← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 76

Sashe 73

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Meya ke faruwa,
Ina Abbu??

Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta.

Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa.

Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta.

Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa.

Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi.

Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba.

Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shine gatan ayshahh da kuma zai samu yancin zuwa Neman yan uwansa da sune kadai rayuwarsa ya saka yake sake tattaro karfinsa yana cigaba da Wani irin gudun da kafafunsa ke fidda jini sosai amma bai tsayaba dan basu tsira ba.

Gudu sukeyi har kusan asuba hakama karfinsa ya kare daqyar yake iya daga kafa sbd galabaita da jininsa daya fara qasa da kuma wata irin azababbiyar ciwon kirji amma hakanan yake dagewa yana daga kafa.

Koda suka isa wani garin dayake daga shi sai inda boukar din tace suje anan suka samu suka tsare wa wainda suka biyosu amma duk da hakan bai tsayaba dauketa kawai yayi ya Kama hannunta tamkar wadda bata gani haka ya ringa Janta ba karfi a jikinta ko kadan.
Tafiya me tsayi suka kuma yi kafin suka isa garin dayake bakin ruwan da zasu tsallaka Anan dinma basu tsaya ba cikin wata gona suka boye yayi sallah a galabaice kafin suka fada jirgi suka bar nahiyar kwata kwata.

Tafiyar wuni guda sukai kafin suka isa inda zasu din suka fito jirgin tareda barin bodar bakin ruwan wadda sai anan ne Abaas ya gane garin da aka siyosa ne dan haka ya sake riqe hannunta gam suna kutsa mutane suna shiga cikin garin sosai Wanda yake a cike tamkar kasuwa koina hidima akeyi.

Wani qaramin gidan baqi da yan gudun hijira ya isa dasu suka zauna Bayan ya tsaya a hanya ya siya mata gasashiyar fulawa da zuma.

Suna Zaunawa ta cusa kanta cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana fasa wani irin kuka mai tsima zuciya koina na jikinta na jijjiga da tsananin quncin da batasan haka radadi da zafinsa yake ba.

Shiru Abaas yayi a gefenta idanuwansa jajir yana Kurawa ruwan dake mamaye da bakin bodar ido zuciyarsa na yanka shima sbd anan ne aka rabasa da tasa rayuwar,
Anan ne ya rabu da wainda suke rayuwarsa,
Anan ne komai na rayuwarsa ya qarasa Juyawa harzuwa matakin dayake yau akai na rayuwa da bulayi cikin duniya shi kadai babu kowa acikinta.

Radadin azaba me tsanani kafafunsa keyi Wanda ya ke sakar masa da zazzabi me Zafi amma bai damuba shiru yayi ido jajir Akan ruwan.

Kuka tayi Wanda saida ya qarasa cinye karfinta kafin tayi shiru tana Kurawa hanyar ido itama batareda ta iya cin abinda ya bata dinba.

A gurin suka kwana Zaune cikin mummunan halin daya tsananta yanayinsa dama nata datake wata rawar sanyi dan haka ya cire rigar jikinsa ya rufa mata Akan nata Kayan da babu ko kallabi a kanta gashinta a bude yake a sake sbd yanayin da suka fito.

Koda gari ya waye daqyar sukai sallah a gurin suka tashi Zaune suna sake gadin hanyar da duk masu isowa,

Duk yanda yayi da ita taci Wani abin qi tayi gashi tayi Laushi sosai ta fita hayyacinta kawai mahaifinta take son ganin ya taho din.

Haka suka wuni har rana ta Kuma faduwa babu boukar ba labarinsa,

Zuwa lokacin dagashi har ita daqyar suke Numfashi dan haka Akan dole sukaci abinci sbd suna Neman karfin cigaba da jiransa har ranar daya taho.

Wani wunin suka kuma yi ba labarinsa haka suka kuma kwana,
Ahankali ahankali kwanakin suka ringa tafiya ba boukar ba labarinsa su kuma sun kasa cire tsammani dan haka basu iya tafiya koina ba haka su kaita zaman jira a bakin bodar wadda tin baa Ankara dasu ba har aka fara ankarewa dasu Ana musu kallan mata da miji marasa hankali sbd yunwa da wahalar data Kama jikinsu take fara bayyana dan kuwa basa Wani iya cin abinci suna cikin tsananin damuwa da baqin ciki tareda rashin sanin inda zasu.

Ganin an fara saka musu ido ya saka suna cika sati shida a gurin Abaas ya tattarata suka bar qasar sbd Wani jirgin na tahowa Wanda zaiyi gaba binsa sukai sbd a yanzu tafiya Neman yan uwansa zai tafi dan haka a qasar datake gaban wannan zai fara tinda daga nan gaba akai dasu Ayanaah.

Tafiya sukai ta kwanaki a jirgin kafin suka isa qasar dake gaban wadda suka Baro,

Isarsu qasar dole anan bakin boda ya samu aikin wahala Wanda zaa ringa biyansa dan yana buqatar kudin dazai nema yan uwansa bazai taba dukiyar Ayshaah ba a gurin nemansu,

Gida suka samu Wanda ake biyan hayar daki daya ya biya hayar ya saka ayshan a ciki shi kuma yana kwana a kofar dakin.

Rayuwa a qasar qunci tafara yi musu sbd yanda ake qyamarsa ganinsa namiji da Kayan maza amma yan kunnen mata ne a kunnensa wainda ya kasa cirewa sbd Ayanah ce ta saka masa su da hannunta bazai iya cirewaba.

Ita kanta ayshahh tsangwamarta mutane suka fara yi sbd tana tareda shi babu aure a tsakaninsu dan haka rayuwa tayi mata qunci da nauyi bata cikin kowace irin walwala bare farin ciki dan haka suka bar garin suka koma can quryar qasar Wani garin suka fara rayuwa shima ahankali ahankali zaman yakasa dadi sbd qabilanci na qasar sam basason baqi dan haka dole suka tattara suka sake sauya guri Wanda duk inda sukaje kaman mahaukaci haka Abaas ke Neman yan uwansa.

Shekara kusan guda da rabi sukai a qasar suka barta gabaki daya zuwa qasa ta gaba Wanda itama aikin wahalar gaske yakeyi wanda yake cin lafiyarsa sosai sbd duk wannan lokacin aikin wahalar gaske yake a rayuwarsa dan rufa musu asiri kuma har lokacin dukiyarta na nan wadda tace ta basa halak malak amma ya kasa tabawa sbd yanason ya Nemi inda zai ajiyeta dan bata rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa amma abin ya gagara.

Ahankali suka fara Gagarin rayuwa a qasashe gurin Neman su Ayanah Wanda zuwa yanzu rayuwarsa ta qarasa macewa gabaki daya sbd ciwon wahala da azabar rayuwa da qunci da suka taru suka rufar masa dan haka ya samu qasa me dan nutsuwa yace zai siya mata gida y ajiyeta tayi rayuwarta ta huta da binsa gararin duniya kada ta qare rayuwarta kamar tasa ta mutu a banza.

Kasa yadda da hakan Ayshaah tayi sbd bazata taba iya rayuwa ita kadai babu sa ba sbd a yanzu shine t Rabin jikinta rayuwarta,
Shine kadai hasken dayake rayuwarta shi kadaine Wanda rayuwarta take dashi dan haka ta shirya mutuwa a gurin Gagarin duniya tareda shi,
Ta shirya rayuwa da mutuwa tareda shi ko an inane ko awa ce qasane zata iya zama dashi.

Da wannan suka fada qasar BOYEM Wanda Sam babu ta yanda zaa barsu su shigeta kusan watan su uku anan babu damar shiga qasar dan haka suka juya suka bar qasar.

A border ta farko da baa shiga qasar BOYEM aka daura musu aure sbd hanasu gurin zama da akai koina garin sbd basada aure dan haka suka daura aure Wanda har cikin zuciya da ransu suna tsananin son junansu hakama sun shirya rayuwa da mutuwa a tare,

Aurensu ne ya kawo wata yar nutsuwar rayuwa a rayuwarsu data cikin tsananin duhu da qunci tareda kadaici,

Kusanci da sabuwar shaquwa da kauna tareda so me tsananin gaske sukewa juna suna sake Jin karfin gwiwan fuskantar rayuwa.

Bayan wata uku suka bar BOYEM sakamakon cikin daya bayyana a jikin Ayshaah,
Cikin ya taho mata da rashin lafiya sosai dan haka tafara wata irin rama taba kofewa alaman jininta yana yin qasa dan haka Abaas ya sadaukar da rayuwarsa da kudirin sa dan bata nutsuwan rayuwan daya kamata kodan abinda zasu haifa kafa suyita yawon duniya dashi dan haka suka juya inda suka fito,

Shima kirgen garuruwan da suka Baro a baya tsawon shekaru lokacin da aka dauko su daga garinsu ya fara yi dan komawa qasar sa garinsa gidansu da iyalinsa sbd matiqar Ayanah tana raye to tabbas yasan zata je nemansa a cikin duniya kokuma anan gidan mafarinsu dan haka zai jirata daga yanzu har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa.

*****tafiyar watanni sukai nai cikeda wahala da ukuba da tsinkewan zuciya ga yanayin ayshahh kafin Allah ya iso dasu dajin garinsu daya sha matiqar wuyar gaske kafin ya gane hakama dukiyarsu tayi qasa dan haka Koda suka iso ANJOM GHAZ cikin Ayshaah ya tsufa yakai wata takwas.
Chapter 73 · 0% Book details