← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 76

Sashe 67

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******A Daren ko kadan aleey bai rintsa idanuwansa da kwakwalwansa ba saida ya hada wasu irin fitinannun bincike da bayanai har asuba,

Sallar asuba yayi ya cigaba da hada kan bayanan sa da zai gabatarwa LEUL kuma yana saka ran ta hakan insha Allah Abaas kaman yana hannunsu ne.

Karfe goma na safe NUAB ya fito a shirye cikin brown gucci wears da takarmin berluti brown suma fuskarsa fresh duk da yana cikin tsananin damuwa a kwanakin amma komai nasa yana nan daukan ido da girgiza zuciya yakeyi,

Koda ya fito aleey yana tsaye shirye a palon hannunsa dauke da iPad fuskarsa sanye da farin glass da girmamawa ya yi masa Barka da fitowa yana bin bayansa zuwa dining inda aka cikeda tsaf da breakfast dinsa sbd yanzu da Amminsa take kwance ya Dena cin abinci acan.

Zaunawa yayi a daidai lokacin shima aleey din ya zauna Bayan yayi serving nasa.

Cikin nutsuwa sukai breakfast din suka kammala suka Baro dining din NUAB ya zauna Akan lafiyayyar 2seater Turkish royal cushion dake palon ya dago fararen idanuwansa masu daukan ido ya sauke Akan Aleey Wanda ya sauke ajiyan zuciya a natse ya matso ya bude iPad dinsa ya kamo bayanin dazai masa ya miqa masa a natse da girmamawa kafin ya dan ja baya kadan yana bude laptop din hannunsa daidai lokacinda NUAB ya bude abinda ya gama hada masa yafara bayani da cewa,

‘ANJOM GHAZ shine asalin garin da su Ammi suka fito,
Safarar bayi ce ta fiddosu daga can zuwa nan Wanda a yanda Maa tayi bayani babu sunan qasar da suka sani Bayan anfito dasu zuwa nan din BOYEM,

Abinda na tattara a bayaninta shine tace qasa goma sha shida aka wuto dasu ta ruwa kafin suka iso BOYEM,
A bayanin nata su qasashe shidan nan bawai ta tabbatar bane amma a iya lissafinta tsayuwa goma
Sha shida akai dasu Wanda hakan ya tabbatar mun da qasashe ne suke tsayawa kenan dan babu jirgin ruwa me girman da zai ringa tsayawa koina idan ba bodar wata qasar ya isoba,

Zoomin map din daya hada yayi yana cigaba da cewa

‘Batasan sunan qasar da suka rabu da Abaas ba amma qasa biyu suka qara tsayawa Bayan rabuwarsu dashi a ta ukun ce suke isa inda aka saida su maana nan BOYEM kenan,
A binciken dana tabbatar bisa ga wannan bayanin nata dama hada shima to qasar LARASIA aka siyar da Abaas Wanda idan muka duba qasa biyu ce tsakaninta da BOYEM dan hakan nake da tabbacin larasia dince inda aka siyar dashi.’

Wani bangaren Aleey ya sake zooming yana cigaba da cewa

‘Idan kuma na aka hada lissafin qasa goma sha shida dake akwai daga nan BOYEM ta gabas to Nahiyar qasar BASSHAH kenan
idan kuma daga yamma ne qasa sha shida daga nan qasar ALSIYASH kenan,
Idan kuma ta kudu ne qasar BUHARAQS kenan
Hakama idan ta arewa ne to qasar ANTARIA kenan.

Duka duka wannan bayanin dana hada qasashen nan sune inda zaa fara binciken nemansa amma dole duk qasar da zamu tafi Bayan sauka qasar sai an tafi bakin bodar ruwansu tanan ne dole zaa iya gane garuruwa masu kusa da manyan oceans da zaa iya samun tabbacin samun sa.

Dagowa yayi ya kalli LEUL BOYEM da idanuwansa da suke cike da Basira da wata irin kwakwalwa me hasko komai Akan lissafi da nazari,

Shima NUAB din gama kallan bayanin da duka suke a rubuce da map din Bayan duk bayanan dayayi masa da baki kuma,
Dagowa yayi ya kalli Aleey ya bude baki a natse yace

‘Meye karshen tinani da bayaninka ya hada?

Ajiye laptop din hannunsa yayi tareda kallan NUAB din cikeda girmamawa yace

‘Tinda ta ruwa suka iso qasar to dole bangare biyu ne Hagu da dama Wanda yake kudu da arewa kenan dan haka a cikin biyun zaa fara da daya maana a faro binciken daga inda suka fito tin farko ANJOM GHAZ kenan dan kuwa akwai yiyuwar tinda Abaas namijine to tabbas a tsawon shekarun nan indai ya samu yancinsa to tabbas ya koma gida dan sake ginawa da farfado da sunan GHAZ da bazai taba barin ya shafe ba Bayan ya nema yan uwansa be samu ba kenan,
Dan haka inaga a fara daga can din Kai tsaye sbd tabbatarwa idan bai komaba Sai a Nemi Sauran qasashen.

Kallansa NUAB ya dago a natse yayi cikin yadda da kowane bayanin aleey a koda Yaushe Akan komai sbd baya taba hada lissafin da bai qure kwakwalwansa akansa ba dan haka Numfashi me sanyi ya sake tareda dagowa yace

‘A gobe Inason a shirya tafiya zuwa qasar buharaqs din Wanda a cikinta ANJOM GHAZ take insha Allah.

Gyada Kai aleey yayi sbd yanada tabbacin insha Allah haka bayanin yake ba tantanma indai Abaas na raye yana saka ran ya koma dan farfado da GHAZ matiqar shi namijin jinin GHAZ ne dan ‘dan halak ko baida zarra bazai yadda sarautar gidansu ta fadi ta shafe a tarihi ba.

Juyawa yayi ya bar gurin yana daga wayar sa dan fara shirin tafiyar tasu da bazata wuce kwana biyu su wuce ba.

Bayan barin aleey shiru NUAAB yayi yana Jin Wani irin yanayi na rashin sanin tinanin Kamawa Akan me haduwan mahaifiyarsa da Abaas zata kasance hakama a yanzu da mahaifiyarsa take cikin halin da bazata iya basa labarin cikakken tarihinta ba a bakin Abaas dayake jininta yakeson jin asalin tarihin komai na Amminsa.

*******
Cikin kwana biyu aleey bai hutawa ba sbd bai taba wasa da duk abinda yake na LEUL ba dan haka shirin tafiyar ya tsaya tsayin daka saida ya tabbatarda ya hadata a cikin sati guda Bayan ya gama tanadar da komai na tafiyar wadda ya hadata hadda Maa sakinah da zata kaisu har cikin ANJOM GHAZ Bayan sun isa qasar kenan.

Tenya batasan da tafiyar ba sai ranar da zaa wuce kai tsaye NUAB ya sanar dasu dan haka jiki a mace da tsananin zullumin daya saka jinin Maa sakinah mummunan hawa sbd komawa inda komai ya faro.

Karfe Dayan rana motocinsu a Jere suka fice daga Masarautun zuwa airport Wanda motocinsu na zuwa gate din qarshe daidai nan motocin da suka dauko mai girma YUNAR BOYEM daga airport tareda ‘yarsa LEYLAH YUNAR BOYEM ‘yar amaryarsa ZUHRAH GHAZ BOYEM wadda ya kawo a matsayin tukuicin dawowan MAGAJI LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya basa aurenta a matsayinta na jinin BOYEM itama.

Ficewa motocinsa sukai tareda securities dinsa Bayan motocin mai girma YUNAR din sun shigo sukuma batareda kowannensu yaga junaba musamman LEYLAH YUNAR data gama mutuwa akansa tin kafin ganinsa a zahiri sbd kallo daya datai masa a hoton labarai ta shirya zama ko mistress dinsa ce ba matarsa ba dan haka wannan tukuicin da mahaifinta ya badata na aure shine abu mafi farin ciki da girma na rayuwarta dan haka batada baqin cikin dawowan su Masarauta da zama.

Su kuwa suna isa airport Kai tsaye jirginsu ya daga yabar qasar.

Tafiyar awanni masu yawa sukai kafin suka isa qasar bhariqs din wadda saida suka kwana a wata qasar kafin suka sake hawan jirgi suka isa.

Tinda suka iso daga shi kansa NUAAB din Wanda baisan kaddarar mahaifiyarsa da zai tarar acan ko tasa sbd zuciyarsa dake Jin rashin nutsuwa da sukuni,
Maa sakinah ma sosai ta shiga mummunan halin daya sakata fara ciwo me dan karfin da har saida taga likita kafin suka dauki wasu mahaukatan motoci zuwa tafiya me tsananin tsayin da zata kaisu ruwan dake qasar Wanda tacan zasu bi sakinah ta gane dajin garin ANJOM.

Kwana daya da wuni sukai suna tafiya kuma saida suka dauko likita ma musamman sbd ciwon Maa dazai iya tashi koyaushe,

Sun iso garin dayake bakin ruwa basu tsaya komaiba Aleey ya siya musu jirgin ruwa gabaki daya suka shiga dan barin gurin.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

62
Tafiyar wuni guda da kwana daya sukai suna zagaye ruwan da tafiya ke tsayi kafin Kaman a mafarki sakinah ta daga hannu tana nuna gurin daya saka idanuwanta jajir hannuwanta na rawa.

Bakin dajin suka tsaya su aleey da Sauran Yaransa suka fidda drones dan duba duk abinda yake cikin dajin da gari ma idan akwai.

Aleey ne yake riqe da iPad din dayake kallan dajin da drones dinsu suka shiga suna yawo a sama,

Sauran yaran kuwa a tsaye suke da mahaukatan bindigoginsu a shirye da harbe ko dabba ce tayi motsi a gurin,

NUAB yana ciki Zaune yana jiran bayani daga aleey Wanda yake sake kallan iPad din hannunsa da kyau sbd tabbas yaga gari.

Wasu mahaukatan bikes dake shiga daji suka fidda daga jirgin ruwan suka hau tareda kutsawa cikin dajin a shirye da bindigoginsu da wasu manyan wuqaqe masu shegen hadari.

Tafiya sukeyi suna kutsawa kafin sukai tafi me Nisan gaske basu isa garin ba sai yamma lis wanda ya saka sakinah yanke jiki ta fadi tama Dora kafarta a qasar garin ANJOM GHAZ kenan.

Cikin kulawa da bada umarni yace a koma da ita jirgi taga doctor ya dubata abarshi daga shi se aleey su fara ganin lafiyar garin ma tukuna.

Sauran yaran da bikes din tareda Maa sakina Juyawa sukai suka koma.

Kafarsa ta dama ya fara dorawa a cikin garin ANJOM GHAZ daya saka tsigar jikinsa tashi sbd ganin yanda garin ya zama tamkar ba garin da mutane suke rayuwa a cikinsaba sbd duk tsawon shekarun garin bai dawo daidai ba sun rasa niima da tarin albarkar garin nasu.

Akwai mutane sosai da gidaje sosai da kasuwanni a garin amma ba kamar baya ba sbd kusan kowa na garin yasan kowa tinda ba yawa sosai.

Ganin baqi a garin ya saka gabaki daya mutane shiga tsoro da tashin hankali dan haka Kowa ya fara silalewa yana komawa gidansa ya shige ya rufe tinda dai shugaban garin nasu baida lafiyar dazai basu kariya,
Fiyeda shekaru tara yana kwance yana jinyar da ba lallai ya tashi ba sbd yayi mummunan nisa.

Gidan shugaban garin Aleey ya nema a taimaka a nuna musu babu musu kuwa Wani ya kaisu har kofar gidan asalin sarautar GHAZ.
Chapter 67 · 0% Book details