← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 76

Sashe 32

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Allah ne ya kaddaro muku hakan da gani har ke har Zuhrah babu Wanda zai iya sauya hakan,
Allah ya fini sanin dalilinsa na yin haka hakama yafi ki sani yafi Zuhrah sani harma da duka masarautar BOYEM din,
Ga dukan alama kaddararki ce ta sako mu halinda muke ciki sbd Allah ya riga kila ya kaddara tarayyarki da sultan YASAR Wanda matiqar akwai rabo a tsakaninku to shine yayi sanadin komai daya faru dan zuwanmu nan,
Komai daya faru ya samu yan uwa da iyayenki ki yadda da rabo mai karfin dayake tsakaninku ke kila ya haddaso hakan dan haka ko a yanzu rabon ke dince ya saka yar uwarki sadaukar da rayuwarta sbd bazata iya qazantar dake shirin shiga tsakaninku ba ta hada shimfida daya da Mutum daya ku haifa masa yaya ku hada yayanku uba daya Kina raye tana raye,

Kinyi kokarin daukan taki rayuwan Amma Allah ya Hana hakan sbd kece wadda kila ya kaddarowa hakan,

A yanzu Zuhrah ta Riga takai karshen tata kaddarar kila dan kuwa har abada mutuwarta ce kadai zata fiddo da ita inda aka kaita waton gawarta ce kadai zata fito idan zaa rufeta kenan,

Tsananin so da kaunar da kike mata da saka rayuwarki a halakar da zaku rasa Ranku gabaki daya bazai taba sauya kaddar datake boye a cikin wannan lamarin ba,

Lokaci yayi da zaki rungumi kaddarar da gaske AYANAH GHAZ,
Zamtowanki imebēti ki haifi jinin BOYEM ko mace ko namiji shine zai baki hope na koba yanzu ba zaki fitar da yar uwarki daga wannan ukubar data Riga ta shiga sai mutuwa,
Zamtowanki cikakkiyar imebētin sultan YASAR BOYEM shine gatan da zakiyi wa yar uwarki da komai dade wa bazata cire rai daga samun ceto daga gareki ba dan kuwa tayi abinda tayi dinne dan ke ki samu zama imebētin ke kadai bada ita ba dan tasan zaki taimaka mata daga lokacinda kika samu daman tashi daga baiwa hakama matiqar kika zama imebētin kika tashi daga baiwa ko ba yanzu ba Kinada Sauran saka ran samun yancin Neman dan uwanki Abaas da shima matiqar yana raye yasan indai Kina raye wata ran Zaki iya nemansa,

Ke kadai kika raye a GHAZ wadda yan uwanki suka Dogara dake dan Allah Nima Ayau Ina rokonki ki jure ki daure ki rayu ko dan yan uwanki Dani kaina…….

Wani irin kuka mai tsananin ratsa zuciya ne sakinar ta sake tana sake sunkuyar da Kai tace

‘Matiqar kika jure kikai sadaukarwa tabbas ranar da zaki fiddo yar uwarki zata zo harma Kuyi rayuwa a tare idan bazaki iyaba ki daure ki iya kiyi sadaukarwar da yar uwarki tayi ki jure kiyi yaqi da komai ki ceto yar uwarki….’

Rufe idanuwa ahankali Ayanah tayi wasu hawaye masu dumin gaske suna gangarowa daga cikinsu batareda ta motsa ba har lokacin,

Shiru sakinah itama tayi hawayen na gangarowa daga cikin idonta babu Wanda ya sake motsawa a cikinsu hawayen Ayanah takeyi sosai hatta gashin jikinta sun kwanta gabaki daya tamkar sun mace,

Babu Sauran rayuwar data rage mata a yanzu da batada kowa a rayuwarta bayan sakinah,

Dukkanin kuzari,farin ciki,ruhi da bugun zuciya da hasken idanuwanta an rabata dasu babu ko daya a tattare da ita dan haka babu Sauran abinda ya raye komai na rayuwa bayan gangar jikinta da yanzu itama zata zama ba nata ba saina biyan buqatan wani Wanda zai watsar da ita ya manta ita da duk abinda ya rabata dashi ta zama fanko sauransa har qarshen rayuwarta,

Batada Sauran zabin daya wuce wannan din matiqar ranar da zata fiddo yar uwarta zatazo tabbas zata zama fankon ragi da Sauran wani din har karshen rayuwarta sbd daman babu abinda ya rage a rayuwan Bayan gangar jikin.

Hawayen ne suka cigaba da gangarowa gefen idanuwanta dake rufe batareda ta motsa ba har lokacin sedai sakinah ce ta saka farin qaramin handkerchief mai tsafta tana share mata hawayen ahankali suna saika Akan kyallen batareda ta sake cewa Ayanah din komaiba sbd ba abinda ya rage ma fada.

Shiru dakin yayi ko numfashinsu Baka Ji har tsawon Daren haka suka shafe sa cikin toshewan zuciya babu motsi,

Sallan asuba ce ta saka Ayanah din motsawa bata iya tsayuwa daidai ta miqe sakinah na riqe da ita har toilet.

Dukkaninsu sallah sukai suka ringa kuka mai tsima zuciya suna fadawa Allah damuwa da quncinsu har gari ya fara haske lokacin sakinah ta fice zuwa dakinsu tayo wanka ta sauyo uniform ta taho tafara aikinta ita kuwa Ayanaah na Zaune zuru ta kwantar da kanta a gwiwan kafafunta seti da window ta zubawa waje ido bata ko kyaftawa.

*********Ayau din aka taho aka kawo masu fara mata gyara ma Musamman Wanda zai qarasa dawo sa asalin kalar fatarta fara sol da gyaran fata da qamshi na musamman Wanda tinda masu gyaran suka iso bata iya cewa komai ba ko kuzarin komai duk yanda akai da ita tana Zaune babu gardama ko hayaniya ta zama tamkar Mutum mutumi dan haka suma suka zags sosai sukai aikinsu hankali kwance a natse,

Har kusan dare Ana abu daya da jikinta kafin suka tafi sai kuma gobe,

Washe gari ma haka suka taho sukai aikinsu suka tafi,

Tsimata akeyi cikinta da fatarta da asalin zallan madarar raqumi da lalle da zuma tareda wasu Hadi masu tsananin qamshin da hatta gashinta dayake Shan gyara qamshi yake fiddawa me sanyaya zuciya da kwantar da hankalin mai shaqa tareda basa nutsuwa da mutuwar jiki,

Sati guda akai Ana mata gyaran daya sauya kalarta da kamanninta asalin Ayanah dinta ta dawo sedai duk tsawon lokacin nan babu Wanda ya taba Jin koda muryanta sbd gabaki daya ko magana ta dena ido ne kadai se Numfashi ya rage mata sai kuma yanda akai da gangar jikinta ta sauya gabaki daya ko sakinah bata samun maganarta se dai ido kawai.

A cikin sati biyu tenya ta gama samun duka abinda takeson samu a gurin Ayanah na zama imebēti kafin zuwa wishmah dan kuwa hatta yatsun kafafun Ayanah dama hannunta abin kallo da daukan hankali ne sbd ta fito asalin balarabar ANJOM GHAZ dinta,

Haskenta da kyanta wani daukan ido yake yana fizgar hankali,
Qamshinta kuwa daya gama Kama kowane saqo na jikinta da gashinta tana tinkaroka zakaji qamshin asalin Larabawan BOYEM yana tashi a jikinta musamman idan tai motsi haka zakaji sa yana ratsa zuciya da gangar jikinka dan haka kwata kwata aka hana kowa ganinta bare Jin qamshinta bayan sakinah da ita kadai ce baiwar da tenya ta yadda ta Barwa hidimart sbd labarin Kyan Ayanah GHAZ na isa gurin HAILE zata iya yanke mata hukuncin Kisa Kai tsaye tin kafin sultan ya mallaketa a shimfidarsa dan haka tenya ta saka ido sosai da tsaro akan AYANAH GHAZ kaman yanda take kiranta kafin ta hau shimfidar sarki sunanta ya tashi daga hakan.

Tsaro sosai Ayanah GHAZ take samu daga tenya wadda daga qarshe dauketa tayi daga bangaren gabaki daya ta dawo da ita gurinta sbd barazanar datake ji a jikinta na kusanto Ayanah din sbd kyanta da yayi Wani irin yawan da itama idan ta kalleta Jin takeyi gabanta ma faduwa.

Dawowan Ayanah gurin tenya ya sakata sake shiga ran tenya sbd shirunta daya zamo tamkar nutsuwar datafi ta kowa data sani a rayuwarta hakama hakanan takejin a ranta Ayanah zata iya sauya musu kaddara dan yanda take Jin nacin son kasancewanta imebēti kota halin yaya dan haka ta matsu safiyar Washe garin ranar ta wanye dan sultan YASAR na kan jirgin sauka BOYEM Wanda a Daren goben ne zata isar da Ayanah shimfidarsa da insha Allah take masa fatar samun rabon haihuwa da ita.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

30
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
A Daren Ayanah bata rintsa kona minti daya ba kwance kawai take amma babu ta inda bacci ya tinkaro idanuwanta sbd koda Yazo na iya ido ne babu kowane sauki da sassaucin dayake bawa ruhi da zuciyarta sbd a daidai wannan gabar ta rasa nutsuwa da farin ciki tareda walwala ko sakewa har abada sai kuma ranar data iya saka daya daga cikin jininta biyu da suke raye a idonta dan haka zata rayu ne kawai gangar jikinta na aiki amma Banda zuciya wadda itama bugawa kawai take amma duk abinda zata samu a duniyar nan yanzu bazai taba bata farin ciki Kona seconds ba sbd ta gama rufe babin rayuwarta babu farin cikin dazai shigo bayan qarasa rayuwa da qunci daddabe a ranta kuma a hakan zata bar duniya.
Chapter 32 · 0% Book details