← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 76

Sashe 68

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadawane suke gadin masarautar amma tsirarru Wanda yake nuni da Masarautar batada karfi ko Kwata kwata tinda garinma duka ba Wani karfi bare Ayi mulki me karfi.

A fada suka zauna nan Sarkin fada ya shigo yana kallansu tareda zubawa NUAB idanunwata kaman zasu gado sbd ganin kammanninsa da jinin GHAZ dayake Neman shafewa daga Yauma kila sbd jikin Shugaba yau yayi tsananin da sai Allah.

Kwarjinin NUAB ya saka shine ya gaidasu yana musu Barka da zuwa maimakon su su gaidasa sbd shine kila me mulkin GHAZ anan gaba.

Aleey cikin nutsuwa shima ya dan gaidasa da yarensu Wanda NUAB yakeji sosai sbd mahaifiyarsa dake masa tin yana yaro hakama Maa sakinah shikuwa ya kullafa saida ya iya yaran shikuwa aleey baya wasa saida ya iya shima sbd uban gidan nasa da idan ta Kama.

Kaman daga Sam Kai tsaye NUAB yace

‘Menene sunan shugaban jinin GHAZ daya rage a yanzu???

Da mamaki Sarkin fada yace

‘ABAAS GHAZ sai ‘yarsa qwalli daya tak AYANAH BAHAR GHAZ sune suka rage jinin GHAZ a duniya…

Wani bawa ne ya fado fadar da sauri yana zubewa qasa yace

‘Sarkin fada jikin Maigirma yana sake tsananta kana buqatan zuwa.

Miqewa Sarkin fada yayi yana barin gurin a rikice Wanda ya saka Kai tsaye NUAB miqewa yabi bayansa sbd kowane Hali Abaas din Amminsa yake yanason ganinsa.

Sarkin fada na saka Kai dakin NUAB ma yana sakawa idanuwansa suka sauka Akan fuskar datake sak da sak data mahaifiyarsa.

Abaas dake aman jini ahankali dagowa yayi idanuwansa na sauka Akan NUAB take ya dauke wuya komai nasa na kokarin tsayawa cak yayi baya zai zube

Taku biyu NUAB yayi ta tarosa jikinsa yana Jin dukkanin nauyin dake zuciyarsa yana qaruwa da ganin sanyin idaniyar mahaifiyarsa a wannan halin.

Feso Wani jini Abaas yai da karfi cikin azabar dayake kasa riqewa NUAB ya katse azabar ciwonsa da cewa

‘NUAB ALMAZZ ‘da ga AYANAH GHAZ……

Rintse idanuwana Abaas yayi cikin wani azababben yanka daya ratsa zuciyansa data gama yanke kauna da yan uwansa har abada musamman yanzu dayake kan gadon mutuwarsa,

Riqosa NUAB yayi cikin rashin bata lokaci sbd kafin komai yana Abaas din na buqatar likita da gaggawa,

Girgiza Kai Abaas yayi cikin wani mummunan rashin kuzari da ciwon da baida sassauci ke kadan ya damqi hannun NUAAB din da karfin gaske yana jan Numfashi da qyar yace

‘Ayanah tana raye???

Cikin sauri NUAB din ya Gyada masa Kai tareda bude baki yace

‘Kana buqatan likitan dazai duba lafiyar Ka da gaggawa daga baya duk zamuyi magana amma Ka sani Amminah tana raye,
Tana son ganinka itama kafin tabar duniya dan haka kada Ka tafi Kabarta zuciyarta bazata iya daukaba sbd kaine hasken zuciyarta da idaniyar Abaas ghaz.

Girgiza Kai Abaas ya sake yi yanajin kaman bazai iya ko minti dayaba a duniya dan haka koma yayane Allah yayi masa rahama ne tinda Sauran ransa daya kawo masa dan Ayanaah zai cika a hannunsa Bayan burinsa na hada jini da Ayanarsa ya cika Akan gadon mutuwarsa.

Sake qanqame hannun NUAB yayi yana bude baki daqyar yace

‘Ka cikawa mahaifiyarka Dani burin da muka tashi dashi na hada zuria da juna Ayau cikin Daren yau na mutu da nutsuwar na bada ‘yata daya tak ga jinin Ayanah……

Wani kallan rashin fahimta NUAB yayi masa yaja kallan aleey yace Ayi gaggawar daukansa dan tafiya dashi ga likita.

Abaas zamewa yayi yana sake dan girgiza Kai daqyar yace

‘Lokaci na yayi Allah ya yanke ganawata da Ayanah bazan Kai koinaba zan bar duniya,
Kokarin daukansa aleey yakeyi amma jikin sake rikicewa yakeyi dan haka ba bata lokaci Aleey ya fita ya fidda wayar sa ya saka kiran Sauran yaran yace a kawo Maa sakinah yanzu.

A lokacinda aka iso da Maa sakinah Abaas cikin tsananin ciwo da rashin karfi ya zayyanewa NUAB labarinsu tas Wanda baida dadin ji me tarin qunci da baqin ciki.

Nasa labarin yake kokarin Dora masa Maa Sakinah ta shiga kafafunta na Takawa ahankali cikin sanyi da rawar zuciyar dake gap da bugawa.

Suna kallan juna Abaas ya fashe da Wani irin kukan daya saka dakin yin tsit gashin jikinsu na tashi.
Itama Maa sakinah zubewa tayi qasa tana fasa kuka a gabansa koina jikinta na rawa tana kiran sunansa da sauti me ratsa jiki.

Bude baki yakeson yi ya Ambaci sunata da tambayar yan uwansa amma karfinsa yayi qasa sosai dan haka ta rarrafo da sauri tana bude bakinta dayake rawa cikin sautin daya sake saka gurin daukan tsit ta fara fada masa dukkanin halinda suka shiga har zuwa halinda ake ciki yanzu da Ayanah dake tsananin so da buqatarsa a rayuwarta.

Magana zeyi harshensa ya fara kokarin karyewa dan haka take aleey yace securities su daukesa Ayi gaggawar tafiya dashi.

Riqe hannun sakinah Abaas din yayi da karfin dayake na barin duniya yana kallanta daqyar ya iya furta ‘yata jinina AYANAH BAHAR….

Kasa qarasawa yayi jikinsa na sakewa gabaki daya.

Gaggawar fita dashi suke kokarin yi sbd har lokacin akwai Sauran rai a jikinsa
Sarkin gida na ganin hakan buga tsalle ya tare kofa tareda kiran fadawa yana cewa kada a Bari su fita koina da Shiguba da yarsa har sai ancika burinsa na auren yarsa Wanda hakan zai basu tabbacin kariyarta Bayan tabar nan sbd igiyoyin auren sa zasu tabbatar musu da zaa iya riqe amanarta matsayinta na ‘yar shugabansu hakama basuda tabbacin Ayanah din da gaske tana raye amma tinda ga ‘danta a gabansu bazaa tafi dasu ba saiya aureta koda Abaas ya rasu kafin akai to ta samu gatan zama Inuwar aure.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

63
Da Wani irin yanayi me ‘dacin gaske da jajayen ido NUAB da aleey suka dago dukkaninsu suka kalli Sarkin fadar Wanda ya sake tsayawa Akan maganarsa ba tsoro sbd wannan shine gatan da adalcin da zasu wa ‘yar shigabansu jinin GHAZ data rage a duniya a idanuwansu,

Su dai bazasu bi su ba hakama bazasu Hana a tafi da Sugabansu ba dan nema masa lafiya sbd yana tsananin buqatarta amma kuma basuda tabbacin zai rayu ko bazai rayu ba a yanda sukaga jikin nasa yayi nisa dan haka gwara ‘dan Ayanah kaman yanda ya fada ya auri Bahar ‘Dinsu a gaban idonsu ta yanda koda Allah bai tashi kafafun Abaas ba sunsan zaman aure zatayi a cikinsu ba zaman garari ba dan haka tsoro ya cire a zuciyarsa matiqar ba auren BAHAR zasuyiba gwara abar musu shigabansu ya cika a gabansu su dauki amanar yarsa wannan shine tsayuwarsu matiqar ba hakan ba kuma sedai a kashe su a tafi da Abaas da BAHAR Bayan ransu.

Kuka Sosai Maa sakinah takeyi tana Jin zuciyarta kaman zata fashe sbd idan Abaas yabar duniya Zuhrah ce kadai ta ragewa Ayanah wadda tafi tsananin kauna da son Abaas a rayuwarta fiyeda komai,
Tayaya Ayanah zata iya jure wannan rashin?

Sake qanqame hannun Abaas din sakinah tayi dake cikin hannunta tana rintse ido da sabon kuka me tsananin rasa zuciya.

Aleey da ransa ya gama baci gashi ba lokaci da gaggawar gaske suke son tafiya da Wanda shine rayuwar Ammmi,

Kallan Securities yayi da idanuwansa jajir yace su kawar da kowa har sai sun fice dashi.

Sarkin fada na Jin hakan ya sake tare hanyar tareda fidda wata irin mahaukaciyar wuqa a jikinsa me munin da zata zata aikaka lahira ba bata lokaci.

Wuqar sa ba komai bace a gurinsu sbd sunada wainda sukaci uwarta da ubanta a jikinsu Wanda zata katse jijiya take kafin kyaftawar ido kawai banbanci tasa dafin gaske ne a cikinta da shine zai kasheka bama kaifinta ba kila.

Bindiga suka daga cikeda rashin tausayi suka seta Sarkin fadar tareda Yaransa da suka taho suka zagaye kofar dakin da makamai masu hadari a hannunsa.

NUAB da jikinsa ke wata irin fizga sbd tsananin tsoron rasa Abaas Wanda shi kansa bayajin zai iya Hadiye radadin rashin sa sbd tsananin kaunar da son dayake masa tin kafin ya gansa sbd shine mutum daya da Amminsa tafi so a duniyarta da rayuwarta fiyeda kowa,
Ko shi kansa data Haifa baya iya gane tsakanin shi da Abaas wane tafi tsananin so dan haka da kaunar Abaas shima ya tashi a ransa hakama da ita zai mutu dan haka bazai taba iya barin ya mutu sakamakon rashin likita ba indai ba Allah ya Riga yayi anan zai cika din ba lokacinsa yayi kenan ba dan haka dagowa yayi da jajayen idanuwansa da sukai mummunan ja kamar ma hadda hawaye a cikinsu ya kalli Sarkin fada Wanda yaja baya kadan sbd tsananin kwarjini da shakkar NUAB din data dakesa zuciya da kafafu amma duk da hakan bayajin zai iya ja da baya Akan abinda ya fada sedai Ayau ya rasa ransa gurin tabbatarda gyara goben BAHAR.

Bude baki NUAB yayi da wata muryan data saka tsigar jikin Sarkin fada tashi gabaki daya yana sake Jin shakkar NUAB na shigarsa yace

‘Ku Bari na ceta rayuwarsa nayi muku alkawarin bawa rayuwarsa data ‘yarsa kariyar da matiqar ina raye sun wuce kowane matsayin da zasu fuskanci kunci ko rashin gata tako ina……..

Girgiza Kai Sarkin gida yayi yana kasa kallan NUAB din Wanda hatta fuskarsa tayi jajir jikinsa rawa yakeyi.

Aleey da zufa ke gangarowa umarni me Zafi ya bada Wanda ya saka aka taqa bindigogin zaa fasa kan Sarkin gida NUAB ya daga hannu daidai nan Maa Sakinta ta zube qasa itama tana fasa sabon kukan daya saka kowa juyowa ya kalleta ahankali da jajayen idanuwa Banda NUAB daya rintse ido hannuwansa dake dauke da Abaas suna wata irin rawar dake bayyanarda halinda zuciyarsa take ciki.

Cikin tsananin kukan data jima batai irinsa ba sakinah ta bude baki tareda dagowa ta kalli NUAB tace
Chapter 68 · 0% Book details