← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 76

Sashe 52

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shekarun da suka shude anyi su ne a cikin tinani da wasi wasin waye zai zama magaji a cikin jini biyu da sultan YASAR me mulki haryanzu daya haifa?

Akwai ‘dan asalin matarsa uwargidansa wato queen haile wadda take zuba taqama da ikon da kaf masarautar ake shakkarta Bayan sultan idan aka cire manyan fada wainda sune fada,
Itace macen datafi kowace mace daraja haryanxu a masarautar da wajen masarautar sbd tini aka shafe tarihin fada da tsantsar soyayyar da sultan yakewa wishmah dinsa wadda tarihinta yayi bacci gabaki daya bata cikin kowane lissafi,

Queen Haile ta karbi kowane irin iko,taqama da isar tsayawa ta tsayar da ‘danta ASIM ga zama cikakken mai jiran gado na karagar mulkin BOYEM kuma hakan ta Zaune dan kuwa masarautar da duniya gabaki daya sun gama shedar da hakan sun gama yadda da sanin ASIM ALMAZ ne Sarkin dazai mulki BOYEM Bayan sultan YASAR sbd shine a tareda mahaifinsa da qasar sa yanzu.

Rayuwa ta dawowa Masarautar BOYEM sabuwa dal da Kama hanyar cikar Buri sbd kowa abinda yake tsananin so ne yake ganin yana Kama hanyar samu musamman queen haile wadda komai datake tsananin so shine ta samu hawan ASIM ALMAZ kujeran BOYEM ne kadai ya rage mata Wanda shima a yanzu yanda take ganin kusancin ASIM din da sultan tasan bama zai taba Hana masa ba sbd ya manta cewan yanada wani magajin kwata kwata tinda bai taba yiwa kowa maganarsa ba tinda yabar masarautar da suke ganin kaman ma korarsa yayi amma aka boye cewan karatu ya tafi dan haka haile ta gama samun dukkanin abinda take so itada danta ASIM Wanda yake zuba nasa iko da mulkin a cikin masarautar sbd ganin shine sultan na gaba kuma hakan ne ya saka gabaki daya BOYEM shakkarsa akeyi da basa tsananin girma duk da babu tausayin Jamaa ko daya a ransa amma mahaifiyarsa ta koya masa boye hakan sbd sake samun damar haye matsayin da suke tsananin buri kuma a shirye suke tsaf da iya kashe kowace rai da zata shiga tsakaninsu da abinda suke so dan haka kowa yasha jinin jikinsa akansu,

MARAKI ma a yanzu ta rasa dukkanin power datake ita sbd haile ce me yaya take zuba iko da mulkin cikin gida,
Hakama imebētis kaf da yayansu da duk wani me matsayi a cikin gida tsananin tsoronta ya ninka a ransu sbd a yanzu itace uwa ga sultan na gaba dan haka babu me iya ko dago Kai ya kalleta komai na mulkin Masarautar ma ya qara tsanani da wasu irin dokar da bayi basuda shaqat ko kadan.

MARAKI duk da daman can kishin tsagwaron soyayyar data hango sultan yana yiwa wishmah da ‘danta ne suka sakota gaba ta sakawa zuciyarta zazzafar kiyayyar Ayanah da NUAB sbd bata taba kishin haile ba dan bata taba ganin soyayyarta data ‘yayanta a idanuwan sultan YASAR ALMAZZ kaman yanda taga wutar son Ayanah da danta naci a idanuwa da ruhinsa ba dan hakan a yanzu data shedar da sunyi tazarar da babu Sauran soyayya a tsakaninsu hankalinta ya dan kwanta ta tattara komai ta ajiye ta koma rayuwarta ta Hutu da kwanciyan hankali bata shiga matsalar da duk ba tata ba dan kuwa ko taya HAILE kishin nema wa danta mulki batajin zata iya sbd sanin ba lallai komai Yazo a sauki ba dan tayi imanin da idan ma sunyi nasarar cire Ayanah a idanuwan sultan to ba lallai sun cireta a zuciyarsa ba bare LEUL NUAB dayake jinin AYANAH GHAZ bazai taba fita a zuciyarsa ba dan haka ta cire kanta a wannan fadan iya abinda ta samu ya isheta ita a yanzu dan haka rayuwa sabuwa ta bude itama ta kwanciyan hankali da nutsuwa,

Imebētis din sultan kuwa da damansu ahankali ahankali sun rasa rayukansu a hannun uwar dakin tasu wadda a yanzu Bayan ita bata buqatan kowace mace a rayuwar sultan Wanda ya rufe shafin karban kowace imebētin a rayuwarsa tinda ya samu Ayanah ghaz kofar shaawansa ga kowace mace ta rufe kwata kwata matansa ne kadai suma haqqin su ne kadai yake saukewa gashi rayuwar ma tayi tsayi yanzu tsufa da manyanci ya taho musu,

A yanzu imebētinsa daya ce rak a raye itama ta jima da komawa tamkar baiwa ga haile ta zama kunnuwanta na dauko mata labarai da sirrin duk inda Hailen bata saniba dan hakanne take raye kamar fanko dan kuwa shi kansa sultan din tintini ya mance da ita baama maganarta a haka zata gama garari a masarautar ta tsufa ta mace,

MARAKI batada kowane irin amfani itama a gurin sultan Bayan na biyan buqatan sauke hakkin aure a ganin HAILE kenan Shiyasa bata damu da ita ba ta tattara ta watsar tinda batada ko ‘dan kanta a duniya kuma tanada daman daukan ‘ya daya ko biyu ma daga cikin yayan imebētis din sultan ta riqe tamkar ta haihu amma Sam batada raayin hakan tin acan baya da akwai Sauran yarinta bare yanzu da duka sun manyanta hakama yaran da yawansu gabaki daya an aurar dasu Masarautu manya masu daula da iko daban daban gabaki daya a yayan sultan din manyan yayansa ne kadai basuyi aure ba wato yayan Haile su biyu Aslm da meryam ta ukunsu neesat tayi aurenta sbd rayuwarta akwai sauki sabanin ta yan uwanta,

Rashin aurensu nada nasaba ne da rashin shaawan auren da basu da shi sbd raayin hakan da mahaifiyarsu ta cusa musu sbd batason su taba aure Masarautar da batai ko kusan matsayin ta mahaifinsu ba,

Duk masarautun da ake aurar da yayan masarautar BOYEM basuyi ikon Masarautar boyem dinba sbd ta boyem din itace wadda babu kamarta dan hakanne dole sai wadda bata kaitaba amma suma Masarautun baa baya sukeba ko kadan ga tarin arziki da dukiyar da bata Jin kashewa tareda iko da mulki me karfi ta qasashe daban daban amma duk da hakan HAILE ta kasa barin yayanta su zaba ko daya daga cikin duk masauratun da ake kawo musu tayin aure gashi a al’adar BOYEM sukuma mazan ne kadai basada ikon auren macen daba jinin ahalin ba amma matan Ana aurar dasu wani gurin kuma Sam baa taba yiwa macen datake jinin BOYEM auren tilas saida cikakken raayinta sbd zataje ne qasar daba tata ba idan akai mata tilas zata rasa ahalinta kuma taje tayi qunci dan haka basa tilas tin farko ga matan boyem,

Wannan dalilin ne ya saka yayan nata suke Zaune masarautar mahaifinsu haryanzu hakama a tsaye suke qyam Akan tabbatarda karban mulkin dan uwansu Wanda tsufa ya kamasu a gida batareda sun ankare ba takai sultan ya rufe kofar Neman aurensu kwata kwata hukuncin su sai ranar da aka nada sabon sultan a Masarautar BOYEM shine zai bude musu kofar Neman aurensu daya rufe,

Hukuncin ya rikitar da rayuwarsu kwata kwata ta juye ta zama baqin cikin da babu Sauran hasken sauki a cikinsu sai zallar rashin imanin yadda da hakura daga abinda suke so dan kuwa indai wannan hukuncin dake kansu zasu jira to ko zasu kashe rai nawa suma saisun tabbatarda ASIM ne ya zama sultan dan kuwa idan ba shidinba ya hau babu me dauke wannan hukuncin zasu tsufa su mutu ne ba aure dan haka babban burinsu na rayuwa Akan tasu dalilin na tsananin son aure ya karfafa kudirinsu Akan hawan ASIM boyem dan yanzu wannan ne ma babban dalilinsu na jajircewa,

Ita kanta queen HAILE wannan shine dalili na biyu me karfi daya sakata tsayuwa Akan qudiri daya na tabbatar da ASIM ya karbi mulkin boyem sbd ganin yayanta zasu suna shirin tsufa su mutu babu aure ga qanwarsu neesat dake aure Masarautar Malaysia yayanta hudu babban ‘danta ma yana kokarin shiga university amma su Sauran suna gida manyanci yana sako musu Kai dan kuwa shekaru ashirin ake magana yanzu ko Bayan Barin NUAB ALMAZZ kasar idan aka hada da shekarunsu na baya ma suna hararar shekarun da suke Neman na wuce aure ma.

*******wishmah Ayanah tinda ‘danta hasken idaniyarta da zuciyarta ya tafi bata taba sake walwala ba a tsayin shekarun nan,
Bata taba manta tsananin soyayya da kaunar datake masa ba kona daqiqa daya,
Bata taba manta kamanninsa ba,
Bata taba dena kewa da tsananin son ganinsa ba duk da babu ranar da baya wuni kiransu akai akai yana video call da itaba sbd tsananin kauna da soyayyar dayake mata wadda ta zarta rayuwarsa da babu komai a ciki sai emptiness da Wani irin Zafin jinin sarauta dayake yawo a jininsa fiyeda mahaifinsa,

Wishmah a hankali taci gaba da manta komai da kowa harta gama mance komai a rayuwarta bata tina komai da kowa Bayan mutane biyar da sune rayuwarta,sune ji da ganinta a yanzu datake tamkar sabuwar haihuwa,
Qunci da baqin cikinta sun wanke babusu a zuciyarta sbd Manta komai datai dan haka rayuwarta take simple fayau ba damuwa da tashin hankali Bayan damuwan rashin HAYATEEM dinta da baya tareda ita Wanda shima hakanan koyaushe take rasa dalilin daya saka bakinta yake furta masa kada ya dawo qasar BOYEM Wanda shi kansa NUAB din wannan furucin nata ne ya hanasa dawowa qasar wadda har abada ya fitar da ita cikin ransa baida niyar dawowa rayuwa a cikinta.

Mutane biyar da su kadai ne a zuciya da kwakwalwan wishmah sune,
Shi kansa HAYATEEM din nata sai Mahaifinsa sultan data kasa cirewa a cikin kanta Wanda duk tsawon shekarun nan babu ranar da shima baya video call da ita kowace asuba sedai bata cewa komai haka zai kira ya zuba mata idanuwansa yana kallanta tana masa shiru batareda cewa komaiba itama tana kallansa harta gaji ta kife wayar tayi kwanciyarta tenya tazo ta dauki wayar ta fice da ita Wanda hakan wani sirri ne da babu Wanda ya sani a duniya daga sultan din se tenya wadda itama ta rasa dalilin sa na hakan a kowace asubar bayan kuma ya Riga ya nunawa duniya wishmah da ‘danta basa gabansa.
#MAMUH
#LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM
#BOYEM LEUL
#ALMAZZ NUAB

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
Chapter 52 · 0% Book details