← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 76

Sashe 42

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinah jiqe take shar kaf da zufa tana tsananta adduarta a fili tana share zufan Ayanah suna sake qanqame hannun juna Ayanah na Jin kaman bazata rayuba rayuwarta zata tsaya ne daga nan sbd abinda take ji tabbas shine kowace uwa takeji yayin jeho yaya a duniya idan har ta mutu anan ta tabbatarda tayi shahada dan haka take Jin inama zata mutu anan din ta huta.

Lokuta masu tsayi suka dauka dukansu suna naquda me tsayi da rashin sauki,
Babu wadda bata Kai qarshen jigata ba a cikinsu tareda fita hayyaci,

Duk wainda suke tareda su sun sare sun shiga tsoro da fargaba tsawon wunin da babu komai cikinsa sai jiran azaba,

Karfe shida na yamma a lokacin da baby ya turo kai fitowa jikin HAILE gadan gadan take su fetto suka shirya tsaf ma tarbansa cikin tsananin matsuwa sbd suna sane da har lokacin Ayanah ghaz bata haihu ba dan akwai sautin karar da ake sakewa masarautar ta amsa gaba daya idan an haihu dan haka tinda basu ji komai ba sun San bata haihunba gashi yanzu tasu zata far haihuwa babbar matsalar shine fita a wannan lokacin batareda haihuwan Ayanah ba zuwa isar da sakon haihuwar.

Cikin azababbiyar azaba da Nishin dayake hade da ihu mai karfi Haile ta saki tana qanqame hannuwan yarta da karfin gaske ta sunbulo babyn dayake cikinta ya fado a hannun likitar dake gabanta idanuwan fetto kaman zasu fado qasa sbd jiran ganin abinda aka Haifa,

A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta sauke wani kakkarfan nishin daya fito da nata babyn duniya itama Wanda ya fado a hannun tenya Wanda jikinta ya dauki mummunan kakkarwar abinda aka Haifa tama kasa yadda da abinda ta gani.
#MAMUH
#THE LION ARRVL

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

38
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
Doctors din guda biyu na masarautar tin tsawon shekaru masu dan dama da basa karban kowace haihuwa sai ta asalin Matar sarki qananun su ne suke karban haihuwan imebētis amma Ayau sune sultan da kansa ya bada sakon umarnin kiransu amsar haihuwan wishmansa Shiyasa Haile bata samu damar samunsu a masu karban haihuwant wannan Karan koda kuwa Ana iya samun damar dan aike ya fita a lokacin naqudar to ba samunsu zatai ba sbd suna Akan wishmar BOYEM,

Ajiyan zuciya suka ringa saukewa suna kallan babyn Wanda kukansa mai karfin gaske ya cike dakin da bangaren gabaki dayansa harma daga wajen GHAZ chambers Ana jiyo kukan nasa.

Ita kanta tenya ajiyar zuciyar ta ringa jerowa ba kakkautawa kafin ta bude Baki da karfi tana cewa

‘MashaAllahhh,Barakallahu laka fi’l-mawhubi lak,wa shakarta’l wahib,wa balagha ashuddah,wa riziqta birrah.
ALHAMDULLILLAH YA ALLAH’ ta qarasa fada da karfi tana karban lallausan showel fari tas hannuwanta na rawa ta dunqulesa tana dawo da kallanta Akan Ayanah cikin rawar murya tace

‘Allah ya qara miki Nisan kwana da lafiya tareda albarka me dorewa UWAR BOYEM GABAKI DAYANTA TA YANZU,
UWA GA ZAKIN BOYEM,
UWAR MAZAJEN BOYEM,
UWAR ME BOYEM NA GABA.

Sakinah rawa jikinta ya dauka da karfin gaske tana juyowa da karfi ta tsira wa babyn hannun tenya din ido bata ko kyaftawa.

Ayanah ma duk da bata hayyacinta bata dawo daidaiba bude jajayen idanunwata tayi zufanta na qaruwa ta zubawa hannun tenya ido tana kasa gasgata da gaske namijin da qasar BOYEM da qasoshi da dama suke jira shi ta haifa,

Hawaye ne suke kokarin ciko idanuwanta na fargaba tsoro da tsananin tausayi da son danta da rikicin qasar gabaki dayanta yake jiransa.

A daidai wannan lokacin bangaren HAILE shima wani Tiriri ya dauka na samuwar cikar Buri dan kuwa itama namijin ne ta haifa Wanda ya sakata kokarin tashi da kanta dan isar da sakon haihuwar ‘da namijin ga sultan tin kafin Ayanaah ta haihu sbd farin cikin samun cikar burin shekaru ya mantar dashi Ayanah da kowa menene zata haifa.

Hanata Miqewa likita ke kokarin yi tareda yarta harma da fetto sbd jinin da babu sosai a jikinta kuzari tareda azabtuwar datai sosai tayi pale sosai suka dage cikin tsananin kulawa da kauna dan komai ze iya faruwa da ita idan ta tashi tsaye amma Sam taqi yadda da hakan rungume take qam da babyn tana kokarin Miqewa zuciyarta a rufe bata Jin ko zata rasa ranta zata iya jiran Ayanah ta haihu batareda sultan yafara sanin ta haifa Zakin qasar BOYEM ba,

Miqewa tayi suka miqe dukansu tareda riqeta zuciyoyinsu da hankalinsu duka a tashe da mugun tsoro da tashin hankalin hukuncin laifin da suke kokarin aikatawa na Binta su fita,

Wani jinin ne ya kuma gangarowa daga qafafunta Wanda ya saka hankalinsu sake tashi dake sauri bayi biyu sukai saurin durqusawa suna goge mata jiki da towel me dumi da suka matse daga ruwan Zafin da aka goge mata jiki gabaki daya.

Sake shiga tashin hankali su fetto da likitar sukai harma da ‘yarta sbd hatta ita Haile din hukunci zai iya hawa kanta dan babban tsatsauran dalilin daya saka wannan tsaurin yake a masarautar lokacin haihuwan kwace mace shine hana cutatar da kowace jaririn da zaa haifa ko uwarsa kokuma sace jarirai musayarsu dan haka baa yanzu wannan dokar take ba tin asalin asalin kafa masarautar yake.

Jiri ne sosai da rashin isashen jini ke Neman zubar da ita amma a haka suka riqeta dan suma bazasu taba son imebetin ta haihu batareda sultan yasan an samu magajin BOYEM ba,

Taku daya biyu sukai suna daga qafafunsu su hudun a tare zasu fito dakin wata kakkarfar sautin qarar da baa taba kada wa ba tin tsawon shekarun da sultan YASAR ya hau mulki bace ta ratsa kunnuwansu cikin sanyi da rikitaccen yanayin daya saka dukkaninsu Sakinta cikin mugun firgita da ficewa hayyacin dan kuwa sautine dayake fadawa BOYEM da duniya gabaki daya MAGAJI kuma ZAKIN BOYEM ya sauka a duniya tsohuwar imebeti sabuwar wishmah AYANAH GHAZ ta haifosa.

Shigar sautin kunnuwan Sultan YASAR da gabaki daya manyan masarautar boyem a lokaci daya suka zube qasa suna yiwa Allah sujjada batareda ma sun sani ba,

Haile kuwa Numfashi daya ta fitar bugun zuciyarta ya tsaya cak sakamakon sautin sakon daya ratsa kunnuwanta ya Harba cikin kwakwalwanta ta zube a gurin jaririn hannunta yana subucewa daga hannunta zuwa qasa,

Cikin wata gaggawa da tashin hankalin dayake Ninkuwa Akan mugun shock din dasuke ciki fetto ta tare babyn koina na jikinta na rawa da kakkarwa,

‘Yarta Aslam ce tayi saurin tarota jikinta itama jikin nata yana rawa sosai da firgici tareda tsananin tsoro sukai qasa har ita har mahaifiyar tata sbd batada karfin da zata iya riqeta tinda jikinta a sake yake kaman babu rai a jikinta,

Dr Kadee ce tayi saurin bin Aslam din qasa tana tayata riqe Hailen itama jikinta rawa yakeyi da firgicin yanda duk wahala da azabar da suka sha ta tashi a iska labarin haihuwan Ayanaah ghaz ya fara shiga kunnuwan sultan YASAR da qasar BOYEM harma da duniya gabaki daya.

Fetto babyn ta rungume jikinta tareda budesa sa sauri taba duba idan yana raye babu abinda ya samesa daga faduwar taga lafiyarsa kalau sedai tinda aka haifesa baya wani kuka saida ya fadin ya fasa kuka sosai Wanda ya sakasu sauke ajiyan zuciya suna tattalar HAILE din dan maidata shimfida a bata taimakon gaggawa.

***A daidai wannan lokacin kuma sautin qarar ya ratsa kunnuwan Zuhrah dake Zaune daqyar sbd azaba da rashin lafiyar da kowace gabar jikinta keyi a cikin wani irin kurkuku mara Kyan gani,

Tinda aka sanar da Masarautar kaf cewa imebeti AYANAH GHAZ na naquda ta tashi Zaunen idanuwanta dake ciwo basa gani sosai ta bude su tareda daga Kai sama ta qurawa sama ido tafara jerowa Ayanah da abinda zata haifa addua jikinta na rawa tana fadawa Allah adduarta Akan yar uwarta
Bata Dena addua da fadawa Allah ya tsayu Akan rayuwar babyn ayanah dinta ba har saida sautin ya ratsa kunnuwanta Wanda ya sakata rufe idanuwanta ahankali tana silalewa qasa kwance tareda fashewa da Wani irin kuka mai ratsa zuciya tana gode wa Allah da bai karbi ran ayanarta gurin haihuwa hakama wata irin tsananin kewarta da kaunar son ganinta a lokacin ta saka sabbin hawaye gangaro mat a tana Jin tsananin so da ganin abinda Ayanah ta haifa musu ta rungumesa a jikinta taji duminsa tareda sakawa rayuwarsa albarka da fada masa sun yafe masa ita da ‘yan uwanta da basa raye sbd kaddarar haihuwansa a jinin BOYEM ce ta lalata tasu rayuwar da babu gyara a cikinta har abada.

Rufe idanunwata tayi hawayen data manta rabon datai yi su sbd kuka ma kansa ya gujeta sai Ayau din datake Jin kewa da tsananin son Ayanah da ‘danta suna ratsata.

****A kuma wannan lokacin ne sultan YASAR ya dago daga sujjadarsa ya daga hannu sama yayiwa Allah godia yana jerowa dan nasa addua me tsananin karfi,
Chapter 42 · 0% Book details