← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 76

Sashe 49

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinah da samun yancinta bai saka taji zata iya barin Ayanaah ba har abada itama sanyaye jikinta yake hakama ta shirya zama baiwar Ayanah har qarshenta ko da yanci ko babu yanci zata bauta mata ta kuma bauta ma ‘danta har girmansa.

******acan tenya kuwa Kai tsaye bangaren gyara ta isa da Zuhrah ta fara bada umarni aka wanke Zuhrah tas aka ringa cire datti harma da wasu qananun qwari a jikinta tsawon kusan wuni guda,
Taso a yanke gashinta amma sbd imebeti zaa turata tana buqatan dogon gashin dan haka sai aka barshi shima ya ringa Shan wanki kan wanki,

Ana gamawa gyaran kafafunta da hannuwanta akai na farce tukuna aka kirawo likitoci suka duba lafiyarta,

Magani dasu multivitamins aka bata sai kuma tenya data bada umarnin aka hado mata mai na gargaji dayake goge tabo a qanqanin lokaci dan goge tabon raunikan data yiwa kanta duk da sun warke sun fara bace wa da disashewa saura dakan Wanda shine kila bazai fita ba sai sun hada masa da magani.

Har dare sosai tenya bata huta ba tana kan lamarin Zuhrah da babu wani lokacin batawa matiqar tanason jefata a matsayin imebēti tana buqatar tsayuwan gaske a gurin gyaranta.

Ayanah kuwa a nata bangaren tinda Zuhrah ta fito sai taji jikinta yayi sanyi ta sake raunana da komai,

Ta bawa sakinah dukiya me yawa Akan ta tafi ta samu yanci tayi rayuwarta amma sakinah Sam bazata iya barinta ta kafe zata zauna da ita har karshen rayuwa,

Batada Sauran walwalan daya rage mata kokuma shaawar rayuwa dan haka bata takura sakinah dinba dan kuwa daman ita kadai ce a yanzu ta rage mata a asalin rayuwarta hakama tana buqatan Wanda zai tsaya mata ya tayata bawa danta kariya duk da ta zabar masa yancin zabar abinda yakeso da kansa ba tirsasawa tin yanzu Akan mulkin datake tsoron kada a illata mata shi akai,
Hakaman tayi hakan ne dan basa kariya daga masifu da hadarin da zai fara fuskanta ta ko ina tin yana jinjirinsa so yanzu zaa bar mata shi yayi rayuwa a cikin aminci tinda an riga an cika mata wannan alkawarin sai kuma idan ya girma idan yanada raayi hakan zai zama barazana ga Maqiyansa da masu so.

A bangaren sultan YASAR kuwa Ayanah ghaz tayi masa babbar sukar data rage mata matsayi a zuciyarta dan kuwa duk irin soyayyar da jinin BOYEM zaiwa mace baya taba sauya abinda yake yawo a jininsa dan ako Yaushe harkar mulkinsu da iko tareda abinda suke Buri yana gaban kowace irin soyayya da kauna,

Duka shekarun daya Debo na tsananin burin samun ‘da namiji sbd hakan ne,
Sbd tabbatarda magaji Akan karagarsa bama batareda ko yanada raayi ba ko bayada raayi amma a Karan farko na tarihin masarautar ta zabawa ‘danta kaddararsa tin yana zanin haihuwansa,

Yanada wani magajin Bayan NUAB da zai iya gadon karagar amma abinda tayi masa ya sakasa Jin ko zata rasa ranta sai ‘dansa da yayi raayi ya mulki BOYEM koda hakan na nufin fizge ta daga matsayinta sedai amma zuciyarsa na kasa barin sa ga aikata hakan dan kuwa kaman yanda jinin BOYEM da bazai taba barin burinsa ba yake a jininsa haka soyayyarta take a jininsa dan haka idan bazai iya cireta a zuciya da jininsa ba to zai iya cireta daga dukkanin qudurinta da bazai taba cika ba.

Haile a yanzu ne ta samu damar sassautawa zuciyarta ta fara Neman lafiyarta da gaske dan kuwa a yanzu ta samu tabbacin tanada dama me karfi ta qwatowa ASIM matsayinsa da aka bawa ‘dan mistress,
Bazata taba hutawa ba ko samun bugawan zuciya daidai har abada idan ba ganin ASIM BOYEM tayi ba Akan kujeran mulkin BOYEM,

Batada Buri ko kudirin daya wuce saka ASIM a zuciyar sultan YASAR fiyeda dan mistress dinsa,
Zata tabbatar ta dawo da matsayi da ikonta a hannunta na juya rayuwar kowace macen datake imebētinsa,
Zata ninka tsoronta da zafinta akansu ta yanda bazasu taba iya kallan Ayanah da ‘danta da darajar data wuce mistress ce da dan mistress dan kuwa a yanzu ne zata tada asalin rashin imaninta Akan abinda takeson ‘yayanta su mallaka,
Ko rai nawa zata kashe batada shakka zata kashesu tamkar dabbobi sbd saita tabbatarda Ayanah ko kallan inda take babu me yi bare bata girman matsayin datake dashi.

****Burika ne suka cike zukatan dukkanin masu jinin sarautar BOYEM Wanda hakan ya fara bayyanarda wasu manyan Zafafan hadari da rayuwa zata fara fuskanta dan kuwa a qanqanin lokaci kadan bayin Ayanah uku suka rasu batareda ansan menene yake ajalinsu ba amma kuma masu bincike sun tabbatarda koma menene kaman poison ne,

Wannan lamarin shine ya fara daga hankalin tenya da sakinah harma da sauran imebētis kowa ya shiga mummunan tsoro da firgici,

Ayanah bata shiga damuwan komaiba sbd rayuwarta data gama mutuwa ayanzu kwata kwata bata San komaiba Bayan qunci da baqin ciki se kadaici dasuke cin lafiya da hankalinta ahankali ahankali batareda sanin kowa ba,

NUAB ne kadai Wanda take Zaunawa ta rungume tana kallansa batareda kyafta wan ido ba tanajin akansa ne kadai take rayuwa yanzu,

A duk lokacinda take kafesa da ido tayita kallansa rabin jikinta Abaas ne kadai take ganin fuskarsa Akan tasa yana yawo kewa da tsananin sonsa na tsananta ciwon dayake cin zuciya da ruhinta dan hakanne a yanzu Abaas kadaine zuciya da rayuwarta take nema.

Tenya na cikin matsanancin tashin hankali da rashin nutsuwa mai yawan gaske da duk ta firgice itama sosai sbd hankalinta daya rabu biyu Akan kulawa da Zuhrah datai wa Ayanaah alkawarin saita tabbatarda ta miqa rayuwarta inda zata rayu cikin aminci kafin ta huta da kuma hadarin datake ganin yana kusanto Ayanah da ‘danta dan kuwa komai ya rikice ga dukkanin imebētis din dake masarautar sun koma tamkar yan amanar HAILE duk abinda ta sakasu shi sukeyi sun bayyanar da tsanarsu me karfi Akan Ayanah da ‘danta,

A bangare daya ma kaf ‘yayan da suke na sultan tsana me karfi sukewa NUAB da Kai tsaye suke ambata da ‘dan mistress kaman yanda HAILE da kanta take kiransa,

Duk wannan abin Ayanah batasan anayi ba sbd bata cikin cikakken hankalinta na tinanin kowa Bayan na danta da kwanakin dake qaratowa na rabuwa da yar uwarta da bata saka a ido ba kuma shikenan bazasu saka juna a idonta.

Tenya sake dage wa tayi Akan aikinta Wanda a yanzu Zuhrah ta sauya sosai tamkar ba ita ba tayi Wani irin Kyan gani da haske sosai duk da haskenta bai dawoba amma ta ciko tayi kyau sosai sai kalar sabuwar fatar tata mai dan duhu tayi mata kyau ta sake sauya kamanninta daga yan uwanta tinda a yanzu tsawon wata daya harda sati guda kenan,

Duk wannan gyara da Jin dadi tareda lafiyayyan Hutu da cima me lafiya da kyau da ake bata itama rayuwarta bata taba cire quncin datake ciki ba koma minti daya itama,
Rayuwarta ta jima da mutuwa kaman yanda ta ‘yar uwarta ta mutu kuma bazasu taba samun sauyin hakan ba duk zuriar da zasu tara quncin daya shigesu ya riga ya tafi da ruhinsa zasu rayu a mistresses din jinin BOYEM zasu tsufa a hakan zasu mutu tarihin zuria ahalin GHAZ ya rufe shikenan.

Da kewa da tsumayin son samun ganin yar uwarta karon karshe Zuhrah take kwana a kowane sare kuma take tashi,

Duk yanda qunci da tarin baqin da damuwa suka fara taba lafiyar Ayanah haka zuhran ma sun dade da fara taba lafiyar kwakwalwanta da ita kuma tafiya inda iyayenta sa Sauran yan uwansu suka tafi take buqata dan gwara Ayanaah a yanzu tanada ‘dan cikinta da shine zaisa ta iya cigaba da rayuwa ko babu dadi ita kuwa batada kowa Bayan Ayanah din kuma a yanzu gashi zasu rabu rabuwan da shikenan.

A Daren da zaa gabatar da Zuhrah a matsayin imebētin da akaiwa mai girma YUNAR tukuicinta a wannan Daren itama wishmah zata fara komawa tirakar sultan Wanda tinda akai bikin basu sake haduwa da juna ba NUAB ne kadai Wanda kowace rana se ankai sa tareda bayi masu tsaron lafiyarsa.

A tsawon wannan lokacin bata taba tinaninsa ba sbd batada tinanin kanta saina ‘dan dayake gabanta da Zuhrah da Abaas sai Ayau din da aketa shirinta Ana mata gyara na musamman da wasu irin tsare tsaren daya ringa tina mata rayuwarta ta farkon zamowa imebetin.

Tenya data har zuciyarta takeson hadasu suyi ganin junan karshe sbd tana iya ganin tsananin halinda kowacensu take ciki hakama matiqar basu ga juna Ayau din ba shikenan dan kuwa Zuhrah daga wayewan garin gobe zata bar qasar zuwa inda ba dawowa dan koda hidima zata kawo YUNAR a boyem to bazai taba zuwa da ita ba matiqar ba matsayin wishmah din itama ta samu ba dan haka zaman daular sa zatai ta ringa hayayyafa har qarshen ranta.

Daga Ayanah har Zuhrah yau damuwansu da quncinsu ya ninka na kullum sbd daga yau ne karshen da zasu shaqi iskar gari daya dan haka kowacensu babu inda yakeda dogon amfani a jikinta.

Karfe goma sha Dayan dare aka fito da kowacensu dan tafiya tiraka duk Taku daya da Ayanah keyi tamkar Ana zare mata ruhinta daga gangar jikinta take ji idanuwanta sunyi jajir daga ita sai sakinah da bayi kusan shida ne suke tafe tareda da ita sakinah na dauke da NUAB sbd tenya tana tareda Zuhrah da doka itace zata kaita har babban bangaren YUNAR dayake da nisa sbd duniya ce guda me zaman kanta zube a bangaren sa.

Tafiya sukeyi Ayanah na sake rasa kanta daidai kusan isarsu tenya ta Ambaci sunanta daga bayanta Wanda ya sakata tsayawa cak batareda ta juyoba kanta na mummunan sarawa.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

45
Kasa juyowa Ayanah tayi idanuwanta na fara wani radadi sbd rashin hawayen dake cikinsu zuciyarta na harbawa da Wani irin karfin dayake nuna tashin isashiyar lafiyan zuciya sbd jikinta ya karba yanayin daya tabbatar mata da Zuhrah ce a bayanta,

Daqyar gangar jikinta ta dawo aiko daga wutar data dauke ta iya motsa kafafunta ahankali tana juyowa hannuwanta na rawa ta damqesu tareda qarasa juyowa gabaki dayanta ta fuskancesu suna bayanta daga nesa kana tsaye,
Chapter 49 · 0% Book details