciki da mutuwar jiki a lokaci daya dan haka bude Baki tayi zata fara gaisuwa da kirarin dayake dolenta…..

Katseta yayi Kai tsaye da muryansa data saka bayin dake bangaren sake Shan jinin jikinsu kansu a qasa,

‘Na dawo Maa’ ya fada a natse Kai tsaye yana kallansu su biyun zuciyarsa cikeda kauna da girmansu,

Tenya ce kauna da matsayin dayake dashi a cikin ranta ya danne matsayinta na jakadiyar sa data mahaifiyarsa ta dago tana fidda Wani murmushin farin ciki mai sanyi tace

‘Barka da dawowan me BOYEM da kansa,
Barka da dawowan Hayateem me zuciyar uwa da uba,
Barka da dawowan Zakin mazan boyem,
Barka da dawowan me jinin boyem da ghaz,
Barka da dawowan magajin asali na BOYEM,
Barka da dawowan LEUL me uwa uku’

Numfashi kawai ya isa saukewa yana kallan Maa sakinah da adduoin tsari kawai take jero masa a zuciyarta da ko bata bayyana ba ya sani haka take ita koyaushe bakinta a cikin adduar basa kariya da tsari daga kowane Sharri take kuma baa fili ba,

Ciki suka juyo suna qarasowa suna gaba yana bayansu dan yi masa iso ga inda mahaifiyarsa take,

A babban palon suka tsaya dukansu suna basa hanyar wucewa palo na gaba shi kadai dan isa ga mahaifiyarsa,

A natse ya wuce ya isa kofar ya saka hannunsa ya bude tareda saka kafarsa ciki idanuwansa na dagowa kallan kofar dakinta data bude itama tana fitowa da tsananin sanyin kafafu idanuwanta da sukai ja suna sauka akansa batareda ta kyafta ba

Shi kansa idanuwansa jajir suka a lokacinda ya kafeta dasu yana mata kallan da kowace gabar jikinsa ke amsa tsananin kaunar dayake mata.

Kasa motsawa tayi daga inda take cak duniyarta na Wani irin Juyawa sbd kasa yadda da abinda idanuwanta ke gani,
Da gaske ne NUAB dinta ne a gabanta kokuwa ire iren gizon da yake mata ne shi da Abaas,

Shi kansa mutuwar tsaye yayi a gurin dayake yake din yana kallan kowane yanayi da mahaifiyarsa ta koma Wanda hadda manyanci dayake nuna tsufa Yazo a tattare da ita ga ciwo fa qunci da damuwa da kadaici tareda rashin cikakken tinin kanta dan haka kan idanunwansa suke sake yin ja radadin rashin lokutan mahaifiyarsa da aka rabasa dasu tin kuruciya suna dawo masa dan kuwa an hanata yarintar ‘danta kaman yanda aka hanasa yarinta a gaban mahaifiyarsa,
An hanasa samun kulawa da tattalin a lokutan ciwonsa da baqin cikinsa kaman yanda kowane ‘da yake samu daga mahaifiya ko mahaifansa,

Shi shikadai yake ciwo yayi jinyar kansa ya kula da kansa ya tsayawa kansa yayiwa kansa komai tamkar marayan da baida uwa baida uba baida gata,
A lokutan ciwo mai tsanani da dama yayi kukan rashin mahaifiyarsa da dumin jikinta kadai zai iya basa warakar dayake nema da sassaucin kowace irin azaba amma duka an hanasa samun hakan an hana mahaifiyansa samun basa hakan daga karshe dai Bayan shekaru Ayau Allah ya hadasu haduwan da mutuwa ce yanzu kadai zata rabasa da ita badai kowane ‘dan Adam ba komai matsayinsa kuwa a duniya.

‘HAYATEEM’ bakinta ya bude ya furta a hankali cikin wani irin sautin daya saka gabaki daya tsigar jikinsa tashi ya tako bai tsaye komaiba ya janyota jikinsa ya rungume da Wani irin karfi yana rintse idanuwansa da har wani radadin yaji suke masa.

Sake ambatar sunansa tayi da sautin daya sake tada duk wata tsigar jikinsa tana Qanqamesa ta fasa wani irin kuka mai qarami da sanyayar sauti tana Jin nauyin kirjinta yana fadawa qasa ahankali ta sake qanqamesa tana ambatar sunansa.

Dagota yayi ya Kama fuskarta da tafukan hannuwansa biyu yakai bakinsa tsakiyar kanta yayi kissing cikeda tsananin kaunarta ya sake juya gefen fuskarta yai kissing ya dago hannuwanta duba biyu yayi kissing kowanne ya sake rungumeta jikinsa tsamtsam yana Jin kaman bazai taba iya rayuwa ba daga ranar da wani mummunan abu ya sameta dan itace kuzarinsa kuma itace weakness dinsa dazai iya bada komai nasa da kansa akanta.

Kuka takeyi sosai tana Jin zuciyarta kaman zata fashe da tsananin kauna da son ‘danta Wanda bata taba ji a ranta zata gansa a gaban idonta ba,ta cire rai daga ganinsa har rayuwarta ta fita tabarta,
Da kewa da radadin rashin sa take kwana take tashi tareda wuce kowace daqiqar rayuwarta amma bakinta kaman an riqe bata taba iya cewa ya dawo koyaushe sedai kada ya dawo bama zata iya tina yaya bakinta ya iya furta masa tana son dawowansa ba kuma duk da ta furta din bata saka ran zuwan nasa ba bare ganinsa ba dan haka take Jin Wani yanayi na tsananin farin cikin rayuwarta a karo na farko Bayan shekaru masu yawa cikin qunci da baqin ciki Ayau ruhinta ya dandana dandanon farin ciki da samun abinda zuciya ke so dan haka take sake qanqamesa da rashin kuzarin datake fama dashi tana rufe ido sbd kuka.
Chapter 58 · 0% Book details