← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 76

Sashe 63

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su tenya da sakina sanyi jikinsu yayi suka shiga zullumi da tinani Kala Kala zuciyarsu na rasa nutsuwa da sukuni sbd sanin hakan ba abune me yiyiwa ba batareda tashe tashin hankali ba da tsallake karfaffun sharudda daban daban dan haka a tsaye zukata da hankalinsu yake suna jiran abinda goben zata haifar idan har zasu samu barin masarautar kaman yanda NUAB ya kudirta da su kansu yanda suke so indai Zasuje suyi rayuwa da Ayanah da NUAB din sun shirya barin Masarautar BOYEM da basuda kowa a cikinta tinda ita kanta tenya yayanta duka basa nan suna gurare daban daban suna aurensu.

Tinda ya sanar dasu suke cikin zullumi da tashin hankalin da baya faduwa kuma baya nunawa musamman tenya data San aka samu matsala akasan dasu ake shirin barin masarautar da wishmah hakan zai iya zama bakin rayuwarsu dan haka suke a rashin nutsuwa da sukuni kwata kwata tareda jiran goben da zasu bar masarautar da qasar gabaki daya shikenan komai ya qare na tashin hankali da damuwa Ayanah zata rayu da ‘danta.

Ita kanta Ayanah din Wani irin rashin sukuni da zullumin goben takeyi sbd tabar nan tabi HAYATEEM duk inda yake rayuwa itama tayi rayuwar acan tareda shi da Abaas da shima yayi mata alkawarin a kwanakin nan zai fara Neman kawo mata shi.

Gabaki dayansu wunin a cikin zullumi me tsanani suke yinsa kaman yanda bangaren HAILE da yayanta suma suke cikin zullumin watan daya cika hakama manyan fada da suma suke cikin zullumin abinda zai iya faruwa a fada yanzu kuma dan suna ji a jikinsu duk Wanda yayi garajen kasa tsayawa ya duba kalaman sa da kyau zai iya rasa ransa batareda yakai qarshen labari ba dan haka su kawai ma barin NUAB da Yaransa suke so a masarautar ya koma inda ya fito masarautar bata buqatarsa hakama halayensa sun gama bayyanarda babuta yanda zaayi yayi mulkin qasa gabaki daya dan zai iya ringa bayyanarda tsiraicin jikinsa ga duniya ne Bayan yana matsayin sultan dan haka Sam babu ta inda zaa basa mulkin BOYEM.

Shi kansa Wani irin yanayi ne me Zafi da radadin kuruciyarsa dayake taso masa yakeji na haduwan da zaiyi da mutumin dayake matsayin ubansa amma yayi watsi dashi tinda qananun shekaru ya jefa sa duniyar da babu kowa da zai rayu dashi a cikinsa, ya kuma rabasa da mahaifiyarsa batareda tausayin halinda take ciki ba har tsawon shekaru….

Numfashi me dumi ya sauke mara sauti a lokacinda yake tsaye gaban mirror din dayake closet dinsa tukuna Kai tsaye ya wuce bathroom dan wanka,

Mintina ya dauka gurin wankan kafin ya fito daure da towel gashina na tsiyayar da ruwa a hankali.

Wani towel din ya saka a kansa qarami yana goge gashinsa dashi kafin ya iso gaban dresser ya tsaya.

Shirin mintin kusan talatin yayi kafin ya gama ya fito a lokacin 10 na dare tana gap da yi dan haka yana fitowa Kai tsaye bangaren sultan ya nufa cikin nutsuwa da Izzarsa.

Suna isa tin daga nesa masu tsaran kofar suka wangale masa kofar kansu a qasa cikeda girmawa suna masa Barka da zuwa da zallar ladabi.

Shima kadir dayake kofar a tsaye yana gadin isowansa dan tarbansa rissinawa yayi yana masa Barka da zuwa cikin girmamawa me girman gaske kafin ya basa hanya ya wuce shikuma yana gabansa dan yi masa iso har inda sultan yake Zaune cikin palon sa dayake hutawa na alfarma koina qamshinsa da sanyin ac ne ya kame ya riqe.

Su aleey a kofar suka tsaya dukkaninsu a natse sha hayaniya,

Palo biyu suka wuce kafin suka isa asalin palon dayake din yana Zaune cikin shigarsa ta hutawa tamkar ba dattijin daya manyanta sosai ba yana sanye da ash Riga da wando masu kauri da tsadan gaske da sukaiwa jikinsa kyau kwarjinsa ya cike gurin kaman yanda qamshinsa ya cike gurin.

Sako kan NUAB a cikin shigar datake kusan iri daya data sultan nasa qamshin a hankali yana gauraye gurin yana kokarin doke na sultan din sanyin nutsuwa a zuciya,

Dagowa sultan yayi yana Dora fararen idanuwansa akansa yana kallansa cikeda nutsuwa da kaunar da ba damar nunawa sbd wutar dayake gani a idanuwan NUAB din ta fushin da ba yanzu zai sauko ba shima baya buqatan ya sauko din yanzu harsai ya tirsasa karban abinda yakeson ya karba,

Kwarjini da nutsuwan kyan NUAB cike idanuwan sultan sukai kaman yanda nasa kwarjini yake kokarin shiga lafiyayyun idanuwan LEUL me BOYEM daya daukesu daga kallan mahaifin nasa yana isowa cikeda nutsuwa da izza tareda kamewa ya zauna a kujeran dake facing sultan din ya dago fararen idanunwansa ya kallesa yana yaqar wutar datake cin zuciyarsa ya bude Baki a taqaice da kamewa yace

‘Barka da wannan lokaci me BOYEM’

Numfashi me sanyi da dan murmushi sultan ya sake yana sake kafe idanuwansa Akan NUAB din Wanda shima dagowa yayi da idonsa masu razana maza ya bude Baki cikeda nasa mulkin da izaa yace

‘Barka da isowan magajin me boyem LEUL NUAB ALMAZZ,
Batareda bata lokaci ba menene dalilin son ganina??

Qarasa fada yayi yana komawa sultan dinsa sak cikeda ikon mulki ba wata sakin Fuska,

Shima NUAB din baida lokacin batawa a maganar ya dago ya kallesa Kai tsaye yace

‘Zan bar BOYEM a karo na biyu kuma wannan Karan tafiya ta har abada Wadda zanyita ne tareda mahaifiyata wadda banajin tanada Sauran amfani a masarautar…’

Qarasa maganar yayi yana dagowa ya zubawa sultan idanunwansa da suka bayyana da kyau fes Akan fuskar sultan din.

Cup din hot green tea din dayake hannunsa yana hayaqi sultan yayi yana jingina bayansa a natse hankali kwance kafin ya kalli NUAB din dakyau har lokacin hankalinsa kwance ba alamar ko mamaki a tattare dashi,

Bude bakinsa yayi da cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali yace

‘Nine datake a qarqashina zan sanar idan ma batada amfanin amma ba Kai da kake baqo ba a masarautar da rayuwarta ba……

Wani irin kallo NUAB yayi masa maganarsa na sukar zuciyarsa baice komaiba idanunwansa na dan sauyawa.

Cigaba da magana sultan yayi da cewa

‘NUAB ALMAZZ mahaifiyar Ayanah ghaz ta haramta gareka da kowa ma duniya Bayan ni daga ranar data zama wishmah ko yayanta basada iko da ita saini,
Wannan shine abinda Baka gama fahimta ba inaga,
Ayanah ghaz har abada kafarta bazata bar Masarautar BOYEM ba sai ranar da bana raye nabar duniya kenan to daga wannan lokacin ne zaka iya samun ikon mahaifiyarka amma Banda ina raye..

Wani irin motsi jijiyoyin NUAB din sukeyi suna fitowa idanuwansa kuwa ja suke rikidewa sunayi me tsananin gaske ya kafe idanuwansa akan sultan din Wanda yake magana hankali kwance,

Zafi jininsa yafara yi yana tafarfasa da maganar da sultan ke kokarin fada masa na cewa baida ikon mahaifiyarsa har sai ranar da sultan din yabar duniya Bayan shi bazai iya jiran hakan ba kome zai iyayi dan a basa mahaifiyarsa….

Bude Baki sultan yayi yana sake daukan cup dinsa yakai bakinsa ya dago ya kalli kadir dayake tsaye Wanda take ya juya ya dauko wasu takardu a cikin file biyu me kyau da tsari Yazo ya ajiye gaban NUAB kan table din gabansa ya juya ya koma gefe.

Sultan ne ya kalli files din kafin ya dago ya kalli NUAB din ya sake sakin nutsatsen murmushi me kyau yace

‘LEUL NUAB ALMAZZ me boyem kanada zabi guda biyu anan Wanda nasan zaka iya sbd mahaifiyarka,

Kallan files din NUAB yayi zuciyarsa na Wani irin tafarfasa da kaunar da har jikinsa ya nuna sbd Wani irin ja fuskarsa da hannuwansa sukeyi,

‘Zabi biyu ne a gabanka,
Na hannun dama takarda nada sabon sultan dazai mulki BOYEM ne datake dauke da sunanka kanta saka hannu a cikinta gobe zaa fitarwa da Masarauta da duniya ita a matsayin sabon sultan dazai fara mulki a gobe Wanda hakan zai Baka damar samun cikakken iko Akan mahaifiyarka harma da mahaifinka da baka buqata,

Ta hannun Hagun kuwa takarda ce da zata fita a gobe itama idan Ka saka mata hannu cewan har abada kabar BOYEM da mahaifiyarka harsai ranar da Allah ya dauki raina….
Zabi na gareka me BOYEM da Moscow.

Idan akwai abinda yafi tafarfasan jini shine yake faruwa da NUAB Wanda dukkanin jikinsa ke wata irin rawa koina nasa nayin ja idanuwansa na kafe Akan sultan Wanda shima shi din yake kalla zuciyarsa a shirye da karban duk zabin da NUAB din zaiyi a cikin biyun.

Yanda jikin NUAB din ke wata irin rawa da fizgar wutar dake ci a jini da kansa da kirjinsa ya saka yayi shiru batareda yace komaiba kuma bai dauke idanuwansa daga kan sultan dayake wa Wani irin kallan tsanar datafi duk wadda ya taba yi masa a baya ba ta yau din kokarin buga zuciyarsa takeyi dan miqewa yayi ya juya yabar palon idanuwansa kaman zasu fara feshin wuta sbd fushin da bai taba shigaba rayuwarsa.

Yana fitowa su aleey suka sha jinin jikinsu taje suka bi bayansa a qame batareda cewa komaiba.

NUAB na ficewa sultan shima take ya aika wa tenya sako a cikin Daren cewan Ayi sanarwar a Daren nan ya maida mata matsayinta na komawa zuwa kwana tiraka daga yau dinnan.

Sakon na isarwa tenya mummunan shock ta shiga Wanda y sakata mutuwar tsaye,

HAILE data fito a Daren itama cikin shirin zuwa tirakar kwana tama fitowa aka Dakatar da ita da sakon hakan Wanda ya sakata mutuwar tsaye kafafunta na kasa daukanta.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

58
Jiri me karfin gaske ne ya dibi HAILE wadda idanuwanta suke kokarin juyewa sbd dishi dishin da suke gani tsabar mummunan bugawan da kirjinta yayi tareda shock na babu tsammani,

Fetto ce tayi saurin riqeta cikeda tashin hankalin da baa saka masa rana ba itama dan kuwa kaman kunnuwansu basu ji musu da kyau
Dagowa fetto tayi ta kalli jakadiyar sakon wadda ke tsaye da bayi biyu a bayanta kansu a qasa cikeda girmamawa ta zuba musu ido bakinta na nauyin rasa ta inda zata fara jeho tambayar ta bude Baki a dan rikice tace

‘Maimaita sakon’
Chapter 63 · 0% Book details