← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 76

Sashe 70

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar saukar gudu ma a tsakiyar kanta taji saukar zancen Wanda ya saka idanuwanta qarasa rasa ganinsu ta kafesu Akan Sarkin fada tana bude baki kanta na mantawa da komai Bayan son ganin mahaifinta da sautin daya saka Aleey dagowa a cikin wani irin yanayi me sanyin jikin auren da aka daura amma ya kasa kallanta sbd a yanzu da igiyoyin auren ubangidansa suka riga suka hau kanta idanuwansu bazasu iya mata kallan Kai tsaye batareda girmamawa ba koda kuwa aure ne da a yanzu baida suna bare matsayi kwata kwata a rayuwar me BOYEM din dan kuwa bai dauka auren ne shima yayi ba abu daya ya sani koma menene yayi sa ne dan tabbatarda karban Abaas Wanda yake rayuwar Amminsa.

‘Yet niw Abaa,yet niw Esu?’ Ta fada idanuwanta na kafe Akan Sarkin fada Wanda ya sauke Numfashi me tsananin sanyi da mutuwar jikin rabuwar da zeyi dasu a lokaci daya babu shiru babu sani ba tareda tinanin hakan ba dan ya dauka shine zai shafe Abaas da kansa ya kuma zama uban BAHAR din wadda zai aurar da ita ga nasa dan amma ko a hakan baiyi baqin ciki ba sbd shi kansa zaifi farin ciki idan Abaas yaje amma idan har hakan shine zai hada Abaas da Ayanaah to wannan shine gatan karshe da zai masa shi da Bahar wadda batasan kowaba a dangin uwa da ubanta ba.

Tasowa yayi ya iso gaban Bahar din zai furta sunanta ta ja da baya cikin wani irin mutuwar jiki da mafi girman tashin hankalin rayuwarta tana girgiza Kai ta sake furta sunan Abaa dinta idanuwanta na yin wani irin ja hawaye masu tsananin zafi na taruwa a cikinsu sbd kadaici ze kasheta idan Abaa yabarta shine kadai ran dayake cikin empty rayuwarta da babu kowa a ciki sai zallan sunayen da babusu maana yan uwan mahaifin nata da iya sunansu ne basu ba a rayuwarta.

NUAB da idanuwansa suke rintse tin lokacinda aka shafa fatihar auren dago kansa yayi ahankali yana bude idanuwansa da sukai jajir ya saukesu Akan fararen kafafun dasuke gabansa masu haske sosai na daukan hankali sarkar Farin azurfan dayake kafar duk motsinta daya na ja da Bayan datake Wani sauti me yar qarar dake shiga kunnuwansa yake fitarwa Wanda ya sakasa dauke jajayen idanuwansa zuciyarsa na Wani irin Zafin lokacin daya bata na cetan Abaas a gurin daurin auren da bai dauru ba a zuciya da rayuwarsa dan kuwa aure ne kadai na biyan buqatar wannan lokacin da suke so na tafiya da Abaas dan haka miqewa yayi batareda ya juyo ya kallo kowaba ya nufi kofa a takunsa na natsuwa da jinin mulkin daya dame sarautar GHAZ ya fice batareda ya cewa kowa komaiba.

Yana ficewa Aleey ya miqe shima yabi bayansa Bayan ya dan kalli Maa sakinah dake Bayan BAHAR da Sarkin fada yace suna jiransu a waje.

NUAB na fito bike din dake nan Sauran daya daya raye shi ya hau Kai tsaye ya wuce aka bar GHAZ din dashi.

Su aleey sai Sauran bikes din sun dawo da sukaji kai Abaas dan haka Aleey fidda wayar sa yayi yafara zagaya masarautar yana daukan videos din dayasan buqatan hakan zata iya tasowa daga baya dan haka ya bawa Maa sakinah da Sarkin fada guri da zasuyi magana da Bahar wadda babu abinda take son ji da gani kawai idan ba mahaifinta ba dan mantawa ma kwakwalwanta tayi da abinda taji na maganar auren da kunnuwanta sukaji an daura da sunanta kawai mahaifinta takeso da ganin idan ba tafiya yayi ya barta ba dan haka ta rikice musu gabaki daya Wani irin rawa jikinta keyi tana ambatar sunansa da karfin gasken daya saka a rikice aka fiddota aka tafi da ita zuwa garesa Bayan Sauran bikes din sun dawo.

Sbd yanda Bahar din ta fice hayyacinta tana kasa yadda da kowa harma da Maa sakinah ya saka dole da Sarkin fada aka tafi dan rakiya garesu.

Koda suka nufo wajen gari idanuwanta tsananta jajir sukeyi cikin wani irin nauyin kirji na zuciya take jinta duniyar na sake mata duhun da tasan itama kila a cikinsa zata rayu ta mutu kaman yanda mahaifinta ya rayu ya tsufa a cikinsa.

Koda suka iso an bawa Abaas taimakon gaggawan dayake buqata amma suna buqatan gaggawar isa dashi asibiti Wanda Dr ya bada shawarar bazai iya kaiwa qasar BOYEM a hakan ba dole suna buqatan fita can cikin babban birnin wannan qasar da suke ciki su fara tsayawa anan dashi asibiti saiya samu dan saukin da zai iya qarasawa dashi qasar BOYEM indai anason ya rayu.

NUAB baida raayin tsayawa kowace qasa dashi Bayan BOYEM amma kuma ga yanayin jikin nasa dayake gani dole maganar Dr din zasu bi ta tsayawa asibitin qasar kafin daga baya su wuce idan ya dan zama stable sbd mummunan nisa yayi Wanda yake girgiza zuciyar NUAB din yanajin kaman bazai taba iya fuskantar Amminsa ba idan Abaas yabar duniya sbd baisan tayaya har abada zai iya fada mata Abaas dinta ya tafi yabartaba dan hakan shine blow na karshe da rayuwarta zata iya samu dan haka zaiyi iya kokarinsa yaga ya isar mata BOYEM dashi koda ganin karshe ne su yiwa juna.

Kai tsaye barin ruwan dajin ANJOM GHAZ sukai Wanda kila shikenan sun barsa a rayuwarsu,
Sakinah tsirawa dajin ido tayi bata kyaftawa zuciyarta na narkewa fiyeda a baya ANJOM shine garin da har su mutu bazasu Dena marmarin dawowa su qarasa rayuwa a cikinsa ba.

Bahar ma dake Zaune gaban mahaifinta hannunta ta saka ahankali cikin nasa ta Kama tareda hade tafin hannuwansu tana Lumshe idanuwanta da sukai jajir wasu hawaye masu dumin cikinsu suka gangaro mata Sarkin fada ma kusa da ita su kadai a dakin dayake Sarkin fada na fada mata ‘dan Ayanar mahaifinta ne Yazo ga mahaifin nata dan basa lafiya.

Babu kowane irin farin ciki ko Jin dadi ko daya daya sauka ga zuciyarta na abinda Sarkin fadan ya fada sbd babu Sauran kowace kauna ko soyayyar datake Jin zuciyarta nada damar yiwa kowa sbd bata tashi da kowa ba a rayuwarta daga ita sai mahaifinta tayi rayuwa,
Rayuwa da zuciyarta a kulle take ga rayuwa da kowa a cikinta sbd kadaici da quncin data taso a cikinsa na rayuwa babu uwar data haifeta wadda ta rasu a ranar data kawota duniya hakama tasowa ta rayu a cikin duhun gidan da babu kowa a cikinsa sai ita da mahaifinta Wanda shima tinda ta bude ido duniya take kallansa cikin qunci da tarin baqin cikin daya hanasa lafiya har yau da rayuwarsa take cikin tsakiyar rayuwa ko mutuwa dan haka zuciyarta da rayuwarta a mace suke ta yanda basuda komai ciki da zata iya farin ciki dan haka rufe idanuwanta tayi ahankali wasu Zafafan hawayen na sake gangaro mata tana fadar idan lokacin mahaifinta ne yayi Allah ya dauki ransu a tare subar duniyar a tare.

Tafiya me tsayi sukai kafin suka isa bakin bodar qasar babu bata lokaci aka fito dashi zuwa ambulance da already ankira tana jiransu dan haka take ambulance din ta daukesa tareda Bahar din a cikinta da Sarkin fada su kuma Sauran motocin suka shiga a guje akai asibiti dashi.

Suna isa aka karbesa da gaggawa akai ciki dashi suka bisu jikin kowa a mace musamman BAHAR wadda zuwa lokacin ko kuka bata iyayi sbd babu alamar sauki ko kadan a lamarin nasa.

A inda ake jira suka zazzauna Banda NUAB da aleey wainda aka kaisu guri kebantacce dan jiran dan hakan har lokacin babu Wanda yayi noticing juna a tsakaninsu.

Maa sakinah ce Zaune a gefen Bahar din wadda kanta yake qasa ta dunqule hannayenta guri daya idanuwanta jajir.

Hannu Maa sakinah ta Dora a hankali kan na Bahar din tareda kallanta cikeda kulawa da kauna me karfin gaske tareda tausayi itama idanuwanta jajir batareda tace komaiba,
Itama Bahar din bata dagoba sedai rintse idanuwanta datai hannuwanta na tsananta rawa Maa Sakinta ta riqe su cikin nata gam alaman bata sassauci.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

65
Zaman da kowace daqiqa take tafiya da tsananin bugun zuciyarsu da zullumi tareda tsoro me tsanani da fargaba sukai na kusan wuni guri kafin aka samu numfashinsa ya dan dawo daidai da oxygen hakama jini aka daura masa Wanda yake na NUAB dinne da kansa aka diba Bayan ya hana Yaransa bada nasu nashin yakeson a sakawa Abaas sbd a shirye yake ga bada jininsa gabak daya idan zaa buqata hakan dan Abaas ya rayu sbd kila Amminsa zata iya juriya da karfin zuciyar rashin sa amma bazata iya daurewa rashin Abaas ba.

Idanuwan Bahar sunyi munin da suka sauya kamanninta koina nata yayi jajir sbd kuka da damuwan datake gap da buga zuciyarta da babu kowa a ciki sai BAA din,

Sakinah dik da tana cikin mummunan tashin hankalin itama amma ta daure ta fidda karfin halinta a matsayi na uwa dake gurin ta bawa BAHAR dukkanin kulawa da kaunar datake buqata a daidai wannan lokacin Wanda hakan ne ya dan rage zarewan da yarinyar ke kokarin yi a Zaune gurin.

Shi kansa NUAB babu Wanda ya gansa a cikinsu dan hakane ma basusan jininsa ne aka sakawa Abaas dinba,
Aleey kadai suka gani shima abinci lafiyayye kusan Kala biyar ya saka aka kawo musu Wanda babu Wanda suka saka a Bakinsu
Duk yanda Maa sakinah tayi Bahar taci Sam ko sakewa babu a tsakaninsu da zata iya ma cusa kanta dole taci ba dan haka bata ci komaiba fatarta mahaifinta ya tashi ya samu lafiyar da zasu koma inda suka fito suci gaba da rayuwarsu su qarasata a tare su biyu kadai.

Dare na yi haka aka daukesu aka kaisu masaukin da yanda Bahar taga rana haka taga Daren batareda ta rintsa ba a Zaune take har asuba idanuwanta sunyi mummunan kumburan da kanta ke tsananin ciwon da ko gani sosai batayi amma Sam ba sassaucin datake ji a zuciyarta.
Chapter 70 · 0% Book details