← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 76

Sashe 16

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jijjiga da fizga jikin Ayanah yakeyi bama rawa ba ta bude Baki da karfin gaske Tana kwala kiran Nurat wadda take Ihun itama sosai.

Abaas harshensa yake cizo yana wani irin gurnanin kiran Yar uwarsa a zuciya jini na fitowa bakinsa sbd mummunan tashin hankali da yanda yake cizan harshensa.

Zuhrah Neman zarewa takeyi itama kaman Nurat Tana qwala kiran Nurat qafafunta na kasa daukanta.

Sakinah ma kuka takeyi sosai zuciyarta na bugawa kaman zata fado,

Miqewa tsaye Ayanah tayi cikin tsananin duhun tana kokarin taka mutane ta isa kofar ta kife sbd sarkar kafarta amma bata tsaya komaiba jikinta na tsananta rawa ta sake miqewa kwala kiran Nurat da karfin daye amsa dakin dukansa har sama inda Nurat din take Tana sake faduwa taba sake tashi tana taka mutane hankalinta gabaki daya ya gushe daga jikinta Ihun kiran Nurat takeyi Tana jin kaman mutuwa zatai a lokacin,

Ihun Nurat dinne yafara ratsosu itama cikin tsantsar azaba tana kiran Ayanah da sunan Ammah muryanta ba dadin sauraro.

Isowa setin kofa Ayanah tayi tafara bugawa da hannuwanta tana wani matsanancin kukan da ihu,

Yanda take bugawa hannuwanta duga biyun da karfi batareda damuwa da yankewan da hannun keyi ba ga qusa dake jikin gurin Tana fasa hannuwanta jini na fita jin kawai takeyi tamkar ranta ne zai fita idan rayuwan Nurat dinta ta lalace.

Kukan datake yi Sam bata hayyacinta sbd da a gabansu ne ake kokarin hakan da yau duka zasu bar duniya sbd bazasu tsaya kallo ba zasu qwaceta koda hakan na nufin rabasu da ransu.

Jini sosai taje fiddawa a hannuwanta amma ta kasa denawa sbd bata ma Jin Zafin komai kukanta na qaruwa sosai har maqoshinta na kasa fidda sauti.

Abaas da Zuhrah harma da sakina da suma kowa ke cikin mummunan Hali suka rarrafo basa gani zuwa inda sautin muryan Ayanah din yake fita
Zuhrah ce tayi saurin riqeta Tana rungumeta sbd jinin dataji hannuwanta nayi data lalabo ta tareda fasa sabon kuka itama jikinta na fizga,

Abaas ma Kansa yake bugawa a kofar yana wani irin kuka zuciyarsa na yagewa tako ina da radadi me yawa ga bakinsa bazai budu ba dai harshensa yake taunawa yana jini yana cigaba da buga Kansa a kofar,

A daidai lokacin da Nurat ta qwalla wata mummunan qara wadda take tabbatarda azaba ce ta keta ta da akai da wasu irin surutai da khams ke sakewa a cikin kunnuwansu suna ratsa zuciya da kwakwalwansu take kowannensu ya silale qasa suna yin tsit sedai sakinah ce ta saki wani irin kuka a lokacin Tana riqe hannuwansu su duka ukun a cikin nata duka biyu sbd yanda suke jijjiga batareda sun iya sake kowane irin yunquri ba alaman zuciyarsu bugawa zatai ko ta dauke wuta,

A cikin kunnuwansu sautin duk abinda khams keyi yake sauka tareda kukan Nurat dake fita har tayi tsit babu kowane irin sautinta sai nasa Wanda duk abinda yayi da ita kunnuwansu sunji musu Wanda kuma sauti ne da zai zauna a kunnuwansu da zuciyoyinsu har abada har ranar da jinsu zai dauke Bayan rai ya fita a jikinsu,

Zuhrah juyewa kanta yake yi itama sbd dukan da zuciyarta ta samu mummunan dayake Neman buga zuciyarta.

Sakinah rungumesu tayi da hannuwanta Tana qanqamesu kukanta na tsananta sbd yanda dakin yayi tsit kowane bawan dake jirgin ranar duk da halin da suke ciki kukansu Ayanah din ya sanyaya jikinsu tareda hawayen tausayin qaddadarsu su duka da basusan ya zata qare ba.

Ayanah zubewa tayi jikin sakinah gabaki daya jikinta na saki idanuwanta na kasa Juyawa ta koma kamar wadda aka zarewa komai aka Barta da rai kawai.

Jin hakan sakinah ta sake rungumeta jikinta kukanta na tsananta Tana Jin inama a ranar da suka so kashe kansu ta barsu sun mutu sun bar duniyar da sun huta da ganin wannan balain da daace iyayensu na raye mutuwa zasu yi idan suka Ji wannan mummunan ranar.

Tsit babu Wanda ya iya ko dogon motsi a dakin kwata kwata kaman yanda babu Wanda ya sake Jin ko kukan su Ayanah ne dukansu sun mutu a inda suke babu abinda ke motsi a jikinsu Bayan zuciya dake bugawa.

Gap da asuba aka bude dakin Wanda ya saka su Ayanah daga Kai ahankali suna kallo aka turo Nurat wadda Kayan jikinta gabaki daya suke a yage harma kusan Rabin jikinta duka a bayyane.

Abaas ne ya Tara hannuwansu biyu ya tareda ta fado jikinsa ya rungume ahankali yana rufe jikinsa ta inda jikinta yake bayyane yana sake rungumeta tsamtsam.

Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga idanuwanta Wanda ya sauka tafin hannuwan Zuhrah data motsa zata tabata,

Saukar hawayen nata ta saka Zuhrah kallan fuskanta cikin duhun bakinta na budewa da tsananin sanyi tace

‘Nurat,Yene(my/tawa) Nurat,Yene fikir(love/masoyiya)
Nurat Rabin Raina.’

Wasu sabbin hawayen ne suka gangarowa Nurat din Tana son Dora hannunta Akan na zuhrah din ta kasa dan haka ta rufe idanuwanta bakinta daqyar ya iya budewa tace

‘Ammah’

Kalmar yanka zuciyar Ayanah da dukkaninsu tayi Ayanah ta rufe idanuwa hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mata ta motsa hannuwanta dake rawa ta Kai fuskar Nurat din taji wani abu yana gangarowa ta hancinta Wanda ta tabbatarda jini ne yake fitowa ta fasa wani irin wahalallen kuka Mara sauti tareda Kai fuskanta ta hade data Nurat din tayi sumbaci goshinta ta sumbaci hancinta tareda sarqe hannunta da nata Tana kasa furta komai sai sumbatar hannunta taje yi tana wahalallen kuka Mara sauti jikinta a mace gabaki daya ba karfi ko daya.

Zuhrah hannuwanta ta kasa janye wa daga hawayen Nurat din dake zuba suna zuba a hannunta itama kukan takeyi sosai kaman ranta zai fita mara sauti,

Nurat data dawo hayyacinta Tana jinsu amma babu inda take iya motsawa a jikinta sbd jininta dayake qarewa yana qarasa zubewa sbd tin acan take zubar da jini sosai haryanzu sosai yake fita a jikinta batareda yan uwanta sun saniba duk da ko sun sani basuda abinda zasu yi sedai zubawa sarautar Allah ido.

A haka suke Zaune kowannensu kuka ne na fitar hankali sukeyi mara sauti har lokacin Abaas yana rungume da ita cikin jikinsa hakama Ayanah na riqe da hannunta tana sumbata Tana kukan da shi Kansa kukan ya gaji sai Zuhrah dake tare hawayenta da hannuwanta duka biyu kowace diga yanka zuciyarta yakeyi,sakinah ma Tana Bayan Ayanah kuka takeyi kawai tana kusan abinda dukansu suke Ji,

Gari ne yi yi haske sbd safiyar datai dan haka duhun dakin ya ragu sosai suna iya kallan fuskanta kuma har lokacin babu Wanda yayi hayaniya ko doguwar motsi a dakin sbd duk da suna qangin bauta suna sheda tsananin kauna da son da yan uwan kewa juna kaman rai,

Ahankali Nurat din ta sake bude ido ta zubawa Abaas Wanda ya kasa kuka sedai jinin dake fitowa daga bakinsa idanuwansa sunyi jan da gap suke da fara fidda jini,

Hannunta ta daga daqyar yana rawa sosai ta share masa jinin bakinsa Tana kallan cikin qwayar idanuwansa hawaye suka sake gangaro mata ta kasa iya cewa komai kafin ta dauke idanuwanta a galabaice tanason kallan Zuhrah da Ayanah amma Allah bai bata ikoba jikinta ya sake ahankali ranta na fita.

Dukansu babu Wanda ya motsa sbd tashin hankalin daya wuce Kai tsaye cikin kansu ya sanqarar da komai nasu,

Sakinah ma mutuwar Zaune tayi dukansu suka dauki mintina a hakan kafin Ahankali Ayanah ta motsa tana tallafo fuskan Nurat din datai haske sosai tareda duka jikinta sbd jininta daya gama tsiyayewa tas ta hade fuskanta da tata muryanta na rawa tace

‘Nurat rayuwata,
Nurat hasken rayuwata,yene Nurat,Nurat kece kuzarina,
Nurat kune haske da kuzarin rayuwata da ruhina da bazan iya rayuwa babu ku ba,
Nurat kune karfin daya saka zuciyata take bugawa haryanxu batareda ta tsaya ba,
Nurat ke suka keta amma mu rayuwar ce aka keta sbd kece rayuwarmu,
Nurat ki bude idanuwanki ki kalli halinda muke ciki
Bazamu taba dawowa daidai ba har abada idan babu ke koda kuwa mun samu sauyin rayuwa,
Nurat,Nurat…….wani irin kuka me tsananin jijjiga duk me saurare da ratsa zuciyar kowane dan Adam dazai jisa ta sake Tana sumbatar tsakiyar kan Nurat din da goshinta kafin ta rungume kanta a kirjinta tana rufe idonta kukanta naci gaba da fita.

Zuhrah ma hannunta Nurat din ta riqe ta sumbata Tana rungumewa kukanta na fita da tsananin kashe jiki,

Abaas a kirjin Nurat din shima ya kife Kansa a Karan farko da sautinsa ya fita Bayan tsawon watanni yana fasa wani irin kuka mai tsananin taba zuciya da narkarwa.

Basu taba tunanin samun kansu a cikin wannnan mummunar halin ba da zasu rungume gawar daya daga cikinsu ba a Hali mafi muni irin wannan,

Koda iyayensu suka bar duniyar sun mutu a hanyar Neman tsira da sauran mutuncinsu,
Amma ayau Nurat ta rasu tabar duniyar da ciwon baqin cikin abinda ya faru da ita,
Bata rasu ba saida tashin hankalin data fuskanta ya dawo da hankalinta jikinta dan hakanne baqin cikin abinda y sameta dashi ta rasu a ranta dole.

Kaman yanda Baqin cikin rashinta bazai taba barinsu ba hakama harsu mutu sautin kukanta a lokacinda ake keta haddinta bazai taba fita daga kunnuwansu da zuciyarsu ba shikenan ya musu rauni a zuci.

Har rana ta keto suna rungume da gawar Nurat sun kasa sakewa saida aka bude su dan basu abinci,

Jeho abinci akeyi masu karba na wawason karba amma babu Wanda ya motsa a cikinsu suna rungume da ita har lokacin babu Wanda idanuwansu ke Dubuwa sbd kumburi da ja.

Saida aka gama Rabon abincin a daidai lokacin suka iso qasar hidua jirginsu ya tsaya a bodar qasar zaayi abinda aka Saba tukuna aka shigo dan diban bayi Sai a lokacin akasan da akwai gawa a cikin gurin.

Zabar bayinsu suka fara yi wainda zasu siyar suka fitar dasu kafin suka dawo suka dauki gawar wadda aka cire daqyar a hannunsu Ayanah da suka riqeta gamgam dukkaninsu ganin bazasu sake ba aka dauko Bulala aka fara dukansu da karfi jikinsu na fashewa amma har lokacin kasa sake gawar sukai.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

16
Chapter 16 · 0% Book details